Monday 4 December 2017

Labari: Barin APC shine babban kuskure Da Kwankwaso zai yi a Rayuwarsa – Tsohon Mai hadimin sa

Tura Wannan Zuwa Ga

Alhaji Ahmed Shuaib Gara-Gombe wanda ya
kasance tsowon mai ba da shawara ga Sanata
Rabiu Musa Kwankwaso ya fada masa cewa
karda ya bar jam’iyya mai mulki wato All
Progressives Congress (APC).

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku
Abubakar yayi murabus daga APC sannan ya
sanar da komawarsa jam’iyyar adawa ta
Peoples Democratic Party (PDP) a ranar Lahadi,
ga watan Nuwamba sannan Gara-Gombe ya
shawarci tsohon gwamnan jihar Kano da karda
ya bar APC zuwa PDP.

Ya ce farin jinin da Kwankwaso ya samu a zaben
2015 wanda ya kai shi ga zama daya daga cikin
shugabannin APC ba lallai bane hakan ya
kasance idan ya bar APC zuwa PDP.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user

0 comments: