Thursday 26 October 2017

Jarumin danafi Kauna Shine Adam A. Zango —Amina Amal.

Tura Wannan Zuwa

Amina Muhammad (Amal) ‘yar asalin ƙasar
Kamaru ce, wadda a yanzu ta fara haskawa a
finafinan Kannywood. Jaruma ce da a yanzu ta
fara shahara sakamakon manyan finafinan da
take fitowa a cikinsu.

Musamman da take taka
rawa tare da shahararrun jarumai irinsu: Ali Nuhu
da Adam A. Zango. A wannan ‘yar gajeriyar
tattaunar da ta yi da Mubarak Umar, ta ɗan taɓo
batun faɗin tashin da ta yi kafin ta zo Nijeriya,
har ma ta fara fim ɗin Hausa.

Ki gabatar wa da makaranta kanki.

Sunana Amina Muhammadu, daga ƙasar Kamaru
na zo Nijeriya. Na yi karatuna tun daga furame
har sakandire a Kamaru, duk cikin harshen
Faransanci. Daga bisani na halarci wata
tsangaya da ake koyar da Turanci a can
Kamarun, na koya cikin wata uku. Yanzu ina jin
yare huɗu, Fulfulde, Hausa, Faransanci da kuma
Turanci. Wannan shi dai a taƙaice.

Ta yaya aka yi kika zo Nijeriya?

To, lokacin da nake Kamaru ina kallon finafinan
Hausa, kuma ina jin daɗin yadda ake nuna al’adar
Hausa.

Na koyi abubuwa da yawa dalilin fim ɗin
Hausa, tun daga kan sanya sutura irin su;
atamfa, abaya, leshi da sauran su.

Haka zalika,
salon maganganun da ake amfani da su, suna
matuƙar birge ni.

Don nakan kwaikwayi abubuwa
da dama.

Jarumin da nake matuƙar ƙauna shi ne Adam A
Zango, saboda shi na baro Kamaru na zo
Nijeriya.

Na daɗe ina mafarkin yin ido biyu da
shi, nagode Allah da ban mutu ba sai da Ya cika
min burina na ganin Zango, har na yi fim da shi.

Da ma saboda fim kika zo?

Eh to, kai tsaya ba zan ce saboda fim na zo ba,
na zo ne saboda in ga Adam A. Zango, sai bayan
mun haɗu na ji ina sha’awar fitowa a fim.

Kuma,
dalilin fitowa ta fim ɗin shi ne, ƙalubalen da na
gamu da shi kafin iyayena su yarda su bar ni
yana da yawa.

Amma dai sun ƙyale ni, tun da sun
fahimci abin da nake so kenan.

Saboda haka, ta
ya ya zan gamsar da su cewa na haɗu da shi,
shi ne in yi fim ɗin da zan kai musu su gani.

Hatta ƙawayena ta hanyar fim zasu yarda na gan
shi.

Tsoron da iyayena suka riƙa ji bai wuce yadda ba
ni da kowa a Nijeriya ba, ba su san hannun
wanda zan faɗa ba.

Sai na nuna musu cewar
Adam A. Zango yana da kirki kuma zai kula ni,
duk ban taɓa haɗuwa da shi ba, na yi iya bakin
ƙoƙarina wajen gamsar da su; duk da ina matsayin
mace, zan kiyaye mutuncina har in dawo gida.

Na faɗa musu duk da ban ga shi ba, ballantana in
san halayensa na zahiri, amma na san Inn Shaa
Allah zai karɓe ni hannu biyu-biyu.

Wane ƙalubale kika haɗu da shi a hanya?

Taɓ! Gaskiya na sha wahala ba ƙarama ba, domin
mota na biyo ba a jirgi na zo ba.

Na shigo
Nijeriya ne ta jihar Ribas, na kwana a Kalaba,
saboda matsalar tsaro da ake fama da ita a
Arewa Maso Gabashin Nijeriya.

Da gari ya waye na samu motar Abuja, sannan
na shigo Kaduna.

Lokacin da na zo Arewa ban san kowa ba, ga shi
ba na jin Hausa, ba kuma kowa ne yake cin
Turanci ba.

Da ma iyayena sun bani kuɗi isassu
kafin na taho, saboda haka na kama otel a
Kaduna na zauna, na fara tunanin ta inda zan
fara.

Lokacin da yunwa ta kama ni, na sa aka kawo
min abinci, sai da na yi kuka har kaina ya yi
ciwo, don ban taɓa cin irin abincin ba; shinkafa
da wake ce.

Amma yanzu na saba.

Yadda kuwa aka yi na san Adam yana Kaduna shi
ne, kullum a waƙoƙinsa yana yawan faɗar garin
Kaduna a matsayin inda yake tinƙaho da shi, shi
yasa kai tsaye na nufin can.

A hankali na haɗu da wani Guyson, wanda
yaronsa ne, sai ya ga hotonsa a wayata, sai ya
ce na san shi ne, sai na ba shi labarin yadda aka
yi na zo Nijeriya.

Daga bisani sai na haɗu da Habu Sarki, wanda
kusan amini ne a wajen Zango, shi ya kula ni, ya
ɗauke ni tamkar ƙanwarsa ta jini, har Allah ya sa
na haɗu da Adam A. Zango.

Haƙiƙa ba zan manta da gudunmuwar Habu Sarki
gare ni ba, ya taimake ni sosai, shi ne kallo a
matsayin ubangidana.

Da kika haɗu da Zango ya kika ji?

Wai! Na yi farin ciki matuƙa, don ni kaina mamaki
na riƙa yi, ina kallon hotonsa a wayata, ina
kallonsa a zahiri.

Tambayar da na riƙa yiwa kaina
ita ce, shin da gaske ne ko kuwa a mafarki nake
yi.

Idan na ce zan faɗi irin farin ciki da na yi
gaskiya zan iya yin ƙarya, gwanda kawai in yi
shiru.

Bayan mun gaisa sama-sama haka, sai ya ce in
dawo gobe mu haɗu a ofis ɗinsa.

Ranar ban yi bacci ba, saboda murna.

Washegari na zo ofis, a nan ne na gamsu cewa
tabbas Adam A. Zango na gani, saboda na ji duk
wanda ya shigo yana ambatar sunansa.

Ta yaya kika fara fim, kuma kin yin fim ya kai
nawa?

Lokacin da zan fara fim na gami da matsaloli da
yawa, na farko ba na jin Hausa, kuma fim ɗin
nan da Hausa ake yi.

Saboda haka sai da na shafe wata shida ina
koyon harshen Hausa.

Haƙiƙa na yi farin ciki ƙwarai kuma ina alfahari da
finafinai Kannywood, ga shi dalilinsa na koyi
harshe da al’adun wani gari da ba nawa ba.

Da aka zo za a fara fim ɗin, sai aka ji hausata ba
ta gama zama gangariya ba, sai aka ƙara min
wasu watannin.

Cikin ikon Allah na koyi harshen Hausa, na yi fim
ɗin na farko mai suna AMAL.

Bayan shi na yi finafinai guda biyu, Hisabi da
Matan Aure.

Har ila yau, lokacin da za a yi min fim ɗin da
yawa suna cewa rol ɗin bai dace da ni ba, to
kuma sadda aka ɗora min kyamara sai tsoro ya
mamaye ni, sai da aka yi da gaske, domin ana so
in yi, tukun na zage aka yi aikin da ni.

Dama kuma an faɗa min, kusan duk waɗanda
suka Kannywood da farko sai sun fuskanci
wannan matsalar, amma a hankali sai ta zama
tarihi.

Mene ne fatanki a nan gaba?

Burina in yi rayuwa da kowa lafiya, iyayena
kullum suna yi min addu’a, suna sanya min
albarka.

Ina godiya ga masoyana bisa irin soyayyar da
suke nuna min, ina kuma addu’ar Allah ya saka
kowa da alheri.

Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka dadinkowa24.blogspot.com

Ku hanzarta sanar da 'Yan Uwa da abokanan Arziki sunan Website din Mu me Albarka, don ganin sabbin posting din Mu se ku duba saman website din akwai "Home" sai ku shiga, mungode

Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com

Idan kana/kina da Labarin daku keson asanarwa da Duniya, ko Tambaya,Shawarwari,Hausa Novels, Nishadantarwa,Ilimantarwa,Ko Neman Sani akan ranakun dazamu cigaba dakawo muku Posting na Hausa Novels da Sauran su, zaku iya tuntubar ma'aikatan mu kuturo da Sunan Ku tareda Addreshin Ku tawannan Email din Officialdadinkowa24@gmail.com kyautane zamuyi muku komai don cigaban Al'ummar Hausa bama bukatar kudinka sai dai idan kaikayi niyyar Turowa don siyan Data Saboda acigaba dayin Posting a Kodayaushe batareda dakatawa ba, Website din Mu bashi da Alaka ta kusa ko tanesa da Wani/Wata Dan Siyasa/'Yar Siyasa afadin Duniya Burin mu shine musamu amincewar Al'umma aika da Gudunmawarka,Labari,Shawara da sauran su a Addreshin mu na email ✉💌📩 officialdadinkowa24@gmail.com

Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com

Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri

ALLAH yabar Zumunci Amin🙏

Source By ©Kannymp3

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user

0 comments: