Thursday 26 October 2017

Hausa Films: Yadda Wakokin Film Din Mansoor Suka Samu Karbuwa Tun Kafin Su Shiga Kasuwa

Tura Wannan Zuwa

A kwanakin baya ne shahararren kamfanin shirya
finafinan Hausa FKD, ya fitar da taba ka lashen
sabbin wakokin fim dinsa mai suna Mansoor,
wadanda yanzu haka suka yamutsa hazo a
farfajiya Kannywood, duk da cewa ba a fitar da
su kasuwa ba.

Da yake zantawa da wakilinmu game da yadda
wakokin suka samu karbuwa a zukatan al’umma,
wani darakta da ya bukaci a sakaya sunansa, ya
ce hakika idan ana batun zuwa da wakoki masu
dadi a cikin finafinan Hausa, to kamfanin FKD shi
ne kan gaba wajen ganin ya zo da dadadan
wadodin masu sanyaya zuciyar mai sauraro.

“Kamfanin FKD ya yi kaurin suna ta wannan
bangaren tun shekaru da dama da suka gabata.

Domin sun fitar da wakoki wadanda har yau din
nan an kasa mantawa da su irinsu:Mujadala,
Fil’Azal, Sai Wata Rana, Madubin Dubawa,
Adamsy, Sirrin Da Ke Raina, Halacci, Halwa da
kuma baya bayan nan Gamun Nan Dai.” In ji shi.

Wannan karon kamfanin ya sake zuwa da wani
salon na daban, wanda za a iya cewa shi ne
irinsa na farko a cikin wani sabon shiri mai suna
MANSOOR.

Wakokin fim din; Abin Da Yake Raina,
Zan Rayu Da Ke, Makullin Zuciya, Macukule,
Jirgin So Zai Tashi da Ya Mansoor Na, tuni sun
hau kan kadamin zamowa shahararru da za su
dade a kunnunwa masoya.

Hakika Umar M Shareef, Abdul D. One, Murja
Baba, Maryam Fantimoti, da Khairat Abdullahi da
suka bada muryoyinsu wajen rera wadannan
wadodi na madaukakiyar soyayya sun taka rawar
gani.

Da ma me ake tsammani daga wurin
mutanen da suke da tarin basira wajen sarrafa
murya don yi wakar soyayya? Bari mu dan kalli
wakokin don yin bayani a kansu…

Abdul D. One (Marubucin Waka kuma Mai
Rerawa), ya yi amfani da muryarsa wajen rera
wakar ‘Abin Da Yake Raina’ da a yanzu samari da
‘yan mata ke yin guzurinta don farantawa juna
rai.

Tabbas dadin wakar ya kai matsayin da idan
mutum ya kunna sai dai ya yi ta ji ba tare da ya
canja wata ba, saboda muryarsa tana da dadin
sauraro.

Maryam Fantimoti, ita ma ba a bar ta a
baya ba, domin wakar da ta rera ‘Ya Mansoor Na’
tuni ta shiga sahun shahararrun wakoki ababen
saurare.

Dan Macukule

,’ duk da ba irin wakokin da Umar ya saba yi ba
ne, amma ya yi matukar kokari tun daga farkonta
har karshe.

Babu wani sabon abu a cikinta,
amma tsarin kid’anta ya yi matuk’ar dadi.

Har ila
yau, lafuzan da aka yi amfani da su sun tsaru
tsaf, ta yadda za a nishadantar da mai sauraro.
Hakika idan wakar ta samu talla sosai, za ta
zamo daya tamkar da dubu a wurin masoya
sauraron waka.

Fitar wakar ‘

Zan Rayu Da Ke

’ ya sauya salon album din gaba daya, domin
Umar M. Shareef ya kara nuna wa duniya cewar
indai bangaren wakar soyayya ne to ba shi da na
biyu. Duk wani masoyi, ko masoyiya, zai so a ce
shi ake rerawa wannan waka.

Tuni ya sanya
hatta manyan jaruman a Kannywood da sauran
mutane rera wakar suna dora ta a shafukansu na
Instagram, yayin da jarumi Ali Nuhu ke bayyana
farin cikinsa da zarar sun yin hakan.

Jirgin So Zaya Tashi

’ wadda Umar suka rera tare da Murja Baba ta yi
dadi matuka, hakan yana kara bayyana basirar
mawakin a fili. Kidan ya tsaru matuka, zubin
tsarin zantukan da aka yi amfani da abun
burgewa ne. Kai da nemi wakar kawai ka
saurara.

‘ Makullin Zuciyata ’ irin wakokin nan ne da idan
mutum ya fara saurara shi kenan sun shiga
jikinsa, batun dainawa ma sam bai taso ba.

Waka
ce da ke bayyana irin yadda masoyi ya kamu da
son masoyiyarsa, da kuma irin fatan da yake da
shi na ganin ta karbi soyayyarsa da hannun biyu.

Wadannan su ne wakokin da fim MANSOOR yake
dauke da su.

An fitar dasu Kasuwa ga wadanda basa cikin Nigeria Ku ci gaba da Kasancew da Shafin Dadinkowa24 don samun Wakokin Cikin Sauki

Babban abinda aka fi mayar da kai yanzu haka
shi ne, yanayin yadda labarin fim din zai
kasance, domin an ga mawaki Umar M. Shareef
ya yi tsalle tare da fadowa duniyar jarumai don a
dama shi.

Ganin Umar cikin fim din ya sanya
masoya zuba ido, suna jiran ganin yadda zata
kayatar.

Labari: Ali Nuhu

Tsarawa: Jamil Nafseen

Rubutawa Waka: Umar M Shareef, Abdul D One

Rerawa: Umar M. Shareef, Abdul D. One, Maryam
Fantimoti, Murja Baba da Khairat Abdullahi.

Koyar Da Rawa: Ali Nuhu

Shiryawa: Nazir Dan Hajiya

Bada Umarni: Ali Nuhu

Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka dadinkowa24.blogspot.com

Ku hanzarta sanar da 'Yan Uwa da abokanan Arziki sunan Website din Mu me Albarka, don ganin sabbin posting din Mu se ku duba saman website din akwai "Home" sai ku shiga, mungode

Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com

Idan kana/kina da Labarin daku keson asanarwa da Duniya, ko Tambaya,Shawarwari,Hausa Novels, Nishadantarwa,Ilimantarwa,Ko Neman Sani akan ranakun dazamu cigaba dakawo muku Posting na Hausa Novels da Sauran su, zaku iya tuntubar ma'aikatan mu kuturo da Sunan Ku tareda Addreshin Ku tawannan Email din Officialdadinkowa24@gmail.com kyautane zamuyi muku komai don cigaban Al'ummar Hausa bama bukatar kudinka sai dai idan kaikayi niyyar Turowa don siyan Data Saboda acigaba dayin Posting a Kodayaushe batareda dakatawa ba, Website din Mu bashi da Alaka ta kusa ko tanesa da Wani/Wata Dan Siyasa/'Yar Siyasa afadin Duniya Burin mu shine musamu amincewar Al'umma aika da Gudunmawarka,Labari,Shawara da sauran su a Addreshin mu na email ✉💌📩 officialdadinkowa24@gmail.com

Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com

Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri

ALLAH yabar Zumunci Amin🙏

Source By ©Kannymp3

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user

0 comments: