Friday 17 November 2017

Hausa Films: Sakar wa ’yan kasuwa mara ne mafita a Najeriya – Aliyu Mustapha

Tura Wannan Zuwa Ga

Asa ranar Juma’ar makon jiya ce
Manajan Edita na Sashin Hausa na gidan rediyon
Muryar Amurka, Alhaji Aliyu Mustapha Sakkwato
ya kawo ziyara hedkwatar Kamfanin Media Trust,
mai buga jaridun Daily Trust da Aminiya domin
gabatar wa mahukuntan kamfanin da wani fim da
gidan rediyon ya shirya mai suna: “Boko Haram:
Tattakin Bakar Akida,” don nuna jajircewar jama’a
a yankunan da yakin Boko Haram ya shafa.

Wakilinmu ya tattauna da fitaccen dan jaridar kan
dalilin shirya fim din da sauran batutuwa:

Me ya ba ku sha’awa kuka shirya wannan fim
kan matsalar Boko Haram?

Na farko dai Najeriya ba kanwar lasa ba ce
babbar kasa ce, ba kasar da mutanen duniya za
su zauna su manta da ita ba ce, Najeriya
muhimmiyar kasa ce da kasashen duniya suke da
sha’awa ainun a kan abin da ke faruwa a cikinta.

Sha’anin Boko Haram abu ne da aka yi shekara
da shekaru ana fama da shi, kuma sha’ani ne da
ya jawo wa kasar nan asara ta rayuka da ba sa
ma kirguwa. Duk da ana cewa mutum dubu 20
dubu meye, Allah kadai Ya san rayukan da aka
rasa.

To Muryar Amurka ta dauki kudiri a kanta yanzu
wajen shekara biyu tana kokari ta shirya wannan
shiri na musamman, ta nuna wa duniya halin da
mutane suka shiga. Ba wai shi kansa yaki ba
gadan-gadan, amma hali da kuma tasirin wannan
lamari a kan mutanen da ya shafa, musamman
mutanen sashin Arewa maso Gabas. Shiri ne da
ake kira “Boko Haram: Tattakin Bakar Akida,” da
Ingilishi kuma ana kiransa “Boko Haram: Journey
for Ebils.”

Shiri ne da Muryar Amurka ta shirya ta
kawo domin ta nuna wa mutane wannan hali da
mutane suka shiga da kuma nuna cewa mutanen
Najeriya suna da jajircewa. Sau da yawa akan ga
Najeriya sai ta yi kamar za ta auka cikin masifa,
cikin rami, sai ta dawo. To, shi ne babban
darasin wannan shirin.

Ku ’yan Najeriya da ke sashin Hausa ne kuka yi
tunanin haka ko mahukuntan gidan rediyon?

A’a, mahukuntan ne, ai wannan shirin ba na
Hausa ba ne na Ingilishi ne aka zo aka fasasara
shi da Hausa. Saboda shiri ne na Muryar Amurka
bakin dayanta, yanzu haka ma ana fassara shi a
harsunan duniya kamar Faransanci da Larabci da
Swahili da Hindu da sauransu za a rarraba. Ko
bayan nan Najeriya da na zo, zan je Jamhuriyyar
Nijar insha Allahu domin mu je mu yi wa mutane
bayani game da shi.

Bayan ’yan Najeriya sun kalli wannan fim wane
mataki kuke so su dauka ko wane darasi kuke
son isarwa?

Darasin da muke so mutane su samu shi ne na
farko su jinjina wa jajircewar ’yan kasar da
lamarin ya shafa. Saboda mun ga tarihin
kasashen da dama da suka shiga irin wannan hali
na yaki da ta’addanci, mun ga yadda suka
karkare. Kuma mun san inda aka fito, saboda
haka yanzu Allah Ya kawo sauki, ba a gama da
shi ba, har yanzu yana nan. Kuma muna so mu
nuna wa ’yan Najeriya cewa kafofin watsa labarai
irinsu Muryar Amurka sun damu da halin da suke
ciki. Kuma duk da cewa mu ’yan Najeriya ne,
galibin wannan aiki wadanda ba ’yan Najeriya ba
ne suka yi basirar cewa ya kamata a yi shi.
Babban darasin, muna so mu nuna wa duniya
cewa Najeriya dai, wallahi ta wahala da wannan
hali da ta shiga.

Mutane ko sun rayu, suna
rayuwa a cikin wahala, saboda haka ya kamata a
fahimci Najeriya, a kyautata wa Najeriya, a kuma
a taya ta yakin baki daya, shi ne babbar
manufarmu.

Wadansu suna ganin kamar cewa kila ko bidiyon
nan ya yi sauri ganin cewa har yanzu yakin nan
bai kare ba, me za ka ce?

Ai kamar yadda na ce, ba a kan yaki ba ne aka yi
fim din, wahalar kuma ba a fita cikinta ba.

Yanzu
in ka dauki dubbai ko in ce miliyoyin mutane na
yankin Tafkin Chadi, wajen mutane miliyan 70 ba
’yan Najeriya kadai ba, ’yan Chadi, ’yan Kamaru
’yan Nijar, duk sun dogara ne a kan noma da
kamun kifi. To harkar Boko Haram ta zo ta sanya
wa wannan birki, ba a iya yi. Ai kuwa in ka ce
mutum bai iya sana’a, ma’ana bai iya ciyar da
iyalinsa ke nan, in kuwa bai iya cin abinci ka san
wahala ta zo ke nan, sun rasa rayuka. To ba
yakin ba ne, yakin kowa ya san bai kare ba, ana
nan ana yi, amma an san an ci karfin yakin.

Amma kafin a ci karfin yakin sai da aka wahala,
amma mutane sun jure wa wannan wahala, shi
ne ake son fitowa da shi fili.

Mu koma kan kungiyarku ta Zumunta da ke
Amurka, wace rawa ta taka a kan wannan lamari
na Boko Haram?

Ka san kungiyar nan ni ne shugabanta na farko
na kasa baki daya. Ni ne shugabanta na farko na
Washington DC. Mu ne muka fara dauko manyan
shugabannin Najeriya irin su Allah Ya jikansa
Sarkin Kano Ado Bayero, su Allah Ya jikansa
Maitama Sule da sauran manyan shugabannin
Najeriya.

Tun wadancan shekaru har yanzu ba
mu daina wannan ba. Na biyu fiye da shekara 20,
cikin natsuwa ba da ma mutane sun sani ba, har
kwanan gobe ’ya’yan wannan kungiya suna bayar
da tallafin karo ilimi kyauta ga ’yan Arewa. Duk
jihohin 19 har rokon jihohi muke yi su ba mu
yaran da za mu ba su sukolaship kuma yana nan
har yanzu ba mu daina ba. Na uku, har yanzu
mutanenmu suna zuwa Najeriya su haka rijiyoyin
burtsatse, ina ba ka ’yan ayyukan da suke yi ne
tukuna.

Ta fannin wannan yakin da ake yi, ka san duk
sana’ar da za ka yi tunani a kanta a duniyar nan,
akwai dan Najeriya da ke yi a Amurka, kuma ga
tarin yawan da suke da shi a Amurka, saboda
yawan ’yan Najeriya, har siyasa suke shiga a
Amurka.

Na san Magajin Gari dan Najeriya da
aka taba yi a wajejen Jihar Oregon. Kuma zaben
nan da aka yi na su Donald Trump, ’yan Najeriya
da yawa sun tsaya takara, musamman ma mata,
wajejen su New York da sauransu. Suna ba da
tarbace na wajen rubuce-rubuce, suna ba da
tarbace na kudade, suna ba da tarbace na hada
tarurruka, suna ba da tarbace wajen bayar da
shawarwari da sauransu. Duk abin da ka ga ’yan
gida suna yi gwargwado, su ma a can suna yi.
Kuma wallahi abin yana ci musu rai cewa kasar
tana cikin wannan hali.

Kasancewa bayar da tallafin karo ilimi na cikin
ayyukanku, wane yunkuri kuke yi don tallafa wa
marayun da yakin Boko Haram ya samar?

Wato in muka tashi bayar da sukolaship din nan
mukan tuntubi jihohi ne alal misali mu ce su
kawo mana mutum goma-goma, ba lallai sai
wadanda wannan lamari ya shafa ba. Kamar
yadda na fada maka su wadannan yankuna ba
mu tsaya kan tallafin ilimi ba, muna bayar da
taimako na kudi, muna bayar da taimako na
magunguna, muna ba da kwamfutoci da yawa na
karatu. Ni kaina na taba zuwa da kwamfutoci da
yawa aka rarraba wa jami’o’i da yawa a Kaduna.

Saboda haka kokarin da muke yi tare da sauran
kungiyoyi na ’yan Najeriya da suke Amurka shi ne
iya gwargwadon abin da za mu iya yi, kuma
muna ci gaba da yi.

Zuwa yanzu yaya girman nasarar da kuka samu
daga lokacin da ka shugabanci kungiyar?

Na fa daina shugabancin.

Amma kana halartar tarurrukanta ko?
kwarai kuwa.

To wasu nasarori kake tsammanin kun samu?

Na farko a wurina nasara ta farko ita ce,har
yanzu muna nan tare a kungiyar. Ka san yadda
kungiyoyi ba su dadewa musamman na ’yan
Najeriya. Bai wai ba mu da kalubale irin na
sauran kungiyoyi ba ne, amma abin alfahari a
wurina shi ne cewa kungiyar nan ta Zumunta ita
kadai ce kungiya da take wakiltar dukan
Arewacin Najeriya.

Amma in ka taba kungiyoyin
’yan Kudu suna da kungiya sun fi 500. Kowane
kauye yana da kungiya, amma ta Arewar nan
daya ce. Kuma ka san yadda tsarinta yake ita
ma tana da kabilu da yawa. Wannan ita ce
nasara ta farko.

Ta biyu, kulawar da aka bai wa sha’anin ilimi.

Ta uku, mun fuskanci wahalhalu, kuma abin
takaic ne muna fuskantar wahalhalu, shi ne
kokarin da muka yi na dibar ’yan kasuwarmu mu
kai su Amurka mu hada su da na can, domin
tarurrukan da muka shirya irin wadannan ba sa
da iyaka. Ko kafin in taso, tunanin da ake yi shi
ne a kira ’yan kasuwa na Najeriya ba ma na
Arewa ba.

Don an sha daukar dawainiyar haka,
saboda abin na Najeriya ne gaba daya. Saboda
duk lokacin da ake bikin samun ’yancin kai
kungiyarnu tana taka rawa.
Sannsn wata nasarar da muke samu ita ce ta
bunkasa al’adunmu na gida. Kafin in so a Jihar
Maryland an yi wani taro saboda sun san mu duk
wanda zai yi wani taro zai zo ya ce, suna
gayyatarmu, musamman in taro ne na kasashe,
saboda so su ga abincinmu su ga kayanmu na
sawa, suturarmu, musamman na mata. Kade-
kadenmu da wakokinmu da sauransu, kuma a zo
a yi su a burge. Mutanen Amurka suna son al’ada
kwarai da gaske, komai tsadar kwat da za ka sa,
rigar jamfa mafi araha ta fi ta kima a idonsu.

Wa
za ka burge da kwat? Kuma in ka sa kwat ba a
sani ina ka fito.

A karshe wane sako kake da shi ga al’ummar
Najeriya kan yadda za su bunkasa ilimi, ganin
ku da kuke waje kun damu da shi?
Wato bari in gaya maka matsalarmu ta kasar nan
tamu, komai ya doru a kan gwamnati ce.

Gwamnati ce ke dauke da kashi 99 cikin 100 na
lalurorin rayuwar yau da kullum ta Najeriya. In ba
ka sha’ani da gwamnati ma a Najeriya ba kai
ko’ina. Yanzu dubi rigimar da ake yi a Kaduna
kan malaman makaranta, wai ba sa iya cin
jarrabawar da ’yan firamare ma suke yi. Ina abin
kunyar da ya kai haka. Kuma gwamnatin da ake
cewa za ta kore sui ta ce za ta sake daukar
wadansu.

A Turai, cinka da shanka da ruwanka
ba ruwan gwamnatin da su, kai ko a harkar
watsa labarai in baya ga gidan rediyonmu duk
Amurka gwamnatin ba ta rediyo ba ta da talabijin
ba ta da jarida ko daya.

Duk abin da ka gani
mutum yana ci yana sha yana karantawa yana
hawa yana meye na wani kamfani ne na masu
zaman kansu.

Mai kamfanin wutar nan in ka biya shi ya ba ka
wutar, in ba ka ba shi ba, ya yanke. Shi kuma
idan bai ba ka wuta isasshiya sai ya bar ka ya
tafi wani wuri. To kowa yana da inda zai je kuma
kowa yana da kishiya. Amma mu nan sha’anin
ilimin nan yanzu makarantar da ka yi da wadda
na yi, lokacin da muka yi su sun fi inganci da
yanayin yau.

Wane irin lalaci ne wannan?

Gada
nawa ka sani a kasar nan wadda har yanzu tana
nan irin wadda in mota daya ta zo sai ta jira
wata ta wuce?

Amma ka ji irin kudaden da ake
wabta na da lokacin kasafin kudade.
Lokaci ya yi da ya kamata a karfafa wa mutane
masu zaman kansu su samu dama su gudanar
da wasu daga cikin ayyukan nan.

Harkar wutar
nan tun shekara nawa ake batunta amma har
yanzu, abin kunya ne ga Najeriya a ce har yanzu
wuta matsala ce.

Na je Burkina Faso, wadda in
ka duba jerin gwanon kasashe a harkar tattalin
arziki ita ce kusan ta karshe, wallahi har na bar
ta sau daya na ga wuta ta yi dil-dil, ita ta tsaya
ba a dauke ba. Don haka a ba mutane dama a yi
jari-hujja shi ke nan.

Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka dadinkowa24.blogspot.com

Ku hanzarta sanar da 'Yan Uwa da abokanan Arziki sunan Website din Mu me Albarka, don ganin sabbin posting din Mu se ku duba saman website din akwai "Home" sai ku shiga, mungode

Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com

Idan kana/kina da Labarin daku keson asanarwa da Duniya, ko Tambaya,Shawarwari,Hausa Novels, Nishadantarwa,Ilimantarwa,Ko Neman Sani akan ranakun dazamu cigaba dakawo muku Posting na Hausa Novels da Sauran su, zaku iya tuntubar ma'aikatan mu kuturo da Sunan Ku tareda Addreshin Ku tawannan Email din Officialdadinkowa24@gmail.com kyautane zamuyi muku komai don cigaban Al'ummar Hausa bama bukatar kudinka sai dai idan kaikayi niyyar Turowa don siyan Data Saboda acigaba dayin Posting a Kodayaushe batareda dakatawa ba, Website din Mu bashi da Alaka ta kusa ko tanesa da Wani/Wata Dan Siyasa/'Yar Siyasa afadin Duniya Burin mu shine musamu amincewar Al'umma aika da Gudunmawarka,Labari,Shawara da sauran su a Addreshin mu na email ✉💌📩 officialdadinkowa24@gmail.com

Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com

Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri

ALLAH yabar Zumunci Amin🙏

Source By ©Aminiya

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user

0 comments: