Monday 18 September 2017

Nigeria ta zama kasa ta farko data samar da Computer me Zallar Harshen Hausa

Tura Wannan Zuwa
A Najeriya, an kaddamar da wata manhaja mai
suna Rumbun Ilimi, wadda ke kunshe da bayanai
a kan fannonin rayuwa da fagen ilimi daban-
daban cikin harshen Hausa zalla.

An kwashe shekara tara ana tsara manhajar
kamar yadda wanda ya kirkiro ta ya bayyana a
lokacin kaddamamarwar.

Mallam Abubakar Muhammad Tsangarwa, shi ne
ya kirkiro manhajar, kuma ya shaida wa BBC
cewa, manhajar ta kunshi darussa a bangarori na
rayuwa daban-daban a cikin harshen Hausa.
Ya ce, ba sha'awa ba ce kawai ta sanya shi
kirkirar manhajar, sai dai domin ya zaburantar da
jama'a musamman masana kan su tashi su rika
hidimta wa harshen.

Mallam Abubakar, ya ce, sai da ya laluba ya ga
kwata-kwata babu wani abu da ya kunshi zallar
Hausa na komfuta a duniya da ke bayar da
gudunmawa a bangaren ilimi, sannan ya yi
tunanin samar da manhajar.

Ya ce, an yi manhajar ne kuma don ta zamo mai
amfani ga duk mutumin da zai iya karanta
Hausa, walau ya je makaranta ko bai je ba.
Kazalika a manhajar, akwai magana a kan abinci
mai gina jiki, da magana a kan ilimin
zamantakewar dan-adam da Hausa da dai sauran
fannoni da rayuwa da ilimi.

Malamin ya ce a yanzu akwai lambar da ake kira
idan ana so a samu manhajar, wadda ita ce
08039648244, ga duk wanda yake bukata, ko da
yake ya ce a yanzu suna kokarin yin 'yan
gyararraki a kai, kafin nan da 'yan kwanki masu
zuwa su kammala..

Sannan ya ce, an kirkiri shafin manhajar na
intanet, wato www.rumbunilimi.com ko kuma a
shafukan sada zumunta da muhawara na
Facebook da Twitter a Rumbin Ilimi, sannan ta
Whatsapp kuma a lambar da ya fada a baya, duk
za a iya samun manhajar .

Source By ©Bbc Hausa
TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user