Thursday 26 October 2017

BH Nigeria: Sojin Nigeria sun 'kashe' matar Shekau a luguden wuta

Tura Wannan Zuwa

Wannan na kunshe ne a wata sanarwa da
rundunar sojin sama ta aikewa manema labarai a
ranar Laraba, wadda mai magana da yawunta Air
Commodore Olatokunbo Adesanya, ya sanyawa
hannu.

Sai dai babu wata majiya mai karfi zuwa yanzu
da ta tabbatar da ikirarin nasu.

Ko a baya ma rundunar sojin Najeriya ta sha yin
ikirarin cewa ta kashe manyan kwamandojin
Boko Haram har ma da shugabansu Abubakar
Shekau, sai dai daga baya kungiyar ta musanta.

Rundunar ta ce rahotanni sun nuna cewa Malama
Firdausi na wakiltar mijinta ne a jan ragamar
wani taro da sauran mayakan kungiyar ke halarta
a wajen da aka kai hare-haren saman.

A ranar 19 ga watan Oktobar 2017 ma rundunar
sojin kasar ta ce ta samu nasara a wani hari da
ta kai kan wasu wurare da suka kasance
maboyar mayakan Boko Haram din a Durwawa.

Rahoton da aka tattara na ta'adin da aka yi a
lokacin ya nuna cewa harin saman da aka kai ya
sa wuta ta tashi, abin da ya lalata wasu gine-
gine na mayakan Boko Haram inda da dama suka
mutu, ya kuma tilasta wa kadan daga cikin su
tserewa.

Dama dai rundunar sojin kasan ta fitar da
sanarwar cewa ta fara wani aiki na kai wa
mayakan Boko Haram hare-hare ta sama, da ta
yi wa lakabi da Operation Ruwan Wuta.

An fara aikin Operation Ruwan Wuta ne a ranar
Litinin 23 ga watan Oktobar 2017, don yin ruwan
wuta a maboyar mayakan Boko Haram.

A ranar farko ta fara aikin, rundunar sojin saman
ta yi ruwan wuta sosai a wasu yankuna da ke
garin Garin Maloma.

An yi amfani da jiragen yaki biyu masu dauke da
bama-bamai da rokoki inda aka dinga luguden
wuta, aka kuma kwashe wasu mayakan masu
kokarin tserewa.

Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka dadinkowa24.blogspot.com

Ku hanzarta sanar da 'Yan Uwa da abokanan Arziki sunan Website din Mu me Albarka, don ganin sabbin posting din Mu se ku duba saman website din akwai "Home" sai ku shiga, mungode

Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com

Idan kana/kina da Labarin daku keson asanarwa da Duniya, ko Tambaya,Shawarwari,Hausa Novels, Nishadantarwa,Ilimantarwa,Ko Neman Sani akan ranakun dazamu cigaba dakawo muku Posting na Hausa Novels da Sauran su, zaku iya tuntubar ma'aikatan mu kuturo da Sunan Ku tareda Addreshin Ku tawannan Email din Officialdadinkowa24@gmail.com kyautane zamuyi muku komai don cigaban Al'ummar Hausa bama bukatar kudinka sai dai idan kaikayi niyyar Turowa don siyan Data Saboda acigaba dayin Posting a Kodayaushe batareda dakatawa ba, Website din Mu bashi da Alaka ta kusa ko tanesa da Wani/Wata Dan Siyasa/'Yar Siyasa afadin Duniya Burin mu shine musamu amincewar Al'umma aika da Gudunmawarka,Labari,Shawara da sauran su a Addreshin mu na email ✉💌📩 officialdadinkowa24@gmail.com

Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com

Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri

ALLAH yabar Zumunci Amin🙏

Source By ©Bbc Hausa

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user

0 comments: