Tuesday 12 December 2017

Labari: Ta Kashe Mijinta yana yin Sallah har Lahira-Karanta Kaji

Tura Wannan Zuwa

Fostar fim din, ta nuna wata mata da jajayen
kaya ta caka wa wani saurayi wuka lokacin
yayi sujjada a sallah.

Wasu na ganin yin fim din bai dace ba
musamman ganin yadda batun ke gaban kotu.

Wasu kuma na ganin ma tunda wani ya rasu,
bai kamata wasu su ci kudi da hakan ta hanyar
fim ba.

Fim din ta kashe shi, fim ne da Jamilu Ahmad
Yakasai ya shirya, kuma har sun fara sayar
dashi a kasuwa.

A labarin dai, kamar yadda aka ji a gaske,wata
mata ce tsananin kishi ya sanya ta kashe
mijinta yana cikin sallah, saboda zai karo mata
kishiya.

Masu hada fim din na fata ne su fadakar da
jama'a kan mugun kishi da abin da zai
tarwatsa ma mutum rayuwa.

A waje daya kuma, wasu na gani tunda batun
yana kotu, bai kamata ayi fim din ba, ko ma
kuma cewa wani ya rasa ransa a gaske, bai
kamata ayi ffim a ci riba dashi ba.

Ku cigaba da Kasancewa da Shafin Dadinkowa24 aduk inda kuke a fadin Duniya

Source: ©Arewatop

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user

0 comments: