Wednesday 20 September 2017

Malaman Jami'o'i Sun Jannye Yajin Aikin Sama Da Wata Daya

Tura Wannan Zuwa Ga

Kungiyar malaman jami'o'i ta Nijeriya ta sanar da
dakatar da yajin aikin da ta shiga na sai-baba-ta-
gani bayan sama da wata daya.
Shugaban kungiyar farfesa Biodun Ogunyemi ne
ya sanar da janyewar, ranar Litinin da daddare
jim kadan bayan wata ganawa da Ministan
kwadago da ayyuka, Dakta Chris Ngige, a Abuja.

Kungiyar ta ce ta dakatar da yajin aikin ne
wanda ta shafe wata daya da kwana shida, har
zuiwa karshen watan Oktoba, lokacin da
gwamnati za ta cika alkawarun da ta yi.

Matakin dai ya biyo bayan tarukan tattaunawar
da aka rika yi ne tsakanin masu ruwa da tsaki a
harkar ilimi, musamman ma'aikatar ilimin da
kuma ta kwadago da ayyuka.
Kungiyar ta umarci malaman jami'o'i da su koma
bakin aiki daga ranar Talata.
Kungiyar ta ASUU ta shiga yajin aikin ne na sai-
abin-da-hali-ya-yi, ranar 13 ga watan Agusta,
sakamakon gazawar gwamnati ta aiwatar da
yarjejeniyar da suka yi a watan Nuwamba na
2016.

.
Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayoyin Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka  dadinkowa24.blogspot.com mungode Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum farin cikin Ku shine Farn Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com ALLAH yabar Zumunci Amin
.
.
Source By ©Dadin Kowa24

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user

0 comments: