Wednesday 20 September 2017

Mutun daya ya rasa ran sa a Kaduna yayin da yansanda suka yi masanya wuta da masu garkuwa da mutane

Tura Wannan Zuwa

Rundunar yan sandan jihar Kaduna, a
ranar Talata ta tarwatsa wasu masu
garkuwa da mutane a lokacin da suka
kai hari a Zaria.

Wannan lamarin ya auku ne sa’o’i 48
bayan masu garkuwa da mutane sun
kashe wani attajirin dan kasuwa
mazaunin Kaduna, Alhaji Sherrif Abida
Yazid akan babban hanya Kaduna zuwa
Abuja.

Mai Magana da yawun hukumar
yansandar jihar, ASP Aliyu Mukhtar, ya
tabbatar da aukwan lamarin da cewa
masu garkuwa da mutane sun kai hari
gidan tsohon shugaban yan bangar
Shika, dake karamar hukumar sabon
gari Zaria Alhaji Mustapha Ghali.

Mukhtar yace masu garkuwa da
mutanen sun fara kai wa dukiyoyin
Alhaji Ghali hari kafin suka yi awon
gaba da yayan shi mata biyu.

A jawabin sa ya ce rundunar yansanda
na PSRS sun tunkare su a lokacin da su
ka kai hari unugwan, sannan suka fara
musayar wuta a tsakanin su, wanda
yayi sanadiyar raunana Ghali da
jam’ian yansanda biyu.

Mai Magana da yawun yansandar ya
tabbatar da mutuwar Ghali a asibitin
Shika bayan jinya da yayi.
Ya kara da cewa masu garkuwa da
mutanen sun kasa tafiya da matan da
suka sace saboda bude wutar da
jam’iyyar tsaro suka mu su.

“Kwamishinan yansadar jihar, Agyole
Abeh yaba da umarnin kara jami’an
tsaro a yankin dajin da suka shiga dan
kama masu garkuwan da suka gudu,”
Inji shi.

Ya ce abun bakin ciki ne Alhaji Ghali ya
rasa rayuwansa a lokacin da yan sanda
suke musayan wuta da masu garkuwa
da mutanen.

Kuma wasu jami’an yansanda sun samu
rauni amma suna jinya a asibitin Shika
dake Zaria.
“Kuma bayan haka an samu nasarar
kwato matar dan kasuwar da masu
garkuwa da mutane suka kashe, Hajiya
Jamila Yazid.

.
Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayoyin Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka  dadinkowa24.blogspot.com mungode Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum farin cikin Ku shine Farn Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com ALLAH yabar Zumunci Amin
.
.
Source By ©Hausa.Naij.com

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user

0 comments: