Saturday 14 October 2017

KADAN DAGA CIKIN TARIHIN KASUWANCI A KANO

Tura Wannan Zuwa Ga

Tsakure daga littafin 'Kano cibiyar Kasuwanci ta
Africa' wanda Marigayi Maje Ahmad Gwangwazo
(Allah yajiqansa da Rahama ya wallafa).

Maigirma Farfesa Sani Muhammad zaharaddin,
babban limamin Kano ya faɗa a ta'alikin littafin
cewar:-

Ana yiwa Kano kirari da "ka misulu alfin, Jalla
Babbar hausa, Gari ba kano ba Dajin Allah! Yaro
ko dame kazo an fika."

Haka kuma marigayi ɗan kishin kasa Sa'adu
Zungur yana cewa a wakarsa Arewa Mulukiyya
ko Jamhuriyya:

Ya! Sarki Alhaji Bayero,
Ga 'yan birni da kanawiyya
Tun Bagauda na Saran kano,
Suka fara fataucin dukiya.

TARIHIN ZUWAN LARABAWA KANO

A shekara ta 1453 miladiyya, a zamanin sarkin
kano Yakubu ɗan Abɗullahi Barja, sarkin kano na
goma sha shidda a mulkin kanawa, waɗansu
larabawa mutanen kasar Gadamus masu fatauci
suka zo daga Tarabulus (Libya), suka sauka a
kano. Sune larabawan farko da suka fara zuwa
kano.

Da saukar waɗannan fatake, sai sukaje wurin
sarkin kano Mallam yakubu, a jujin 'yan Labu, a
lokacin ba'a gina gidan sarautar kano na yanzu
ba, suka ce da sarki a cikin harshen larabci su
fatake ne, suna so su zauna a kano domin suyi
ciniki.

A wannan lokaci kuwa, limamin kano Mallam
Muhammadu Hashimu ne yake fassarawa sarkin
kano abinda waɗannan fataken larabawa ke faɗa
a matsayin tafinta. Daga nan sai sarikin kano
yakubu yayi farin ciki kwarrai da gaske, sannan
yace da shamakin kano ya kaisu sararin nan dake
yamma da unguwar Garke watau Dandali, suyi
gidaje su zauna acan.

Sabili da waɗannan mutane suna da jar fata, sai
mutanen kano suka sa musu suna Turawa. Don
haka koda larabawan suka zauna a wannan wuri,
sai mutane suka sanyawa wurin Dandalin
Turawa. Dalilin sunan dandalin turawa kenan yau
kusan shekaru 553 kenan.

Tun daga wancan lokaci ne larabawa suka
cigaba da zuwa kano fatauci. Kamar misali akwai
Yamalawa mutanen Yamen, da larabawan Tunis
duk sun riski kano, amma kowaɗanne akwai
nau'in kasuwancinsu.

Su larabawan Libya mafi yawan abinda suke
siyarwa kayan alatu ne irin na sarakai da kayan
kamshi da kayan zaki.

Sai dai ya kamata a sani, da wahala ace ga
lokacin da aka soma samar da kasuwanci a kano.

A zamanin da, mutanen kano sunfi riko da noma
fiye da wata harkar kasuwa, amma ana aiwatar
da sana'o'i na gargajiya misalin rini, jima, kira da
sak'a.

Waɗannan su suka haifar da ainihin
kasuwanci, domin mutum zaiyi abu ya siyar ga
jama'a.

Koda yake, a wancan lokacin, ba'a fara amfani da
kuɗi ba a kano, ana yin cinikin furfure ne, watu
ban gishiri in baka manda.

Daga baya ne lokacin da fatake ƙlarabawa ko
Asbinawa da Agalawa suka zo kano, kasuwanci
ya fara kankama a kano.

Haka ma, sauyawar akalar kasuwancin kasar
hausa daga izuwa kano kamar yadda littafin
'Kano civil war and the British Over Rule
1882-1940' na Muhammad F.A ya ruwaito ya
taimakawa kano matuka gaya, domin an samu
cewar fatake sun yiwa katsina tawaye ne, suka
koma kano ɗungurungum da kasuwancinsu.

Zuwan turawa kano kuwa, da kuma yadda suka
samar da farin kuɗi a shekara ta 1930 don yin
musanje ya haɓaka kasuwanci sosai a kano.

Domin a zamanin ne kanawa suka samu buɗewar
ido ainun a harkar, har ya zamana suna yiwa
kansu jagoranci, abinda ya sanya kano ta k'ara
bunksa kuma kenan har ake mata kirari da
Tumbin giwa ko dame kazo an fika.

Kai bama nan ba, har daga kasashen
Kasabalanka ta Morocco da Yunana ta Girka
fararen fata sunzo fatauci kano, bari kuma kuji
yadda suka zo...

Zamu ci gaba Insha ALLAH

Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka dadinkowa24.blogspot.com

Ku hanzarta sanar da 'Yan Uwa da abokanan Arziki sunan Website din Mu me Albarka, don ganin sabbin posting din Mu se ku duba saman website din akwai "Home" sai ku shiga, mungode

Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com

Idan kana/kina da Labarin daku keson asanarwa da Duniya, ko Tambaya,Shawarwari,Hausa Novels, Nishadantarwa,Ilimantarwa,Ko Neman Sani akan ranakun dazamu cigaba dakawo muku Posting na Hausa Novels da Sauran su, zaku iya tuntubar ma'aikatan mu kuturo da Sunan Ku tareda Addreshin Ku tawannan Email din Officialdadinkowa24@gmail.com kyautane zamuyi muku komai don cigaban Al'ummar Hausa bama bukatar kudinka sai dai idan kaikayi niyyar Turowa don siyan Data Saboda acigaba dayin Posting a Kodayaushe batareda dakatawa ba, Website din Mu bashi da Alaka ta kusa ko tanesa da Wani/Wata Dan Siyasa/'Yar Siyasa afadin Duniya Burin mu shine musamu amincewar Al'umma aika da Gudunmawarka,Labari,Shawara da sauran su a Addreshin mu na email ✉💌📩 officialdadinkowa24@gmail.com

Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com

Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri

ALLAH yabar Zumunci Amin🙏

Source By ©Sadiq Tukur Gwarzo

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user

0 comments: