Wednesday 27 September 2017

Sauya fasalin Kasar Nigeria tamkar samun kasar Biafra ne - Ohaneze

Tura Wannan Zuwa Ga

Shugaban kungiyar 'yan kabilar Igbo ta Ohaneze
Ngigbo, John Nwodo ya ce Najeriyar da aka
sauya wa Fasali, tamkar Biafra ce.

A hirar da aka yi da shi a shirin Newsday na
sashen Turanci na BBC, Mista Nwodo, wanda ya
shaida yakin basasar Najeriya, ya ce bai kamata
a sake tayar da maganar yakin ko kuma sunan
Bifra ba.

Ya bayyana cewar sauya fasalin Najeriya shi ya
fi dacewa da muradun 'yan kabilar Igbo na nan
gaba maimakon fafatukar kafa kasar Biafra.

Ga fassarar hirar da aka yi da shi a shirin
Newsday:

Bana tunanin ya kamata mu sake tayar da yakin
(basasar Najeriya) kuma ko kuma maganar
Bifara a yanzu.

Tambaya: Me kake nufi da a yanzu? IPOB ta ce
Najeriya ba ta kiyaye hakkokin 'yan kabilar Igbo
dake kudu maso gabashin Najeriya, kuma
saboda haka suna son kasarsu. Shin baka yarda
da haka bane ko kuma ka yarda?

Nwodo: Dukkanmu mun yarda da ginshikin lamarin.

Inda muka yi sabani shi ne hanyar da za a bi (a
dakile matsalar). Na yi imanin cewar in aka sauya
fasalin Najeriya, tamkar an samar da Biafra ne.

A Najeriyar da aka sauya wa fasali, za su samu
'yancin kai na tattalin arziki da na siyasa a
yankunansu kamar yadda muka samu a 1963.

Tambaya: Abin da kake so shine abin da ake
kira cikakkiyar tarayya?
Nwodo: Wannan haka yake.

Tambaya: Amma ba kasa mai cin gashin kanta
ba?
Nwodo: A'a.

Ta yaya za ka tinkari dubban matasan da ke
gudanar da zanga-zangar goyon bayan IPOB da
ke son kasa mai cin gashin kanta?
Nwodo: E, na ji haka a shekarar 1967. Na wuce
irin wannan tunanin a yanzu, kuma na san abin da
suke nema na da wuyar samu yanzu. Kuma na
biyu,fafutukar Biafra din ba alheri ba ne a gare su
nan gaba.

Idan kana son kasar Biafra mai cin gashin kanta,
sai ka bi wadannan hanyoyin. Sai ka bi ta hanyar
zaben raba gardama. Kundin tsarin mulkin Najeriya
bai ba da damar zaben raba gardama ba.

Zan iya ba ka wasu misalai kadan da suka zamo
hargitsi kuma har yanzu suna fama. A Sudan
yawan kashe-kashe ya tilasta musu su bai wa
Sudan ta Kudu 'yanci tun kafin a gudanar da zaben
raba gardama.

A kasar Ethiopia da Eritria irin wannan lamarin ne
ya faru. Kuma gabar da ke tsakanin bangarorin
biyu na haddasa hasarar rayuka har yanzu a
wadannan wuraren biyu.

A daya bangaren na Maroko da Kamaru kuma, har
yanzu ba a san yadda za ta kaya ba.
Gaskiyar maganar ita ce bin daya daga cikin
wadannan hanyoyin yana da wuyar gaske. Kuma in
ka samu kudirin kan lamarin a kungiyar Tarayyar
Afirka (AU) ko kuma Majalisar Dinkin Duniya, za ka
bukaci majalisar dokokin kasarmu ta amince da
dokar.

Kuma bayan haka za ka bukaci a ware wa hukumar
zaben kasarmu saboda ta samu ta shirya zabe.

Wannan wani abu ne mai wuya.
Wannan dai ba shi ne karo na farko da wasu
jagorori a al'ummar Igbo ke nesanta kansu da
ayyukan fafutukar kungiyar IPOB ba, ko a farkon
wannan watan ma, gwamnonin yankin Igbo sun
haramta IPOB.

.
Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka  dadinkowa24.blogspot.com mungode
.
Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Idan kana/kina da Labarin daku keson asanarwa da Duniya, ko Tambaya,Shawarwari,Hausa Novels, Nishadantarwa,Ilimantarwa,Ko Neman Sani akan ranakun dazamu cigaba dakawo muku Posting na Hausa Novels da Sauran su, zaku iya tuntubar ma'aikatan mu kuturo da Sunan Ku tareda Addreshin Ku tawannan Email din Officialdadinkowa24@gmail.com kyautane zamuyi muku komai don cigaban Al'ummar Hausa bama bukatar kudinka sai dai idan kaikayi niyyar Turowa don siyan Data Saboda acigaba dayin Posting a Kodayaushe batareda dakatawa ba, Website din Mu bashi da Alaka ta kusa ko tanesa da Wani/Wata Dan Siyasa/'Yar Siyasa afadin Duniya Burin mu shine musamu amincewar Al'umma aika da Gudunmawarka,Labari,Shawara da sauran su a Addreshin mu na email ✉💌📩 officialdadinkowa24@gmail.com
.
Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri
.
ALLAH yabar Zumunci Amin🙏
.
.
Source By ©Bbc Hausa

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user

0 comments: