Saturday 14 October 2017

Labari: Abin Kunya ne A Nigeria a Rasa Magani a Gwamnati sai anfita Kasashen Waje-Aisha Buhari

Tura Wannan Zuwa

A Najeriya, 'yan majalisar wakilan kasar za su
gudanar da bincike a kan mawuyacin halin da
asibitin fadar shugaban kasar ke ciki.

'Yan majalisar sun nuna damuwar cewa duk da
irin makudan kudaden da ake warewa asibitin a
kasafin kudin Najeriya , amma ana samun
rahoton rashin kayan aiki a asibitin.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da
uwargidan shugaban Najeriya, Aisha Buhari, ta
zargi asibitin da rashin kayan aiki a makon da ya
gabata, lokacin da ta kai ziyara asibitin da ba ta
da lafiya.

Hajiya Aisha, ta ce abin takaici ne yadda idan
aka duba halin da asibitin fadar shugaban kasa
ke ciki, balle kuma a zo maganar sauran
asibitocin kasar da ke jihohi ko karkara.

Mai magana da yawun majalisar, Hon Abdurrazak
Namdaz, ya shaida wa BBC cewa, tun daga
shekarar 2015 zuwa shekarar da muke ciki, ana
warewa asibitin fadar shugaban kasar kudade a
kasafin kudin kasar, dan haka ya ce dole a
bincika domin gano inda kudaden suka tafi.

Hon. Namdaz ya ce wani kwamiti na musamman
ne aka bawa wuka da naman gudanar da bincike
a kan inda kudaden kula da asibitin fadar
shugaban kasar suka shiga.

Dan majalisar ya ce nan bada jimawa ba
kwamitin zai fara aikinsa, kuma da zarar ya
kammala binciken ya bayar da rahotonsa, za a
sanar da jama'ar kasa komai dalla-dalla.

Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka dadinkowa24.blogspot.com

Ku hanzarta sanar da 'Yan Uwa da abokanan Arziki sunan Website din Mu me Albarka, don ganin sabbin posting din Mu se ku duba saman website din akwai "Home" sai ku shiga, mungode

Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com

Idan kana/kina da Labarin daku keson asanarwa da Duniya, ko Tambaya,Shawarwari,Hausa Novels, Nishadantarwa,Ilimantarwa,Ko Neman Sani akan ranakun dazamu cigaba dakawo muku Posting na Hausa Novels da Sauran su, zaku iya tuntubar ma'aikatan mu kuturo da Sunan Ku tareda Addreshin Ku tawannan Email din Officialdadinkowa24@gmail.com kyautane zamuyi muku komai don cigaban Al'ummar Hausa bama bukatar kudinka sai dai idan kaikayi niyyar Turowa don siyan Data Saboda acigaba dayin Posting a Kodayaushe batareda dakatawa ba, Website din Mu bashi da Alaka ta kusa ko tanesa da Wani/Wata Dan Siyasa/'Yar Siyasa afadin Duniya Burin mu shine musamu amincewar Al'umma aika da Gudunmawarka,Labari,Shawara da sauran su a Addreshin mu na email ✉💌📩 officialdadinkowa24@gmail.com

Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com

Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri

ALLAH yabar Zumunci Amin🙏

Source By ©Bbc Hausa

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user

0 comments: