Wednesday 20 September 2017

ADAM A. ZANGO YA DAKATAR DA YIN FIM!

Tura Wannan Zuwa

Fitaccen jarumin nan na
fina-finan Kannywood,
Adam A. Zango, ya ce daga
yanzu ba zai ci gaba da
fitowa a fina-finai ba.

A sakon da ya wallafa a
shafinsa na , Zango ya ce
"zan yi amfani da wannan
damar don bai wa masoya
kallon fina finaina... hakuri a
kan na dakatar da yin fim".

Ya kara da cewa "zan tsaya
iya waka domin na samu
sauki da kwanciyar hankali".

A ranar Lahadi ne muka
wallafa labarin da ke cewa
jarumin ya yi tsokaci kan
masu shaidar karatun digiri.

Sai dai Adam Zango ya nemi
afuwa kan kalaman da ya yi,
inda ya ce "ina bai wa 'yan
boko hakuri a kan abin da
@bbchausa suka ce na fada
game da masu degree. A
gafarce ni".

Jarumin ya kuma goge
sakon da ya wallafa din
wanda akansa ne muka gina
labarin.

'Sakon da ya fara wallafawa'
A sakon da ya fara
wallafawa a shafinsa na
Instagram, wanda tuntuni ya
goge, jarumin ya yi shagube
cewa shi ba shi da shaidar
kammala karatu ta digiri
amma ya fi masu digiri
amfani.

A cewarsa, "Idan ka mallaki
digiri baka da aiki. Ni kuwa
ba ni da digiri amma
shekara 12 ina da aikin yi.

Ko da kana da aiki idan na
rera waka daya zan samu
kudin da suka fi albashinka."
Da alama dai yana yin raddi
ga wasu ne, wadanda bai
fadi sunan su ba.

Zango ya ce bai iya turancin
ba, yana mai cewa wadanda
suka iya turancin sai su "ci
shi" idan abinci ne, yayin da
shi kuma zai rika yin larabci.

Sai dai wannan batu ya jawo
masa suka daga wajen wasu
masu amfani da shafukan
sada zumunta, inda daya
daga cikinsu ke cewa "ai ni
ban taba jin Zango ya yi
larabci ba."

.
Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayoyin Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka  dadinkowa24.blogspot.com mungode Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum farin cikin Ku shine Farn Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com ALLAH yabar Zumunci Amin
.
.
Source By ©Fadila M. Idris

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user

0 comments: