Thursday 30 November 2017

Sirrin 'Yan Matan Kannywoid: Akwai Rashin Gaskiya A Harkan Fina Finan Hausa – Fati Nijar Karanta Kaji

Tura Wannan Zuwa

Fitacciyar Mawakiyar Hausa Kuma Jaruma A
Masana’antar Shirya Fina Finan Hausa Na
Kannywood ‘Binta Labaran Wacce Ake Yiwa
Lakabi Da Fati Nijar
Tace Akwai Rashin Gaskiya A Harkan Fina Finan
Hausa, Jarumar Ta Fadi Haka Ne A Cikin Wata
Fira Da Tayi Da Wata Mujallar Film, Gadai Yadda.

Firar Tasu Ta Kasance Kamar Haka.
FIM: Hajiya Fati Nijar, kusan shekara biyu kenan
tun da ki ka tsunduma cikin harkar shirya fim da
fitowa a fim. A lokacin da ki ka fara, kin bugi
k’irjin cewar za ki shirya finafinai masu yawa a
kamfanin ki na Girma-Girma, to sai dai daga
lokacin zuwa yanzu fim d’aya ne ki ka fitar. Ko
dai kin karaya ne?

FATI NIJAR: To gaskiya ba karaya na yi ba,
kawai dai an d’an samu jinkiri ne ban k’ara fitar
da wani ba, shi ne ake ganin kamar na karaya.
Masu kallo su zuba ido, nan gaba kad’an za su
ga finafinai na da na shirya zan fito da su, kuma
akwai wad’anda na ke shirin yi nan gaba kad’an,
irin ‘Kasada’ da kuma ‘’Yar Maiganye’. Sannan
kuma akwai shirin da na ke yi na yin finafinai
masu dogon zango, irin wad’anda ake nunawa a
manyan gidajen talbijin a yanzu.

FIM: Rikid’ewar da ki ka yi daga mawak’iya zuwa
jaruma ta mayar da ke wata Fati Nijar ta daban.
Ko yaya ki ka ji da ki ka samu kan ki a haka?

FATI NIJAR: To ni dai gaskiya ban ji komai ba,
amma dai zan iya cewa na samu d’an canjin
yanayi saboda a matsayi na na mawak’iya kuma
na koma ina yin aktin duk da cewa akwai
bambanci sai dai ba wani yawa ba ne.

FIM: Bayan kasancewar ki jaruma, sai ya zama
ke ce mai shirya fim d’in. Yin hakan bai sa aiki
ya yi maki yawa ba?

FATI NIJAR: Ai ina ganin abin duk d’aya ne,
mawak’i ma zai iya zama furodusa kuma jarumi.
Wannan ne ma ya sa na ga ya kamata na rink’a
yin furodusin, ba wai na tsaya kawai a wak’a ba.

FIM: Ita harkar furodusin a masana’antar fim
yadda ta ke daban da yadda ake kallon ta. Ko
yaya ki ka samu kan ki a matsayin ki na
furodusa?

FATI NIJAR: A gaskiya akwai wannan. Ka san
yadda harkar mutane ta ke, ba za ka iya gane
halin mutum ba sai lokacin da harka ta had’a ku,
don akwai rashin gaskiya sosai a wajen mutanen
mu. Sai ka ga su na ta yi maka dad’in baki,
amma daga ka shiga hannun su, to sai dai Allah
Ya fitar da kai.

FIM: A fim d’in ki na farko, ‘Sakatariya’, kin nuna
jarumtar da masu kallo su ke ganin kin burge su.
Ko yaya ki ke kallon wannan nasarar da ki ka
samu a fim d’in?

FATI NIJAR: To haka ne, don wasu jama’a da
dama sun ji dad’in aktin d’in da na yi, har ma su
na cewa ai tun tuni ya kamata a ce na fara,
wasu kuma su na cewa ya kamata na tsaya a
wak’a ta. Ka san mutane kowa da yadda ya ke
kallon rayuwa, kuma da man shi fim d’in da na
fara yi na fara ne don na samu wata k’warewa a
harkar, kuma na yi koyi da sauran mawak’a na
duniya; domin idan ka kula da yawa fitattun
mawak’a na duniya za ka ga su na yin fim.

FIM: Kin tab’a fad’a mana cewar ki na so ki
zama jarumar da ta sha gaban duk wata jaruma
a harkar fim. Ko har yanzu ki na da wannan buri?

FATI NIJAR: In-sha Allahu kuwa! Burin ya na nan,
kuma da yardar Allah zan cika burin nawa.

FIM: Salon fim d’in ‘Sakatariya’ ya bambanta da
sauran finafinai ta sigar labari da kuma tsari. Me
ya sa ki ka d’auki wannan salon?

FATI NIJAR: Haka ne. Ka san duk finafinan mu
yawancin su labarin duk iri d’aya ne, kuma jigon
su soyayya. Duk da ba laifi ba ne a nuna soyayya
a fim, amma dai bai kamata ta rink’a zama ita ce
jigon labari ba. To ni gaskiya ina so na kawo
canji ne a masana’antar mu ta fim ta hanyar
kawo abubuwan da ba a yin su a ciki.

FIM: To da wak’a da fim wanne ya fi cin lokaci?

FATI NIJAR: A gaskiya wak’a ta fi cin lokaci,
saboda shi fim magana ce , kuma kafin ka fara
sai ka haddace, amma ita wak’a sai ka tsaya ka
yi tunani a k’wak’walwar ka. Sannan sai ka shafe
tsawon sa’o’i uku ka na cikin situdiyo. Amma shi
fim za ka iya yi a cikin minti talatin, idan an
gama sin d’in ka ka yi tafiyar ka.

FIM: Ganin jarumtar da ki ka nuna a ‘Sakatariya’,
an yi zaton za a rink’a ganin ki a sauran finafinai
na wasu kamfanoni, amma sai ba a ga hakan ba.
Ko dai kin tsaya ne a na kamfanin ki kawai?

FATI NIJAR: To ya danganta dai, don gaskiya ina
da k’arancin lokaci ne, amma dai ana kawo mini
aikin sai dai rashin lokaci, sai dai ina sa ran nan
gaba kad’an zan rink’a ware lokaci na yin fim
wanda zai zama ko wata shida ne a cikin
shekara, don ya zama na samu damar yin
finafinai har ma wad’anda ake gayyata ta.

FIM: A yanzu dai ki na nufin k’ofa a bud’e ta ke
ga duk wanda zai gayyaci Fati Nijar aiki matuk’ar
ya dace da ita?

FATI NIJAR: E, gaskiya haka ne. Duk wanda ya
ke ganin na dace da fim d’in sa, to ya na iya
zuwa ya same ni mu daidaita. Sai dai kuma
kamar yadda na fad’a maka, ina da k’arancin
lokaci, amma dai hakan ba zai hana ni na yi fim
ba.

FIM: Daga yadda ki ka kalli harkar fim bayan
shigar ki, ki na ganin nan gaba akwai nasara?

FATI NIJAR: E, gaskiya za a iya cin nasara,
amma dai sai an cire son zuciya, don gaskiya
harkar fim mu na da buk’atar gyara sosai, kuma
babbar matsalar da ta kashe harkar ita ce ba ma
karb’ar gyara a daidai lokacin da ya dace, sai
abu ya b’aci sannan za a zo ana yin kame-kame.

FIM: A yanzu harkar fim ta na cikin wani hali ta
fuskar kasuwa. Me ki ke ganin ya kawo hakan?

FATI NIJAR: Gaskiya yanayin finafinan mu ne. Da
kamar a ce mu na yin finafinai irin yadda ya dace
da rayuwar mu, to da ba za a samu kai a cikin
yanayin da ake ciki ba a yanzu.

FIM: Menene ya fi ba ki sha’awa game da harkar
fim?

FATI NIJAR: To ka san ita harkar fim akwai
nishad’i a cikin ta, kuma shi d’an’adam kullum ba
abin da ya ke so kamar ya samu kan sa cikin
nishad’i. Don haka na kan samu kai na cikin farin
ciki idan mu ka had’u a wajen lokeshin mu na
wasa da dariya.

FIM: A matsayin ki na jaruma, wace shawara za
ki ba abokan aikin ki?

FATI NIJAR: To gaskiya shawarar da zan bayar
ita ce su zamo masu gaskiya da kamun kai,
musamman ma mata, saboda wani lokacin idan
mace ta na kama kan ta sai a ce ta na da
girman kai, to ba girman kai ba ne. Don haka
mata ya kamata su gane matsayin su na ’ya’ya
mata; ba ko’ina za su rink’a zuwa su na yin abu
kai-tsaye ba.

Don haka mata mu tsare mutuncin
mu.

Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka dadinkowa24.blogspot.com

Ku hanzarta sanar da 'Yan Uwa da abokanan Arziki sunan Website din Mu me Albarka, don ganin sabbin posting din Mu se ku duba saman website din akwai "Home" sai ku shiga, mungode

Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com

Idan kana/kina da Labarin daku keson asanarwa da Duniya, ko Tambaya,Shawarwari,Hausa Novels, Nishadantarwa,Ilimantarwa,Ko Neman Sani akan ranakun dazamu cigaba dakawo muku Posting na Hausa Novels da Sauran su, zaku iya tuntubar ma'aikatan mu kuturo da Sunan Ku tareda Addreshin Ku tawannan Email din Officialdadinkowa24@gmail.com kyautane zamuyi muku komai don cigaban Al'ummar Hausa bama bukatar kudinka sai dai idan kaikayi niyyar Turowa don siyan Data Saboda acigaba dayin Posting a Kodayaushe batareda dakatawa ba, Website din Mu bashi da Alaka ta kusa ko tanesa da Wani/Wata Dan Siyasa/'Yar Siyasa afadin Duniya Burin mu shine musamu amincewar Al'umma aika da Gudunmawarka,Labari,Shawara da sauran su a Addreshin mu na email ✉💌📩 officialdadinkowa24@gmail.com

Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com

Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri

ALLAH yabar Zumunci Amin√√√

Source By ©kannymp3

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user

0 comments: