Tuesday 19 September 2017

Muhimman Jawabai 5 na shugaba Muhammadu Buhari a taron majalisar dinkin duniya

Tura Wannan Zuwa Ga

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi
jawabai a madadin Kasar najeriya baki
daya a taron majalisar dinkin duniya, inda
ya taya zababben sakatare janar na
majalisar da kuma godiya ga tsohon sakare
janar Ban Ki Moon akan hidimar da ya
yiwa majalisar da duniya baki daya.

1. Batun Nukiliyar kasar Iran,
Yarjejeniya akan sauye sauye yanayi na
na Farisa da hatsaniyar nukiliyar kasar
Koriya ta Arewa

2. Yabawa majalisar dinkin duniya
akan rawar da ta taka wajen bayar da
matsugunni ga 'yan gudun hijira da
yakin kasar Siriya, Iraq da
Afgahanistan ya yi ma su sanadiyar
zamantakewar su da muhallansu.

3. Godiya ga gwamnatin Jamhuriyyar
kasar Jamus karkashin jagorancin
Angela Merkel da kuma gwamnatocin
kasar Italiya, Girka, Turkey wajen
taimakawa dubunnan 'yan gudun
hijira.

4. Ya jinjinawa kasashen duniya da
al'ummominsu wajen jajintawa,
taimakawa da goyon bayan nahiyyar
mu da al'ummominmu da yankin tafkin
Chadi akan barazanar ta'addancin Al
Qa'ida da Boko Haram.

5. Jajintawa da nuna damuwarsa akan
rashin kare 'yancin ɗan adam rikicin
Gabas ta tsakiya, da kuma wahalhalun
Falasdinawa da na Gaza. Akwai rikicin
kasar Yemen da kuma na kwana-
kwanan nan na kasar Myanmar.

Shugaba Buhari ya musalta rikicin
Myanmar da abin da ya faru a kasar
Bosnia a shekarar 1995 da kuma kasar
Rwanda a shekarar 1994.

.
Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayoyin Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka  dadinkowa24.blogspot.com mungode Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum farin cikin Ku shine Farn Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com ALLAH yabar Zumunci Amin
.
.
Source By ©Hausa Naij.com

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user

0 comments: