Saturday 18 November 2017

Siyasar Nigeria: A yayinda Kaduna ke shirin korar malamai-Dubi abinda Gwamnatin Bauchi ta shirya ma nata ma’aikatan

Tura Wannan Zuwa

A yayin da gwamnatin jihar Kaduna ta duƙufa
wajen rage yawan malamai a jiharta. Cen kuwa a
jihar Bauchi gwamnatin jihar ce duƙufa baiwa
ma’aikatanta horo kan aiyukansu na gwamnati a
faɗin jihar.

Inda ma’aikata sama da 2,000 suke
amsar horo na musamman kan shirin aiwatarwa
da saraffa kuɗaɗe ta hanyoyin sadarwar zamani
a cikin shirin gwamnatin na inganta aikin
gwamnati.

Horon dai an fara shi ne ranar jiya a Bauchi.

Majiyar Hausa Times ta ruwaito gwamnatin jihar
Bauchi ce da haɗin guiwar babban bankin duniya
suke gudanar da horon ma’aikatan da nufin
ɗaukaka darajar aikin gwamnati daga matakin
gargajiya zuwa matakin zamani na fasahar
sadarwa domin tabbatarwa da inganta aiki, yin
gaskiya a aiki, riƙon amana, da kuma kyakkyawan
shugabanci a yayin aiki.

Shugaban ma’aikata na jihar Bauchi Alhaji Liman
Bello ya bayyana cewar gwamnati mai ci ta
himmatu wajen baiwa ma’aikata horo kan
aiyukansu domin inganta aikin gwamnati da kuma
ɗaukaka darajar aikin a kowane mataki, gami da
tafiya da zamani a cikin harƙoƙin aiki.
Alhaji Liman Bello ya kuma bayyana cewar zasu
ci gaba da tsara horon a dukkanin faɗin jihar,
kuma ya ce za su yi abun ne rukuni-rukuni domin
kowane ma’aikaci ya samu horon da ya dace.

Hausa Times ta ruwaito tuni manyan sakatarori,
daraktoci da kuma shuwagabanin manyan
ma’aikatu suka samu wannan horo.
 
  

Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka dadinkowa24.blogspot.com

Ku hanzarta sanar da 'Yan Uwa da abokanan Arziki sunan Website din Mu me Albarka, don ganin sabbin posting din Mu se ku duba saman website din akwai "Home" sai ku shiga, mungode

Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com

Idan kana/kina da Labarin daku keson asanarwa da Duniya, ko Tambaya,Shawarwari,Hausa Novels, Nishadantarwa,Ilimantarwa,Ko Neman Sani akan ranakun dazamu cigaba dakawo muku Posting na Hausa Novels da Sauran su, zaku iya tuntubar ma'aikatan mu kuturo da Sunan Ku tareda Addreshin Ku tawannan Email din Officialdadinkowa24@gmail.com kyautane zamuyi muku komai don cigaban Al'ummar Hausa bama bukatar kudinka sai dai idan kaikayi niyyar Turowa don siyan Data Saboda acigaba dayin Posting a Kodayaushe batareda dakatawa ba, Website din Mu bashi da Alaka ta kusa ko tanesa da Wani/Wata Dan Siyasa/'Yar Siyasa afadin Duniya Burin mu shine musamu amincewar Al'umma aika da Gudunmawarka,Labari,Shawara da sauran su a Addreshin mu na email ✉💌📩 officialdadinkowa24@gmail.com

Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com

Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri

ALLAH yabar Zumunci Amin🙏

Source By ©Hausa Times

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user

0 comments: