Saturday 14 October 2017

Tarihi: KO KUNSAN ATTAJIRI MAIGIDA MUHAMMADU ABACHA?

Tura Wannan Zuwa

hine Muhammadu Abacha ɗan muhammadu
Sani ɗan Muhammadu, an haife shi shekarar
1905 a garin Maiwa ta Kukawar jihar Borno.

A Maiwa yayi karatun alkurani, daga nan ya
soma kasuwancin shanu tun yana matsahins,
inda yake kawo shanu daga garin zuwa kano da
wasu garuruwa, daga bisani ya komo kano da
zama.

A gidan Bature Mai Amburzin ya soma sauka a
kano, wanda yake auren 'yar uwarsa zara, daga
bisani ya koma unguwar Sabon gari, a wani layi
da har yau ake kira layin Abacha. sannan kuma
babu jimawa sai ya sayi gidansa na kansa a layin
Ibrahim Tawo.

Bisa gudummuwar Maigida Muhammadu Abacha
kungiyar 'Yankasuwar Arewa (Nothern Traders
Association) ta kafu, kuma shine shugabanta na
farko.

Maigida Muhammadu Abacha ya samu damar
zamowa zaɓaɓɓen wakili (councillor) a shekarar
1950.

Ance ahi mai farin jamaa ne anan sabon
gari saboda halayyarsa ta korki. Da taimakonsu
kuma aka bunkasa kasuwannin dake birnin kano
tare da gabatar da wasu manyan aiyuka.

A shekara ta 1963 ne Maigida Muhammadu
Abacha ya kara zama zaɓaɓɓen wakili a
majalisar arewa dake kaduna.

Kasancewar sa
ɗan kasuwa, ance yayi aiki tukuru wajen
kwatowa yankasuwa yanci a gwamnatance, haka
kuma bisa gudunmuwarsa attajirai irinsu Alhaji
Dangote da Alhaji Maude Tobacco da wasunsu
suka soma hurɗa kai tsaye da kamfanin Nigerian
Tobacco Company.

Maigida Muhammadu abacha na ɗaya daga cikin
attajiran da suka taimaka aka sabunta tare da
faɗaɗa babban masallacin juma'a na kano a
shekarar 1954.

Ance taimakon marasa karfi aikin sane, sannan
mutum neshi wanda baya son zalunci.

A karshe Ya rasu ranar talata 6 ga watan mayun
shekarar 1980. Anyi janaizar sa kuma tare da
ɗumbin jama'a.

Daga cikin 'ya'yansane Tsohon shugaban kasa
Janar Sani Abacha ya fito, amma baya dashi
yana da 'ya'ya kimanin sha uku, misalinsu Alhaji
Mustafa, Alhaji Nangana, Hajiya Titi, Hajiya
Fanta, Alh Abdul da wasunsu.

Da fatan Allah ya gafarta masa amin.

Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka dadinkowa24.blogspot.com

Ku hanzarta sanar da 'Yan Uwa da abokanan Arziki sunan Website din Mu me Albarka, don ganin sabbin posting din Mu se ku duba saman website din akwai "Home" sai ku shiga, mungode

Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com

Idan kana/kina da Labarin daku keson asanarwa da Duniya, ko Tambaya,Shawarwari,Hausa Novels, Nishadantarwa,Ilimantarwa,Ko Neman Sani akan ranakun dazamu cigaba dakawo muku Posting na Hausa Novels da Sauran su, zaku iya tuntubar ma'aikatan mu kuturo da Sunan Ku tareda Addreshin Ku tawannan Email din Officialdadinkowa24@gmail.com kyautane zamuyi muku komai don cigaban Al'ummar Hausa bama bukatar kudinka sai dai idan kaikayi niyyar Turowa don siyan Data Saboda acigaba dayin Posting a Kodayaushe batareda dakatawa ba, Website din Mu bashi da Alaka ta kusa ko tanesa da Wani/Wata Dan Siyasa/'Yar Siyasa afadin Duniya Burin mu shine musamu amincewar Al'umma aika da Gudunmawarka,Labari,Shawara da sauran su a Addreshin mu na email ✉💌📩 officialdadinkowa24@gmail.com

Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com

Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri

ALLAH yabar Zumunci Amin🙏

Source By ©Sadiq Tukur Gwarzo

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user

0 comments: