Monday 4 December 2017

Labari: Abunda ya hadani da matata ta caka mini kwalba a kirji ta nemi kasheni

Tura Wannan Zuwa Ga

A kwanakin baya Hausa Times ta kawo maku
rahoton yadda wata mata a jihar Zamfara ta
sokawa mijinta mai suna Bilyaminu kwalba a kirji
bayan ta buga masa a kansa. Wanda dakyar aka
iya ceto rayuwarsa.

Jaridar Dimokardiyya ta
tattauna da mijin matar kuma ya bayyana abunda
ya faru tsakaninsu har takai ga abunda matar
tasa tayi mashi.

Malam Biliyaminu yace “Wata rana na dawo daga
aiki da daddare sai aka kira Matata a waya, tun
kafin ta ajiye wayar ta fara salati, sai na
tambaye ta abunda ya faru sai take gaya mun
cewar Yayan ta ne aka kama yanzu haka ya
kwashe yan kwanaki a kulle dajin haka sai nace
mata to da safe sai mu je police station din
mugani.

Bilyaminu cikin jini bayan matarsa ta caka masa
kwalba
Da gari ya waye muka tafi Police station da
muka isa sai aka sheda mana cewar wannan
Yayan nata an kulle shi ne saboda an kama shi
yana saka ma wata Yarinya yar kimanin shekaru
4 hannu a gaban ta yana yi mata kwakule karshe
ma dai gobe ma za’a kai shi Kotu.

Dana ji haka sai ta bukaci a bamu Belin shi sai
Yan Sandan suka ce magana ce ta kudi saboda
haka idan muna so a bayar da Belin shi sai mun
bayar da nera 15000, bayan mun dawo gida
washe gari da safe na shirya naje wajen aiki ko
rance in samo nayi kokari in sami kudin wajen
abokan aiki na” abun ka da leburori ban samu
kudaden ba, dana koma sai nace mata ban sami
wadannan kudaden ba amma ko cikin yayayyakin
ki idan akwai wadanda zata jinginar taje ta bayar
saboda ni ban San inda zanje in kai Jinginan
kayayyakin ba.

Ina kwance sai ta matsa mun lallai sai mun tashi
mun tafi data matsa mun sai nace mata baza ni
ba idan zata je ita ta tafi, sai tace in bata wayata
zata yi kira sai nace mata bazan bayar ba sai ta
sanya hannu ta dauka ta fara waya sai nace
mata babu Kati a waya ta sai na saka hannu na
karbe waya ta na koma na kwanta, sai ta fara
surutai tana cewa dan ba Dan’uwana bane nace
mata kiyi hakuri har in sami kudi, jiya dani dake
muka wuni can yau ma tunda ba kudi haka zaki
kara zuwa kuma ke mace ce.

Sai ta koma da baya banyi aune ba kawai sai naji
ta buga mun Kwalbar Fanta a kai kwalbar ta
fashe a kai na sa’anan kuma ta Chaka mun
Kwalbar a kirji na Kwalbar ta shige ni sosai Dan
dena gani nayi.

Lokacin da abun ya faru guduwa tayi sai dana yi
kusan sati daya a Asibiti ba’a kamata ba sai da
aka kama Kakarta da kawun ta da wanda ya bani
Auren ta kafin ta fito aka kama ta, yanzu haka
tana hannun Yan sanda a Tudun/wada Division.”

Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka dadinkowa24.blogspot.com

Ku hanzarta sanar da 'Yan Uwa da abokanan Arziki sunan Website din Mu me Albarka, don ganin sabbin posting din Mu sai ku duba cikin  website din akwai "Home" sai ku shiga, mungode

Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com

Idan kana/kina da Labarin daku keson asanarwa da Duniya, ko Tambaya,Shawarwari,Hausa Novels, Nishadantarwa,Ilimantarwa,Ko Neman Sani akan ranakun dazamu cigaba dakawo muku Posting na Hausa Novels da Sauran su, zaku iya tuntubar ma'aikatan mu kuturo da Sunan Ku tareda Addreshin Ku tawannan Email din Officialdadinkowa24@gmail.com kyautane zamuyi muku komai don cigaban Al'ummar Hausa bama bukatar kudinka sai dai idan kaikayi niyyar Turowa don siyan Data Saboda acigaba dayin Posting a Kodayaushe batareda dakatawa ba, Website din Mu bashi da Alaka ta kusa ko tanesa da Wani/Wata Dan Siyasa/'Yar Siyasa afadin Duniya Burin mu shine musamu amincewar Al'umma aika da Gudunmawarka,Labari,Shawara da sauran su a Addreshin mu na email ✉💌📩 officialdadinkowa24@gmail.com  hanya me sauki ko kuma daga kasan Website din akwai inda akasa

Name...
Email...
Message...

Sai Ku turo mana mun gode

Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com

Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri

ALLAH yabar Zumunci Amin

Source By ©Hausa Times

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user

0 comments: