Sunday 22 October 2017

HANYOYI 15 DA ZAKA SA MATAR KA CIKIN FARIN CIKI A KODA YAUSHE DA KUMA SAMUN KYAKKYAWAR ZAMATAKEWA A TSAKANINKU

Tura Wannan Zuwa Ga

1- Idan ka shiga gidan kace
Assalamualaikum' shaaidan zai bar
gidan!

2- Ka rika yawan bata labarai.
Saboda Allah (S.w.t) ya sanar da mu
dan Adam yana son labari.

3- Ka zama mai yawan yabonta,
kuma a wajen da ake kusheta ka
nuna bacin ranka.

4- Ka zama mai yawan bata
kyaututtuka. Kyauta tana kara
dankon soyayya.

5- Ka rika mantawa da wasu daga
cikin kurakuranta ka nuna baka ma
san ta yi ba. Kuma ka dauka a
matsayin abinda ya shude, karka
ajiye shi a zuciyarka

6- Ka nuna mata tausayawarka
gareta a fili, musamman a lokacin da
take da juna biyu

7- Kada ka daukaka abokanka fiye da
matarka.
(lokuta da dama wasu mazan suna
fifita abokansu na karatu ko na
sana,a sama da matansu)

8- Ka rika nuna mata babu wata
macce dake gabanka sai ita, Ka nuna
mata kullum a matsayin sabuwa take
a gurinka.

9- Ka rika tunawa da ita a cikin
addu'arka. Hakan zai kara kauna
tsakaninku.

10- Kada kayi mata gori akan dukkan
abubuwan da kake mata, kamar
siyan sutura ko abinci,Saboda daman
hakkinta ne ka kawo mata,sannan
kasan ce wa abincin kawai kake
kawowa amma Allah shi ne mai
ciyarwa.

11- Shaidan ne abokin gabarka ba
matarka ba,Lokuta da dama idan
mata da miji suka dan samu sabani
har zata kai ana maida martani cikin
fushi,To ka dauka a ranka cewa ba
ita bace take gayama kaza da kaza
a’a shaaidan ne ke zugata, Saboda
shi yana mutukar son ayi saki. ( A
rika hakura don a bashi kunya )

12- ku rika cin abinci tare matarka
har Ka dauki abinci ka saka mata
abaki. Annabi (s.a.w) ya ce, "abincin
ba cikinta kadai zai shiga ba, zai
huce har zuwa zuciyarta."

13- Ka kasance mai yawan yi mata
murmushi/ fara'a domin Manzo
(s.a.w) ya ce: "Duk wanda ya nunawa
matarsa fara'arsa to dai-dai yake da
yin sadaka."

14- Ka zama mai yawan neman
shawararta. (wasu suna ce wa ba,a
shawara da mata). To ku sani ce wa
manzo (s.a.w) ya kasance yana
shawara da matansa.

15- Kar ka Boye mata damuwar ka,
farin cikinka ko bakin cikinka.
Domin ita magani ce a tattare dakai.

ALLAH yasa mu dace, Amin

Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka dadinkowa24.blogspot.com

Ku hanzarta sanar da 'Yan Uwa da abokanan Arziki sunan Website din Mu me Albarka, don ganin sabbin posting din Mu se ku duba saman website din akwai "Home" sai ku shiga, mungode

Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com

Idan kana/kina da Labarin daku keson asanarwa da Duniya, ko Tambaya,Shawarwari,Hausa Novels, Nishadantarwa,Ilimantarwa,Ko Neman Sani akan ranakun dazamu cigaba dakawo muku Posting na Hausa Novels da Sauran su, zaku iya tuntubar ma'aikatan mu kuturo da Sunan Ku tareda Addreshin Ku tawannan Email din Officialdadinkowa24@gmail.com kyautane zamuyi muku komai don cigaban Al'ummar Hausa bama bukatar kudinka sai dai idan kaikayi niyyar Turowa don siyan Data Saboda acigaba dayin Posting a Kodayaushe batareda dakatawa ba, Website din Mu bashi da Alaka ta kusa ko tanesa da Wani/Wata Dan Siyasa/'Yar Siyasa afadin Duniya Burin mu shine musamu amincewar Al'umma aika da Gudunmawarka,Labari,Shawara da sauran su a Addreshin mu na email ✉💌📩 officialdadinkowa24@gmail.com

Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com

Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri

ALLAH yabar Zumunci Amin🙏

Source By ©Fadila M. Idris

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user

0 comments: