Wednesday 20 September 2017

BABU DANGANTAKA TSAKANINA DA RAHAMA SADAU- NAFISA ABDULLAHI

Tura Wannan Zuwa Ga

Fitacciyar jarumar
Kannywood Nafisa Abdullahi
ta ce duk da yake sana'arsu
daya da Rahama Sadau,
babu wata alaka ta 'yan
uwantaka ko kawance a
tsakaninsu.

Nafisa, wacce ta bayyana
haka a shafinta na
Instagram, ta ce babu wata
abokantaka tsakanin matan
da ke yin fina-finan na
Hausa.

A cewarta, "Ina mamakin
yadda masu amfani da
shafin Instagram ke daukar
mu ['yan fim] wallahi. Ya
kamata ku sani cewa da ni
da Rahama sana'armu guda,
amma babu abokantaka ko
'yan uwantaka tsakanimu.
Kai, babu wata dangantaka
tsakaninmu mata 'yan fim.

Don haka, duk wanda yake
tunanin muna jituwa
yaudarar kansa kawai yake
yi."

Jarumar ta yi ikirarin kowa
ta kansa yake yi tsakanin
'yan kannywood, tana mai
cewa lokacin da wani ya
wallafa hotonta sanye da
gajeren wando—batun da ya
janyo mata zage-zage—babu
wata 'yar Kannywood da ta
fito ta kare ta duk da yake
sun san cewa an yi ne
domin a bata mata suna.

Ta kara da cewa ta yi
amanna Rahama za ta iya
jure wa halin da ta fada a
ciki, sannan ta yi kira ga
mutanen da ke son ta bi
sahun masu kiraye-kirayen a
janye korar da aka yi wa
Rahama su daina bata
lokacinsu.
.
.
Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayoyin Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka  dadinkowa24.blogspot.com mungode Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum farin cikin Ku shine Farn Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com ALLAH yabar Zumunci Amin
.
.
Source By ©Dadin Kowa24

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user

0 comments: