Sunday 22 October 2017

Ina Nan Daram-Dam A cikin Addinin Musulunci –Rahama Sadau

Tura Wannan Zuwa Ga

Shahararriyar yar wasan kwaikwayon nan ta
kannywood, Rahama Sadau ta maida martani
dangane da wani audio na jita-jita da aka rinka
yadawa a kafar sadarwa ta WhatsApp kan cewar
wai zata bar addinin Musulunci sakamakon tayi
da aka yi mata da wasu miliyoyin dalolili, da
kuma samun matsayin shiga masana’antar
wasan kwaikwayo ta Hollywood.

Ta bayyana cewa wannan zance ne da bashi da
tushe ko makama wanda kuma an kirkire shi ne
don a bata mata suna, inda ta nuna damuwa
matuka sannan kuma ta bukaci jama’a da suyi
watsi da wannan recording na audio da ake
yadawa.

Ta kara da cewar sana’arta baza ta
shafi addininta ba ballantana ma har ace zata
sayar da imaninta wa wasu yan dalolili.

Idan zaku iya tunawa, a can bayane jarumar ta
fito a wani faifan Bidiyon waka tare da mawakin
hiphop Classiq
wanda hakan ya jawo kakkausar suka a gareta
inda daga bisani hakan ya janyo MOPPAN Ta kori
Jarumar daga kannywood wanda sanadin hakan
ne ta samu gayyata zuwa masana’antar fina-finai
ta Hollywood dake kasar Amurka.

“Abin ya kona min rai matuka, musamman ma ta
yadda har wasu manyan malamai suka yarda da
wannan jita-jitar da aka rinka yadawa kuma suka yi
amfani da ita wajen suka ta ba tare da sunyi
bincike don tabbatar da sahihancin labarin ba,
wanda hakan ya harzuka yan uwa da abokan arziki.

Abisa wannan dalilin ne naga ya zama wajibi na
fito na yiwa jama’a bayani. “

” Ni Rahama Sadau inaso in shaidawa al’umma
gami da jaddada musu cewar wannan zancen da
ake yadawa akai na karya ce mara tushe da aka
kirkiro don a bata mun suna, saboda haka ina kira
ga masoya na da su yi watsi da wannan jita-jitar. ”

Ta kara da cewar” in baku manta ba, Akon wanda
yake musulmi ne kuma dan asalin kasar Senegal ya
fuskancin irin wannan kalubalen daga kafafen yada
labarai na can kasar ta su. ”

Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka dadinkowa24.blogspot.com

Ku hanzarta sanar da 'Yan Uwa da abokanan Arziki sunan Website din Mu me Albarka, don ganin sabbin posting din Mu se ku duba saman website din akwai "Home" sai ku shiga, mungode

Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com

Idan kana/kina da Labarin daku keson asanarwa da Duniya, ko Tambaya,Shawarwari,Hausa Novels, Nishadantarwa,Ilimantarwa,Ko Neman Sani akan ranakun dazamu cigaba dakawo muku Posting na Hausa Novels da Sauran su, zaku iya tuntubar ma'aikatan mu kuturo da Sunan Ku tareda Addreshin Ku tawannan Email din Officialdadinkowa24@gmail.com kyautane zamuyi muku komai don cigaban Al'ummar Hausa bama bukatar kudinka sai dai idan kaikayi niyyar Turowa don siyan Data Saboda acigaba dayin Posting a Kodayaushe batareda dakatawa ba, Website din Mu bashi da Alaka ta kusa ko tanesa da Wani/Wata Dan Siyasa/'Yar Siyasa afadin Duniya Burin mu shine musamu amincewar Al'umma aika da Gudunmawarka,Labari,Shawara da sauran su a Addreshin mu na email ✉💌📩 officialdadinkowa24@gmail.com

Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com

Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri

ALLAH yabar Zumunci Amin🙏

Source By
©Zaharaddeen Hamisu Dabai

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user

0 comments: