Friday 17 November 2017

Nigeria: Ka kara kwazo, yan Nigeria na cikin bakar wahala, inji Tinubu ga Buhari

Tura Wannan Zuwa

Shugaban jam’iyyar, APC, kana tsohon Gwamnan
jihar Lagos, Bola Tinubu, ya shawarci shugaba
Muhammadu Buhari da yayi amfani da ragowar
lokacinsa na mulki wajen gina Nigeria domin ceto
yan Nigeria dake cikin wahalar rayuwa.

Mista Tinubu yayi wannan kiran ne a yau Alhamis
lokacinda yake jawabi a wajen taron kaddamar
da littafin da akayi domin hasashen tafiyar
Gwamnatin Buhari.

Yace kodayake akwai shugaba Buhari na kokari
matuka amma akwai bukatar ya kara dagewa
domin yan Nigeria na cikin matsananciyar wahala
ta yunwa, rashin, rashin aikinyi da matsin rayuwa

Yace idan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya
baiwa fannin noma da kiwo da masana’antu fifiko
za’a samu sassaucin kuncin da ake fuskanta.

Ya bada misali da kasashen England da Japan da
China wadanda suka tsara manufofi kyawawa a
fannin masana’antu da kere kere shi yasa sukaci
gaba.

‘Don haka inji Tinubu lokaci yayi da Nigeria zata
rika kere ababe masu fa’ida wadanda za’a iya
sayarwa ba kere ababen da suke da saukin
kerawa ba.

Sannan kuma inji shi lokaci yayi da
Gwamnati zata tashi daga duniyar fadi a baki
kawai zuwa duniyar fadi da cikawa musamman
abunda ya shafi kyawawan manufofinta a gani a
kasa.

Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka dadinkowa24.blogspot.com

Ku hanzarta sanar da 'Yan Uwa da abokanan Arziki sunan Website din Mu me Albarka, don ganin sabbin posting din Mu se ku duba saman website din akwai "Home" sai ku shiga, mungode

Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com

Idan kana/kina da Labarin daku keson asanarwa da Duniya, ko Tambaya,Shawarwari,Hausa Novels, Nishadantarwa,Ilimantarwa,Ko Neman Sani akan ranakun dazamu cigaba dakawo muku Posting na Hausa Novels da Sauran su, zaku iya tuntubar ma'aikatan mu kuturo da Sunan Ku tareda Addreshin Ku tawannan Email din Officialdadinkowa24@gmail.com kyautane zamuyi muku komai don cigaban Al'ummar Hausa bama bukatar kudinka sai dai idan kaikayi niyyar Turowa don siyan Data Saboda acigaba dayin Posting a Kodayaushe batareda dakatawa ba, Website din Mu bashi da Alaka ta kusa ko tanesa da Wani/Wata Dan Siyasa/'Yar Siyasa afadin Duniya Burin mu shine musamu amincewar Al'umma aika da Gudunmawarka,Labari,Shawara da sauran su a Addreshin mu na email ✉💌📩 officialdadinkowa24@gmail.com

Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com

Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri

ALLAH yabar Zumunci Amin🙏

Source By ©Bashir M. Suleiman

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user

0 comments: