Friday 17 November 2017

Labarin Gaggawa: Tsoho ya kashe mahaifiyarsa mai shekara 100 kan maita

Tura Wannan Zuwa

Daga dama Kwacha Manu dadansa Likita Manu
da ake zargi da kashe Inne mai shekara 100 a
Neja
Wani tsoho mai kimanin shekara 80 mai suna
Kwacha Manu har yanzu bai nuna nadama ba
kan kashe mahaifiyarsa mai suna Inne Kaiyo
bayan shafi kwanaki a tsare a hannunyan
sanda.

“Na yi mata duka kan kashe jikata, Magajya ta
hanyar maita,” ya shaida wa manema labarai a
hedkwatar ‘’yan sandan Jihar Neja da ke Minna,
inda aka gabatar da shi da wadansu mutum 13
kan zargin aikata laifuffuka daban-daban a
karshen makon jiya.

Kwacha ya yi ta kokarin kare aika-aikarsa da ta
dansa mai shekara 40, mai suna Likita wanda aka
kama shi kana bin da ’yan sanda suka bayyana
da zargin “aikata kisa kai.” Ya shaida wa masu
bincike cewa: “Ta kashe Magajiya wadda a
kullum take kula da ni.”

Magajiya Likita mai shekara 17, kuma jikar
Kwacha ta hadu da rashin lafiya ne a tsakiyar
watan Oktoban da ya gabata a kauyen Marke
Gada Maja da ke karamar Hukumar Rijau a Jihar
Neja. An ce cutar ta ki jin magani. Kuma rashin
lafiyar ya dada muni lamarin da ya kai ga
rasuwarta a ranar Alhamis mako biyu da suka
gabata.

“Jikata, Magajiya ta rasu ne bayan an kai ta
asibiti da misalin karfe 8 na safe,” inji Kwacha.
Ya ce, abin takaicin mahaifiyarsa Inne ce
sanadiyyar rasuwar. “Ita ta kashe Magajiya,” ya
nanata. Kuma da aka tambaye shi wane tabbaci
yake da shi cewa Inne ce ta kashe tattaba
kunnenta, sai Kwacha ya ce, ba Magajiya ce
kadai ta rasu ba a sakamakon ayyukan maita na
Inne.

A cewarsa it ace ta shida a baya-bayan
nan.

Da aka tambaye shi kan hujjar da za ta alkanta
Inne da rashin lafiyar Magajiya da kuma
rasuwarta, sai ya ce: “Magajiya ta rika rokon
Inne ta sake mata kurwarta a lokacin da cutar ta
ki jin magani. Kuma dukanmu mun rika rokn
mahaifiyata ta sake ta amma ta ki.”

Ya ce, ya
kadu lokacin da aka kawo gawar Magajiya gida
bayan ta rasu a hanyar kai ta asibiti. “Na yi fushi
da mahaifiyata, kuma saboda fusata na doke ta a
kafafuwanta da wani rake inda ta rasu,” inji shi.

Sai dai sabanin Kwacha, dansa Manu, wanda shi
ne mahaifin Magajiya, cike yake da takaicin abin
da ya faru a ’yan kwanakin nan. Rasuwar
Magajiya wadda ita ce ’yarsa ta biyu da kuma ta
mahaifiyar babansa wadda ta jawo su ga fadawa
a hannun ’yan sanda.

Shi ne ya fara kai rahoton lamarin ga ’yan sanda,
amma aka hada da shi cewa da hannunsa a
lamarin duk da cewa rundunar ’yan sandan ta ce
har yanzu ana ci gaba da bincike a kai.

Ya yi ta kokarin danne hawayen da ke kokarin
zubo masa a lokacin ganawar da manema labarai
a hedkwatar ’yan sandan. “Ina so ne kawai in
koma gida,” ya fadi cikin kuka, yana rokon
manema labarai su taimaka su roki ’yan sanda su
sake shi.

Ya ce yana Rijau lokacin da lamarin ya faru,
kuma yana mamakin dalilin da ’yan sanda za su
tsare shi tare da mahaifinsa. “Ban san dalilin da
’yan sanda suke tsare da nib a. Baya ga zafin
rashin ’yata, wadansu ’ya’yana biyu yanzu haka
suna fama da mugun rashin lafiya a gida. Tun
lokacin da lamarin ya auku ko gawar ’yata ban
gani ba. Kuma ba ni da wata matsala da
mahaifina kana bin da ya faru, wannan kaddarar
Ubangiji ne.”

Sai dai ’yan sanda suna kallon lamarin ta wani
gefe. Batu ne da ya shafi “Kisan kai,” inji
Sufurtanda Abigail Onaeze, Kakakin Rundunar ta
shaida wa manema labarai a ranar Asabar da ta
gabata lokacin gabatar da wadanda ake zargin.
Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, ba a
gabatar da wadanda ake zargin a gaban kotu ba,
saboda ba a kammala binciken lamarin ba.
Wata majiya ta kusa da rundunar ta ce, ’yan
sanda suna bincikin lamarin a tsanake. Ta ce,
al’ummar kananan hukumomin Rijau da Mashegu
an san su da ‘batutuwan’ da suka shafi maita.

“Akwai lokacin aka rika kashe mata har ma da
kananan yara bisa zargin maita,” inji majiyar.
Malam Sulaiman Rijau, wani mai kasuwancin
hatsi daga yankin ya tabbatar da wannan ikirari
inda ya ce: “Lamarin abin takaici ne da ke sosa
zukata.” Ya ce duk da cewa Musulmi da Kirista
ne mafiya rinjaye a yankin, rikice-rikicen da ke
tasowa bisa zargin maita sun zama ruwan dare a
tsakanin al’ummar da suka yarda da ita.
Wani masanin tunanin dan Adam, Abubakar
Abdulkadir ya ce, tsoro da jahilci suna taka
muhimmiyar rawa a al’amarin. “Abin takaici ne ci
gaba da aukuwar wannan camfi na tsohuwar
al’ummar Afirka.

ana aukuwa ne saboda gurgun
tunani da damfara ga al’adu da kuma karancin
koyarwar addini; kuma wani abin takaicin shi ne
a karni na 21 a Najeriya a daidai lokacin da
addinan gargajiya ke bacewa, ana ci gaba da
samun hakan sosai musamman a yankunan
karkara,” inji shi.

Ya ce, mutane suna dora wa maita laifin rashin
samun Amfanin gona da aukuwar cuta da
mutuwa, haka ma lalacewar gonaki da sauran
abubuwan bakin ciki.

Ya tabbatar da cewa an fi samun haka a
kauyukan Mashegu da Rijau fiye da sauran
yankunan jihar. “Babban abin daga hankalin shi
ne kowace cuta koda wadda za a iya maganinta
ce, sai a jingina ga maita, wanda hakan ke kawo
yawan mace-mace musamman a lokacin da
cututtuka masu yaduwa suka barke,” inji shi.
Ya ce: “Wannan mugun tunani ne ya jawo mace-
macen da za a iya kauce musu ga yaran da ke
yankin karkarar Mashegu lokacin da cutar
sankarau ta barke a farkon wannan shekara.”

Mece ce mafita? Abubakar ya bayar da shawarar
a rika gudanar da gangami da kamfe din wayar
da kan jama’a ta hanyar amfani da malaman
manyan addinan nan biyu da kuma sarakuna a
kan lamarin.

“Akwai bukatar a sake fasalin dokoki
don dakile ci gaba da musgunawar da ake yi ga
yara da sunan maita. Kuma akwai bukatar a
samu dokokin da za su haramta musguna wa
mutane bisa tunanin su mayu ne. Dokokin ya
kamata a rika aiwatar da su, ta yadda za a rika
hukunta shugabannin addini da na al’umma da
suke karfafa hakan,” inji shi.

Babu abin da zai kawar da maita a duniya
Baba Impossible

Wani masani abin da ya shafi camfe-camfe da
al’adu a Sashin Koyar da Harsunan Najeriya a
Jami’ar Bayero, Kano, Dokta Muhammad Tahar
Adamu da ake kira da Baba Impossible, ya ce
babu wani abu na ci gaban zamani da zai iya
kawar da maita a duniya.

Dokta Muhammad Tahar ya bayyana cewa maita
al’ada ce, wadda ake samu a kowace irin
al’umma ta duniya.

“Idan aka duba za a ga babu
al’ummar da ba ta da maita tun daga kan
Larabawa da Turawa da mutanen Afirka, har
zuwa nan Najeriya.

Idan aka sauko a nan
Najeriya za a samu cewa kowace kabila ta yi
imani da maita.

Haka kuma akwai irin sunan da
kowa yake kiranta da shi. Ita maita ta zama
al’ada mai zaman kanta, wacce babu wani ci
gaba da zai iya kawar da ita, zamani daban ita
kuma maita daban.

Zancen ma a ce wai karatun
boko ko wani wayewa zai canja tunanin mutane
a kan maita bai taso ba,” inji shi.

A cewar malamin jami’ar, maita aba ce da za a
ci gaba da yin ta ba wai za ta kare ba, “Matukar
ka yarda ba za ka raba mutum da al’adarsa ba,
to haka ba za ka iya raba shi da abubuwan da ya
yi imani a kansu ba ciki kuwa har da maita,” inji
shi.

Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka dadinkowa24.blogspot.com

Ku hanzarta sanar da 'Yan Uwa da abokanan Arziki sunan Website din Mu me Albarka, don ganin sabbin posting din Mu se ku duba saman website din akwai "Home" sai ku shiga, mungode

Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com

Idan kana/kina da Labarin daku keson asanarwa da Duniya, ko Tambaya,Shawarwari,Hausa Novels, Nishadantarwa,Ilimantarwa,Ko Neman Sani akan ranakun dazamu cigaba dakawo muku Posting na Hausa Novels da Sauran su, zaku iya tuntubar ma'aikatan mu kuturo da Sunan Ku tareda Addreshin Ku tawannan Email din Officialdadinkowa24@gmail.com kyautane zamuyi muku komai don cigaban Al'ummar Hausa bama bukatar kudinka sai dai idan kaikayi niyyar Turowa don siyan Data Saboda acigaba dayin Posting a Kodayaushe batareda dakatawa ba, Website din Mu bashi da Alaka ta kusa ko tanesa da Wani/Wata Dan Siyasa/'Yar Siyasa afadin Duniya Burin mu shine musamu amincewar Al'umma aika da Gudunmawarka,Labari,Shawara da sauran su a Addreshin mu na email ✉💌📩 officialdadinkowa24@gmail.com

Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com

Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri

ALLAH yabar Zumunci Amin🙏

Source By ©Aminiya

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user

0 comments: