Monday 4 December 2017

Kannywood: Adam A. Zango zai shirya Film din da ba'atabayin irin saba-Karanta Kaji

Tura Wannan Zuwa Ga

Shahararren jarumin wasan Hausa, Adam A
Zango, ya sanar da fara gabatar da wani shiri
mai taken KARSHEN ZANCE a wannan watan da
muke ciki.

Zango ya bayyana hakan ta kafar sada zumuntar
Facebook a yau Lahadi.

Sanarwar ta ce za a fara
gabatar da shirin ne 18 ga wata.

Kamfanin RITETIME MULTIMEDIA LIMITED ne
suka dauki nauyin shirin, sannan Sheikh Isa Jalo
ne Darektan shirin, Nasir Gwangwazo ya rubuta,
Hanan kuma ta tsara shi.

Tauraruwar Jarumi Zango na cigaba da haskawa
a kamfanin shirya fina-finai na Kannywood duk da
kasancewar yanzu baya shirya fina-finai a jihar
Kano tun bayan samun sabani da shugaban
hukumar tace fina-finai a jihar, Babannan Rabo
Muhammad, shekaru da dama da suka wuce.

Tuni jarumin ya dawo jihar sa ta haihuwa,
Kaduna, inda ya cigaba da sana'ar sa ta
shiryawa da fitowa cikin wasan kwaikwayon
Hausa.

Source: ©Hausamini

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user

0 comments: