Friday 1 December 2017

Labari da Tarihin Bilkisu Abdullahi: Sana'ar Film Tafi aikin Gwamnati samun Makudan Kudade-Sabuwar Jaruma Bilkisu Abdullahi

Tura Wannan Zuwa

Shahararriya kuma matashiyar ‘yar wasan
Hausan Kannywood, Bilkisu Abdullahi, tana daya
daga cikin jarumai mata da tauraruwarsu ke
haskawa a wannan lokacin, a cikin kwanakin nan
ta yi finafinai da dama wasu sun fito wasu suna
kan hanya.

Bilkisu tana daya daga cikin jarumai mata masu
kwazo da maida hankali musamman a ta fuskar
masana’antar da kuma ayyukanta. Tana da
kwarjini idan aka duba ta fuskar al’umma, cikin
kankanin lokaci ta samu karbuwa a idon duniya.

Bilkisu ta na iya bakin kokari ta ga ta birge masu
kallo. Akasarin masu kallon fim suna son su
ganin ta a ciki finafinai. Jarumar ta kware a gurin
rawa da iya magana.

Masoya na son ganin ta
hau kowace rara da darakta ka iya dora ta.

Al’umma suna yabon Bilkisu kwarai da gaske ta
wadannan fuskoki uku musamman gani rawar da
ta taka a finafinan ta na kwanan nan.

Bilkisu haifaffiyar garin Legas ce, a nan ta girma
a can kuma ta yi Makarantar Noziri da Firamare
dinta, daga bisani kuma ta dawo Kano da zama,
anan ne kuma ta yi karatun Sakandiri a Dinop
International School dake Hotoro, bayan ta
kammala karatunta, sai ta shiga harkan fim.

Ta bayyana a Abinda ya ja hankali ta ta fara
harkan fim a wata hirar da suka yi da wakilinmu
ta ce, “fim akwai abubuwa da dama, fim akwai
fadakarwa sosai a cikinsa, ni kaina akwai
FINAFINAN da na yi na ga abubuwa sosai wanda
ni ma na dau darusa a cikinsa”,

Ta kuma bayyana mana cewa ‘Kanina’ na daya
daga cikin finafinan da ita kanta ya birge ta,
koda aka tambaye ta dalili, sai tace, “Saboda irin
yanda labarin fim din yake, ya yi kyau, kuma
akwai darussa a ciki wanda al’umma za su karu
da su”.

Ta kuma ba ‘yan uwanta maza da mata na
masana’antar Kannyood shawarar da su rike
sana’ar fim da hannu biyu, inda take cewa, “Fim
dai sana’a ce mai kyau daidai gwargwadon da
zaka rufa ma kanka asiri, kuma sannan su yi
abinda ya kawo su, sannan su bi ta hanyar da
suka san ta alhairi ni, kuma za a taimaka masu
kuma mai shi yana da hanyar.”

Koda aka tambayeta wani irin kalubalen ta
fuskanta a rayuwarta, da fara harkan fim.

Ta ce
ita bata fuskanci matsaloli ba gaskiya, sadda ta
fara harkan fim, saboda da yardar mahaifanta ta
shiga industri, kafin Allah ya musu rasuwa, kuma
ko yanzu ba ta wani samun tsangwama daga
gurin ‘yan uwanta da masoyanta, suna zaman
lafiya har gobe.

Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka dadinkowa24.blogspot.com

Ku hanzarta sanar da 'Yan Uwa da abokanan Arziki sunan Website din Mu me Albarka, don ganin sabbin posting din Mu se ku duba saman website din akwai "Home" sai ku shiga, mungode

Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com

Idan kana/kina da Labarin daku keson asanarwa da Duniya, ko Tambaya,Shawarwari,Hausa Novels, Nishadantarwa,Ilimantarwa,Ko Neman Sani akan ranakun dazamu cigaba dakawo muku Posting na Hausa Novels da Sauran su, zaku iya tuntubar ma'aikatan mu kuturo da Sunan Ku tareda Addreshin Ku tawannan Email din Officialdadinkowa24@gmail.com kyautane zamuyi muku komai don cigaban Al'ummar Hausa bama bukatar kudinka sai dai idan kaikayi niyyar Turowa don siyan Data Saboda acigaba dayin Posting a Kodayaushe batareda dakatawa ba, Website din Mu bashi da Alaka ta kusa ko tanesa da Wani/Wata Dan Siyasa/'Yar Siyasa afadin Duniya Burin mu shine musamu amincewar Al'umma aika da Gudunmawarka,Labari,Shawara da sauran su a Addreshin mu na email ✉💌📩 officialdadinkowa24@gmail.com  hanya me sauki ko kuma daga kasan Website din akwai inda akasa

Name...
Email...
Message...

Sai Ku turo mana mun gode

Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com

Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri

ALLAH yabar Zumunci Amin

Source By ©Arewablog

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user

0 comments: