Monday 25 September 2017

Jam'iyyar ƙin musulunci ta samu tagomashi a Jamus

Tura Wannan Zuwa Ga

Zaben majalisar dokokin Jamus ya ba shugaba
Angela Merkel damar zarcewa wa'adi na hudu a
kan mulki.

Ko da yake, ya rage mata kason kuri'un da
jam'iyyarta ta samu zuwa 33 cikin 100, adadi
mafi karanci a shekaru gommai.

Mrs Merkel za ta shiga tattaunawa mai wahala
don kafa gwamnatin gambiza a wani yanayin
siyasa maras alkibla.
Ana sa ran tattaunawa ce da sai an kai ruwa
rana.

Karon farko, bayan samun kasa da kashi 13 cikin
100, jam'iyyar AfD mai tsattsauran ra'ayin kishin
kasa za ta karbi kujeru a majalisar Busdestag..

Wakilin BBC a Berlin ya ce jam'iyyar da ke gud'ar
samun nasara yanzu, ita ce AfD mai janyo
rarrubuwar kai, ta masu ƙin jinin baƙi da addinin
musulunci.

"Kasa da shekara biyar bayan kafuwarta, mai
yiwuwa a yanzu AfD ta tashi da kujera 100 a
Majalisa," in ji shi.

Haka zalika, sakamakon ya janyo fushi da nuna
taraddadi a kasar ta Jamus.

Zanga-zangar nuna adawa da jam'iyyar AfD ta
barke a birane da dama ciki har da Berlin, an ma
kama adadin mutane da dama.
Jazaman ne sai gwamnatin da Merkel za ta kafa
ta samu hadin kan jam'iyyu ƙanana guda biyu
bayan 'yan Social Democrat sun sanar cewa ba
za su shiga gamin gambizar ba.
Hakan ya biyo bayan mummunan kayan da suka
sha wanda rabonsu da ganin irinsa tun a
shekarun 1930.

Rashin tabbas ya sa darajar takardar kudin euro
tangal-tangal a kasuwannin Asiya bayan sanar da
sakamakon zaben.

.
Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka  dadinkowa24.blogspot.com mungode
.
Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Idan kana/kina da Labarin daku keson asanarwa da Duniya, ko Tambaya,Shawarwari,Hausa Novels, Nishadantarwa,Ilimantarwa,Ko Neman Sani akan ranakun dazamu cigaba dakawo muku Posting na Hausa Novels da Sauran su, zaku iya tuntubar ma'aikatan mu kuturo da Sunan Ku tareda Addreshin Ku tawannan Email din Officialdadinkowa24@gmail.com kyautane zamuyi muku komai don cigaban Al'ummar Hausa bama bukatar kudinka sai dai idan kaikayi niyyar Turowa don siyan Data Saboda acigaba dayin Posting a Kodayaushe batareda dakatawa ba, Al'ummar Nigeria  daga N50 zuwa abinda yasamu duk zaku iya turo da Lambobin katin  ta Email din mu akan officialdadinkowa24@gmail.com  ko Neman Account Number din mu na Bank ga mutanen dabasa cikin Nigeria, Website din Mu bashi da Alaka ta kusa ko tanesa da Wani/Wata Dan Siyasa/'Yar Siyasa afadin Duniya Burin mu shine musamu amincewar Al'umma aika da Gudunmawarka,Labari,Shawara da sauran su a Addreshin mu na email ✉💌📩 officialdadinkowa24@gmail.com 
.
Suna addreshin misali..
.
Subject: Fatan Alheri
Suna: Yusuf Tk
Kasa: Nigeria
Gari: Kano
Garin da akeda Zama: Kaduna
Sako: Yaushe Ne zaku cigaba da Labarin Kundin Tsatsuba Littafi na 2 na Madakin Gini? Mungode
.
Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri
.
ALLAH yabar Zumunci Amin🙏
.
.
Source By ©Bbc Hausa

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user

0 comments: