Thursday 26 October 2017

Kasashen Waje: Yadda Za'a Gudanar da Zaben Kenya

Tura Wannan Zuwa Ga

Shugaba Uhuru Kenyatta na Kenya ya yi kira ga
mutane a kan su sauke nauyin da ya rataya a
wuyansu kuma su kada kuria a zaben shugaban
kasa da za a sake yi a yau .

Mista Kenyatta ya ce an tura da jamian tsaro
zuwa sasan kasar daban-daban kuma ya yi
gargadin cewa ba zai amince da tashe tashen
hankula ba.

Jagoran 'yan hammaya, Raila Odinga , ya nemi
magoya bayansa a kan su kauracema zaben ,
saboda ya yi ammanar cewa ba sahihin zabe
bane.

Zaben zai gudana ne bayan da kotun koli ta kasa
saurarar karar da wasu suka shigar a gabanta,
inda suka nemi a dage zaben.

An yi taho-mu-gama tsakanin 'yan sanda da
magoya bayan Mista Odinga a lardin Kisumu.

Gwamnatin kasar ta bada hutu a jiya Laraba
domin mutane su samu damar yin tafiya zuwa
wuraren da aka yi mu su rajista.

Zaman doya da manya da ake yi tsakanin 'yan
siyasa na janyo fargaba kan barkewar tashe
tashen hankula.

Mutum fiye da 1'600 ne suka mutu ya yinda
dubai sun rasa matsugunansu a tashin hankalin
da ya biyo bayan zaben shugaban kasa da aka yi
a 2007.

Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka dadinkowa24.blogspot.com

Ku hanzarta sanar da 'Yan Uwa da abokanan Arziki sunan Website din Mu me Albarka, don ganin sabbin posting din Mu se ku duba saman website din akwai "Home" sai ku shiga, mungode

Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com

Idan kana/kina da Labarin daku keson asanarwa da Duniya, ko Tambaya,Shawarwari,Hausa Novels, Nishadantarwa,Ilimantarwa,Ko Neman Sani akan ranakun dazamu cigaba dakawo muku Posting na Hausa Novels da Sauran su, zaku iya tuntubar ma'aikatan mu kuturo da Sunan Ku tareda Addreshin Ku tawannan Email din Officialdadinkowa24@gmail.com kyautane zamuyi muku komai don cigaban Al'ummar Hausa bama bukatar kudinka sai dai idan kaikayi niyyar Turowa don siyan Data Saboda acigaba dayin Posting a Kodayaushe batareda dakatawa ba, Website din Mu bashi da Alaka ta kusa ko tanesa da Wani/Wata Dan Siyasa/'Yar Siyasa afadin Duniya Burin mu shine musamu amincewar Al'umma aika da Gudunmawarka,Labari,Shawara da sauran su a Addreshin mu na email ✉💌📩 officialdadinkowa24@gmail.com

Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com

Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri

ALLAH yabar Zumunci Amin🙏

Source By ©Bbc Hausa

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user

0 comments: