Tuesday 12 December 2017

Karanta Wannan: 'Yan Nigeria ba Zasu kuma sake Zabar APC Ba Don Haka PDP ce Zata Lashe Zaben 2019-Atiku Abubakar

Tura Wannan Zuwa

Tsohon mataimakin Shugaban kasa Atiku
Abubakar ya bayyana cewar hadin kai tsakanin
‘ya ‘yan jam’iyyar PDP ne zai sa jama’a su sake
amincewa da jam’iyyar.

Atikun ya bayyana hakan
ne a jawabin da ya gabatar a babban taron
jam’iyyar da akayi domin zaben sabbin
Shugabannin da zasu ja ragamar jam’iyyar ta
PDP.

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito fasarar cikakken
jawabin na Atiku Abubakar kamar haka:

Duk tsawoncin rayuwa ta, ni mutum ne da yayi
Imani da Kasarmu Nijeriya. Nayi Imani da cewa
Nijeriya zata iya zama kasa daya mai baiwa
kowane dan kasa ko yar kasa damar yin fice ga
al’amarinsa ba tare da banbanci ba.

Nayi Imani da cewar Najeriya tana iya zama kasa
daya mai kudurin alheri ga dukkan dan kasa.

Wannan Imani da nike dashine ya bani kwarin
guiwar hada hannu da sauran ‘yan-uwana ‘yan
Nijeriya masu irin wannan ra’ayi domin mu kafa
Jam’iyyar Mutanen Damokradiyya (watau PDP)
wadda mukayi wa ginshiki na hadin kan kasa,
kuma muka gina ta a kan tafarkin zumunci,
gaskiya, da kuma adalci ga ko wane dan kasa ba
tare da bambanci ba.

Jamiyar PDP da muka gina, ta kafu ne a kan
tafarkin damokradiya, kuma ta aminta da bin tsari
irin na damokradiyaa cikin duk tsare-tsaren
tafiyar da al’amurran yau da kullum na Jam’iyyar.

Wannan manhaja itace kawai zata iya shimfida
mulki na gaskiya da adalci a kasarmu Najeriya.
Yin haka din shine tubalin ginin sahihiyar kasa
mai haddin kai wadda dukkan ‘ya’yanta zasuyi
alfahari da ita.

Wannan ya zama dole ne domin sai da hadin kai
ne kawai zamu iya shinfida ginshikin tattalin
arziki wanda zai haifar da ayyuka ya kuma ba
kowane dan kasa damar yin fice a kowane
zarafin rayuwa.

Tunda aka kafa Jam’iyyar nan ta PDP, shekaru
goma sha tara (19) da suka wuce, imanina na
nan daram dam akan wadannan ginshikoki da
muka kafa wannan Jam’iyyar akansu, duk kuwa
da yake akwai wadansumu da dama da suka
rikide suka kuma chanza matsayinsu.

A cikin wadannan shekarun:
Nayi yaki da rabe-raben kawunan ‘yan
jam’iyarmu.

Nayi yakin kare Tsarin Mulkin
Jam’iyarmu da kuma tsarin Mulkin Kasarmu,
Najeriya, wanda har ma yin haka din ya ja akayi
amfanin da karfin mulki aka fiddani daga cikin
Jam’iyyar da na taimaka aka kirkiro.

Wannan
kuwa bai bani mamakiba domin na daukeshi
tamkar sakamako ne da mutum ka iya samu
domin fafutukar dawwamar mulkin damokradiya a
kasarmu.

Imani na akan tubalin da muka gina
ginshikinJam’iyar PDP a kanshi baitaba girgizaba,
a duk halin da na samu kaina.

A yau dinnan ina
nan zaune daram bisa kan wadannan ginshikokin,
kamar yadda na zauna a kansu ranar 17 ga
watan Agusta, 1988, lokacin da Marigayi Alex
Ekwume, da Marigayi Solomom Lar, da Marigayi
Abubakar Rimi da sauran manya manyan yan
kishin kasa da suka hadu suka sanar wa duniya
da haihuwar Jam’iyar PDP.

A yau dinnan, ina alfaharin shaida maku cewar
na dawo gida. Na dawo Jam’iyarmu.

Ina chike da farin ciki da kuma alfaharin cewar
Jam’iyar nan tamu ta PDP itace ta samu nasarar
kwace mulki daga hannu sojoji a shekarar 1999
Ina kuma cike da farin ciki da alfahari cewar
Jam’iyar mu ta PDP itace daya tilo wadda ta
kawo damar da zababben shugaban kasa ya kare
mulkinsa ya kuma mika jagorancin kasar zuwa ga
wani sabon zababben shugaban kasa a cikin
shekarar 2007.

Ina alfahari da cewar a cikin shekarar 2015,
wannan Jam’iyyar ta PDP ta jagoranci zaben da
ya mika mulki zuwa ga dan takarar shugaban
kasa daga Jam’iyyar adawa lami lafiya.

Ina kuma matukar alfahari da cewa gwamnatin
Jam’iyar PDP ta kawo ci gaban tattalin arzikin
kasar da ba’a taba samun irinsa ba a tarihin
Najeriya.

Amma kash! A cikin shekarar 2015, Jam’iyyar
PDP bata da hadin kai, ta wargaje. A saboda
hakane kuma, mutanen Najeriya suka juya mata
baya suka zabi chanji.

Anyi wa ‘yan Najeriya alkawarin yalwatar arziki,
da zaman lafiya da kuma mulkin gaskiya ba boye-
boyen komai.

Ashe abin duk yaudara ce.

Jam’iyyar APC ta yi alkawarin kirkiro ayyuka
milyan ukku a kowace shekara. Amma sai gata
tana rusa ayyuka milyan ukku a kowace shekara.

Jam’iyyar APC tayi mana alkawarin zaman lafiya
da kuma hadin kan yan kasa baki daya. Amma
sai gashi kasarmu, a yau, ta samu rarrabuwa da
kuma rashin kishi da hadin kan junan da bata
taba samu ba tun lokacin da aka gama yakin
basasa a Najeriya.

Jam’iyyar APC tayi alkawarin sake shirin jihohin
Najeriya domin qyara yanayin zaman
Jamhuriyarmu. Amma da ta dare bisakan gadon
mulki, sai ta juya wa shirin baya, tayi watsi da
shi.

Jam’iyyar APC tayi alkawarin yaki da cin hanci
da rashawa. Amman babu yakin da suka sa a
gabansu yanzu banda fataucin yan adawa. “Suna
ba albasa ruwa amma kuma suna tuge tumatari.”

A Najeriyar mu a yau, idan kai dan jam’iyar
adawa ne, kuma aka tsinkayi cewar zaka iya
razana jam’iyar gwamnati, sai a fara kama
yaranka da abokan huddarka a daure, a kuma
fara muzguna ma Kampanonin kasuwancinka.

Duk da manyan kurakuaran da gwamnatinmu ta
PDP ta yi lokacin da ta ke kam mulki, yau
mutanen kasarmu na juyayin wucewar
gwanmatin. Sukan ce “jiya ba yau ba ………”

Kuma suna fadan haka din da kyakkyawar hujja:

domin lokacin da Jam’iyar PDP ta karbi mulkin
Nigeria a shekarar 1999:

Yawa-yawan yan Najeriya basa wuce shekara 44
a duniya sai su mutu.

A duk fadin Najeriya ba za’a iya alfahari da
wayoyin tarho na hannu da suka kai milyan daya
ba.

Tattalin Arzikin kasarmu shine na ukku mafi karfi
a nahiyar Africa.

Bayan shekaru goma sha shidda (16) da jam’iyar
PDP ta shugabanci gwamnatin kasarmu, da ta
sauka daga karagar mulki a cikin shekarar 2015,
ta bar Najeriaya a cikin wani sabon yanayi kamar
haka:

Ta kara shekaru goma (10) akan adadin yawan
shekarun da mafi yawan yan Najeriya sukeyi a
duniya kafin su mutum. Watau yanzu shekarun
sun zama hamsin da hudu (54)
Ta baiwa ‘yan Najeriya milyan chasain da tara
(99 million) damar amfani da wayar salula.

Ta bunkasa tattalin arzikin Najeriya har ya zama
na daya a cikin Africa, ya wuce na Masar (Egypt)
da kuma Africa ta Kudu (South Africa).

Ni kanyi matukar mamaki da juyayi a duk lokacin
da naji ana maganar cewar tabarbarewar farashin
man petur shine dalilin da yasa gwamnatinmu
take gazawa.

A yau din nan, farashin gangar Man Petur bai
taba sauka kasa da dala Amirka hamsin ($50)
ba.

Amma zamanin da na zama mataimakin
shugaban kasar Najeriya, farashin gangar man
petur bai wuce dala amirka ashirin ($20) ba.

Na taka rawar gani wajen samowa da kuma
daukar hazikan yan kasa masu ilimin tattalin
arziki wadanda suka taimaka ainun wajen
habbaka tattalin arzikin kasarmu da kashi kamar
shidda cikin dari (6%) a kowace shekara.

Babban abin burgewa ma a nan shine, sai gashi
mun yi amfani da dan kudaden da muke samu
mun biya duk basukan da ake bin kasarmu daga
kasashen waje.

Wannan shine ya gwada mana cewar yadda kasa
tayi amfani da arzikin ta ya fi muhimmanci fiye
da adadin ma’adinan da take da su.

A matsayinmu na ‘ya’yan jam’iyar PDP muna da
abubuwan yin alfahari da yawa. A cikin shekarun
nan goma sha shidda (16) da mukayi muna mulki
a najeriya, mun sami zaman lafiya da habakar
arzikin kasa mai tarin yawa.

Babu shakka munyi wasu kurakurai, amma
bamuyi watsi da hadin kan kasa ba.
Bamu maida jihohin da suka zabemu ba ‘ya’yan
bora muka kuma maida jihohin da basu zabe mu
ba ‘ya’yan mowa.

Amma kash! Sai gashi yanzu muna karkashin
mulki Jam’iyar APC wadda ta share fiye da
shekaru biyu kan mulki amma har yanzu tana
kuka da gwamnatin da ta gada a kan
tabarbarewar al’amurran ta, tana kuka da jama’a
maimakon share masu hawaye, domin share
masu hawayen nan shine musabbabin da yasa
aka zabesu.

Jam’iyar PDP itace zata kyautata tsarin shirin
Jamhuriyar Najeriya, ta inganta ma’aikatunta, ta
kuma mika mulki zuwa ga hannun talakawa.

Kuma zata yi hakan ne ta hanyar:
Karfafa Masana-antu da hada-hadar kasuwanci
wanda zai kirkiro ayyukan yi irin wadanda
gwamnati bazata iya yi ba;

Za ta kafa tsarin tattalin arzikin kasa na ‘yan
“Jari-Hujja” wanda zai karfafa wa jama’a gyuiwar
saka jari domin kirkiro ayyukan yi a kasa.

Zata gyara yanayin Gwamnati domin ta zamo
ingantacciya mai kuzari da kuma sanin ya
kamata.

Gwamnatin PDP ba zata yarda ta dauki
kaso mafi tsoka na kasafin kudi domin biyan
albashin ma’aikatan gwamnatin da ba su shige
kashi daya cikin dari (1%)na jama’ar kasar ba.

Duk da matsalolin da Jam’iyar PDP take ciki a
halin yanzu, itace jamiyar da tafi bazuwa a
kowane bangare da sashe na Najeriya. Dole ne
mu sake salon tafiya domin ‘yan Najeriya su
aminta da mu su sake maidamu a bisa karagar
mulki. Idan har Allah ya sake bamu mulki, to dole
ne muyi aiki tukuru domin daukaka martabar
kasarmu najeriya da kuma dawwamar da mulki
demokradiya a cikin ta.

Ba zamu iya yin haka ba sai idan munyi aiki da
kuduri guda cikin hadin kai. Ainihin hadin kanmu
shine babban tubalin ginin mafificiyar kasa mai
adalci ga jamaarta.

Dole ne mu manta da yin
mummunan zargi ga junanmu, kuma mu zage
damtse domin baiwa duk dan najeriay damar
shahara akan aikinsa ba tare da la’akari da
jinsinsa ba ko kuma addininsa.

Dole mu kasance Jam’iyar da take kawo
kyakkyawan tsarukan da zasu baiwa duk yan
kasarmu kwazo da karfin gyuiwar dogaro da
kuma alfahari da kasarsu Najeriya, ba wai kawai
su so su labe wajen kauyukansu ba ko kuma
cikin kabilun su kawai ba. Ko kuma ma sufi
shaawar barin kasar dun-gurun-gun.

Hakkinmu ne da kai da kuma ni mu tabbatar
cewarmun zamanto Jam’iyar da zata kawo
waraka a cikin kasarmu ba Baraka ba. Zamu
tabbatar cewa ba za’a sake rarraba kawunanmu
ba har abada.

Saboda haka, a wannan dandalin babban taron
Jam’iyar nan tamu, dole ne mu tabbatar da cewa
mun zabi shugabannin Jam’iya masu basira da
kwakwalwa, wadanda suke da hangen nesa kuma
suna da kudurin daukaka kasarsu fiye da misali.

Shugabannin da suka fahimci bukatar aiki cikin
gaggawa domin ci gaban kasarmu Najeriya.

Ya kamata ku zabi shugabannin da suka
gwanance wajen ginin Jam’iya domin su taimaki
PDP ta zama amintacciyar Jam’iya wadda ta
bambanta da Jam’iyar “Kama-Karya” ta APC.

Mu zabi shugabannin da basu da wata yana a
cikin idanunsu wadda zata hana su ganin cewar
zamanin nan namu ya canza kuma guguwar
chanjin nan bazata bar duk wadanda ba zai
fahimci sabuwar alkiblar ba.

Misali, muna bukatar
shugabannin da suka fahimci cewar kasuwar
man petur a cikin duniyar makamashi ta na
dushewa kuma dushewarnan zata saka kasarmu
cikin mummunar damuwa idan ba mu chanza ba
cikin sauri.

Wallahi muna bukatar shugabannin da suka
fahimci hikimar gyaran shirin zamantakewa da
kuma tsarin tattalin arzikin kasarmu ta yadda
za’a bar gwamnatocin jihohi su taka gagarumar
rawa cikin ayyukan ci gaban kasa, wadanda
kuma zasu iya janye ragamar tattalin arzikin
kasarmu daga man petur, su kuma hana korafe-
korafen wariyar al-umma da takura wa kananan
kabilu.

Wadannan sune shugabannin da zasu
karfafa zamantakewarmu su kuma gina kasarmu
da kyau.

Source: ©Hausa Times

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user

0 comments: