Thursday 30 November 2017

Tuna Baya: Me ka sani game da mutuwar Dr Ahmad Abubakar Mahmud Gummi Karanta Kaji

Tura Wannan Zuwa

Hakika Fitan rai yana da
wani irin radadi wanda
babu mai saninsa sai dai
Mamaci..

Mamaci yayin da ransa ya
kusan fita, Muryarsa takan
karye, Qarfin jikinsa yakan
tafi.. Babu damar Eehu ko
kururuwar zafin da yake ji.
Domin zafin mutuwa ya
riga ya ratsa dukkan
sassan jikinsa..

Ba zai samu damar neman
taimako ba, ballantana
adauke masa zafin radadin
da yake ji. Sai yayi fatan
wannan nishin da yakeyi ko
zai zama dalilun samun
rangwame, amma inaa!!.

Idan har akwai ragowar
wani Qarfi gareshi shine
za'a rika jin wani irin
gurnani yana fitowa daga
chan cikin Qirjinsa da
Makogoronsa yayin da rai
yazo fita.. Alhali launin
fuskarsa ya chanza saboda
tsananin halin da yake ciki.

Yayin da ranka yazo
Makogoro, awannan lokacin
zaka manta da
Makusantanka, iyalanka ko
'Ya'yanka, balle Makobta.

Awannan lokacin ne 'Dan
Adam yakan ji wata irin
Qishirwa mai tsanani
wacce sai ya gwammaci
inama ya bayar da dukkan
abinda ya mallaka domin a
bashi ruwan da zai kurba
koda kurbi guda ne!!.

A wannan lokacin duniya
da dukkan abin cikinta zasu
zamanto ba komai ba...

Ballantana dukiya ko Mulki
ko wani gata... 'Dan Adam
zai gane cewa ashe shi ba
komai bane.. Kuma tun
daga sannan zai fara
nadamar lokutan rayuwarsa
da suka tafi wajen sa'bon
Allah!!

Tunda Shugaban Halitta
(sallal Lahu alaihi wa aalihi
wa sallam) ya 'dan'dana
zafin mutuwa, Ka sani
cewa kaima sai ka
'dan'dana!!

Imamul Bukhariy ya ruwaito
daga Nana A'isha (rta)
tana bayar da labarin jinyar
da Manzon Allah (saww)
yayi adakinta, har zuwa
rasuwarsa. Tace :
"Hakika Manzon Allah
(sallal Lahu alaihi wa aalihi
wa sallam) ya kasance a
gabansa akwai wata guga
wacce akwai ruwa acikinta,
yana shigar da hannayensa
acikin ruwan sannan ya
shafe fuskarsa dasu.

Yana
cewa :
"LA ILAHA ILLAL LAAH!!
HAKIKA MUTUWA TANA
DA RADADI!".
Sannan ya chira hannunsa
sama yana cewa : "ACIKIN
TAWAGA MADAUKAKIYA!''.

(Alokacin an bashi za'bi ne
tsakanin ci gaba da zaman
duniya, ko kuma komawa
zuwa ga Ubangijinsa).
Yana fa'dar haka har sai
da aka karbi ransa sannan
hannunsa ya karkato...

Annabi Muhammadu kenan
(saww) Shugaban halittun
Allah baki daya, wanda bai
ta'ba sa'ba ma Allah ba.

ballantana kai wanda
kullum acikin sa'bon kake
kwana kake tashi.

Lokacin da Amru bn Al-As
(ra) yazo rasuwa, an
tambayeshi shin yaya yake
ji?. Sai yace "Ji nakeyi
tamkar sammai sun fa'do
akaina, Qassai kuma sun
matseni".

Sayyiduna Umar bn Al-
Khattab (ra) ya tambayi
Ka'abul Ahbari ya siffanta
masa yadda mutuwa take.
Sai yace :
"Ya Kai Sarkin Muminai!
Hakika ita mutuwa kamar
wani reshe mai yawan
Qayoyi ajikinsa, ashigar
dashi cikin cikin mutum.

Bayan kowacce Qaya ta
rike wata jijiya daga
jijiyoyin jikinsa, sai kuma a
samo wani mutum
Ma'abocin Qarfi, ya kama
wannan reshen ya fizgoshi
da Qarfi, ya fizgoshi kenan
tare da tsoka da jijiyoyin
jikin!!!.

Yanzu 'Yan uwa koda
tunanin wannan ranar bai
ishemu dalilin rage sa'bon
Allah ba!!.

Wannan ranar fa sai ta
riskeni, sai ta riskeka, sai
ta riskeki, sai ta riskemu
baki dayanmu kamar dai
yadda ta riski wadanda
suka rayu kafinmu.

Daga cikin abubuwan dake
haddasa tsananin zafin
fitan rai tare da gigicewa
akwai :

- Wulakantar da Sallah
.
- Wulakanta Mahaifa.

- Chutar da Manzon Allah
(saww) ko iyalan gidansa
da zuriyarsa ko kuma
Sahabbansa (Radhiyallahu
anhum).

- Cin Mutuncin Malamai
Waliyyai da salihan bayin
Allah.

- Shan giya ko Miyagun
Kwayoyi.

- Cin haram (Cin hanci,
wawure kudin gwamnati ko
Kudin Marayu, ko Satar
dukiyar jama'a, etc).

- Kisan rai ba tare da hakki
ba.

- Zina, Luwadi, Madigo.

Ya Allah ka kiyayemu daga
Mummunar mutuwa.
Ameen.

Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka dadinkowa24.blogspot.com

Ku hanzarta sanar da 'Yan Uwa da abokanan Arziki sunan Website din Mu me Albarka, don ganin sabbin posting din Mu se ku duba saman website din akwai "Home" sai ku shiga, mungode

Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com

Idan kana/kina da Labarin daku keson asanarwa da Duniya, ko Tambaya,Shawarwari,Hausa Novels, Nishadantarwa,Ilimantarwa,Ko Neman Sani akan ranakun dazamu cigaba dakawo muku Posting na Hausa Novels da Sauran su, zaku iya tuntubar ma'aikatan mu kuturo da Sunan Ku tareda Addreshin Ku tawannan Email din Officialdadinkowa24@gmail.com kyautane zamuyi muku komai don cigaban Al'ummar Hausa bama bukatar kudinka sai dai idan kaikayi niyyar Turowa don siyan Data Saboda acigaba dayin Posting a Kodayaushe batareda dakatawa ba, Website din Mu bashi da Alaka ta kusa ko tanesa da Wani/Wata Dan Siyasa/'Yar Siyasa afadin Duniya Burin mu shine musamu amincewar Al'umma aika da Gudunmawarka,Labari,Shawara da sauran su a Addreshin mu na email ✉💌📩 officialdadinkowa24@gmail.com

Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com

Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri

ALLAH yabar Zumunci Amin√√√

Source By ©24wikis.com

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user

0 comments: