Sunday 22 October 2017

NIMA BANGA ABIN GODIYA BA A WANNAN LAMARIN- Abba Ahmad Gwammaja

Tura Wannan Zuwa Ga

Zaune muke da wani abokina muna hirar duniya tare da dan nishadi, nan take sai yace dani: "Gaskiya kana matukar kokari yadda kake jurewa wajen rubuce-rubuce a facebook". Nan take kuwa sai na bashi amsa da cewa: "ai ba wani aiki bane, harka ce ta sa kai da juriya, kuma kaima zaka iya".

Fadar hakan ke da wuya sai ya dora da cewa: "Amma kuma in tambayeka mana", ni kuwa nace "Allah yasa na sani".

Sai ya dora da cewa: "Wai me yasa idan 'yan siyasa sukayi wani abin yabo bana ganinka a cikin masu yaba musu?".

Nan take sai nayi murmushi, na dora da cewa: "to menene abin yabo ga maigida dan ya ciyar da iyalinsa?".
Shi kuwa sai ya kada baki yace: "ya zaka amsamin tambaya da tambaya?".

Sai kuwa nace: "ai wannan ita ce tartibiyar amsarka".
Nan take sai yace: "kai fa matsalarka kenan, sai ka ringa yiwa mutane magana mai harshen damo, sai kace a dutsen Dala aka raineka".

Dariya ce ta su6ucemin, tare da cewa: "kai kuma matsalarka kamar ba a kasar hausawa aka haifeka ba".

Ba tare da 6ata lokaci ba yace: "to dan Allah nidai yimin bayani yanda zan gane".

Ni kuwa na kara da cewa: "yanzu kayi magana, to a zahirin gaskiya abinda yake faruwa shine kamar yadda ya zama wajibi akan maigida ya ciyar da iyalansa haka ya zama wajibi akan masu madafun iko su sauke nauyin jama'ar dake wuyansu, domin kuwa mutane ne suka sha wahalar shiga layi ba tare da jin zafin rana ba, suka yanki katin za6e, sannan kuma suka dawo ranar za6e cikin rana suka kara 6ata lokacinsu wajen za6en wadannan mutane ba tare da an biyasu albashi ba, suka kuma jure wurin zaman jiran sakamakon abinda suka za6a, yayinda su kuma mata dake gida suka saka rediyonsu a gaba don sauraron sakamakon, su kuwa matasa a 6angare guda zakaga sun kasa zaune sun kasa tsaye har sai an bayana sakamakon. Kuma idan kayi bincike ba lalle ne iyalan 'yan siyasar suna da katin za6e ba, ballantana kuma asha waccan wahalar dasu.

Bayan bayyana sakamakon kuma idan ba Allah ne ya kiyaye ba tarzoma ta biyo baya, kuma duk akan talaka take karewa.

Shi kuwa wanda yayi nasara zai canza rayuwa, tare da shiga sabuwar daular rayuwa ta hanyar canza muhalli da yanayin zamantakewarsu da jama'a, domin kuwa yanzu duk wani nauyi nasu tun daga kan gidan kwana, motar hawa, kiwon lafiya, ilmi da sauransu ya koma wuyan gwamnati, basu da wata matsala da ta danganci neman kudi.

Haka kuma idan ka dauki wasu 'yan siyasar ka auna albashinsu, alawus da cuwa-cuwar ofis na shekara guda yafice albashin ma'aikaci na shekara goma, duk a dalilin me suka samu wannan in ba mulki da talaka yasha wahala ya za6esu ba?

Sannan kuma da kake zancen sunyi aiki a yaba musu ai aikin na dole ne, domin kuwa idan basu yiba jama'ar da suka za6esu suna da 'yancin tuhumarsu, haka kuma ya zama lalle su amsa tambaya a gaban Ubangiji kan mulkin da aka za6esu".

Banyi kasa a gwiwa ba na dora da cewa: "Idan har talaka zaiyi sanadiyar shigarsu cikin wannan daular duniyar wa ya kamata yayiwa wani godiya a cikinsu?".

Ai kuwa sai yayi caraf yace: "Gaskiyane na gamsu da bayananka, kuma NIMA BANGA ABIN GODIYA BA A WANNAN LAMARIN".

Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka dadinkowa24.blogspot.com

Ku hanzarta sanar da 'Yan Uwa da abokanan Arziki sunan Website din Mu me Albarka, don ganin sabbin posting din Mu se ku duba saman website din akwai "Home" sai ku shiga, mungode

Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com

Idan kana/kina da Labarin daku keson asanarwa da Duniya, ko Tambaya,Shawarwari,Hausa Novels, Nishadantarwa,Ilimantarwa,Ko Neman Sani akan ranakun dazamu cigaba dakawo muku Posting na Hausa Novels da Sauran su, zaku iya tuntubar ma'aikatan mu kuturo da Sunan Ku tareda Addreshin Ku tawannan Email din Officialdadinkowa24@gmail.com kyautane zamuyi muku komai don cigaban Al'ummar Hausa bama bukatar kudinka sai dai idan kaikayi niyyar Turowa don siyan Data Saboda acigaba dayin Posting a Kodayaushe batareda dakatawa ba, Website din Mu bashi da Alaka ta kusa ko tanesa da Wani/Wata Dan Siyasa/'Yar Siyasa afadin Duniya Burin mu shine musamu amincewar Al'umma aika da Gudunmawarka,Labari,Shawara da sauran su a Addreshin mu na email ✉💌📩 officialdadinkowa24@gmail.com

Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com

Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri

ALLAH yabar Zumunci Amin🙏

Source By  ©Abba Ahmad Gwammaja

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user

0 comments: