Tuesday 12 December 2017

Siyasar Nigeria: Ina matukar mamakin yadda wai PDP ke son dawowa mulkin Najeriya –Muhammadu Buhari

Tura Wannan Zuwa Ga

Rahoton DailyNigerian Hausa

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya bayyana
cewar, yana matukar mamakin yadda wai PDP
take son dawowa kan karagar Mulki a Najeriya,
bayan duk irin muguwar barnar da ta aikatawa
kasarnan wai har wani shirye shirye suke yi na
sake dawowa kan karagar mulki a babban zaben
2019 da ke tafe.

Shugaba Buhari yana magana ne, a taron
kungiyoyin al’umma da aka gudanar a gidan
Gwamnatin Kano, a bukukuwan da ake yi na
ziyararsa a birnin Kano ta yini biyu, wadda ta
kare a ranar Alhamis.

Shugaba Buhari yace ‘yan
Najeriya ba zasu taba mancewa da mulkin
shekaru 16 na jam’iyyar PDP ba.

Kamar yadda ya fada, cin hanci da rashawa bai
sake samun gindin zama ba, sai a zamanin
mulkin PDP a Najeriya. PDP sai da ta kusan
tsiyata Najeriya, kuma ita ke da alhakin dukkan
wannan balahira da batarnaka da ake yi ta cin
hanci da rashawa a Najeriya. Dan haka babu
abinda PDP ta yi illa muguwar barna a Najeriya.

Ya cigaba da cewar, tsarin Gwamnatin APC shi
ne samar da canji, ta hanyar yakar fitinar Boko
Haram, da yakarcin hanci da rashawa, da kuma
samar da tsarin da tattalin arzikin Najeriya zai
dawo cikin hayyacinsa.

Dan haka wannan
Gwamnatin ta APC tana samun nasarori sosai
akan abinda suka sanya a gaba, inji Buhari.

Shugaba Buhari ya kara da cewar,” Amma yaki
da cin hanci shi ne abinda yafi ci mana tuwo a
kwarya.

Dan haka tilas ne ‘yan Najeriya su
fahimci bambancin tsarin Gwamnatin soja da
kuma Gwamnatin Demokaradiyya. Tun zamanin
da nayi Mulki cin hanci da rashawa yake yunkurin
kashe kasarnan, ni kaina sai da na kare a gidin
kaso a sakamakon yakin da na kuduri aniya da
cin hanci.”

“A lokacin da nake shugaban kasa a mulkin soja,
na kama kuma na tsare ‘yan siyasa da yawa,
sabida a lokacin ina da kuruciya, amma
mutumbiyu daga cikin wadan da muka kama,
muka ga ashe su ba masu laifi bane, marigayi
Bilyaminu Usman da kuma Malam Adamu
Chiroma, su kadai ne bamu samu da laifi ba, a
cikin mutanen da muka kakkama a wancan
lokacin.”

“A wannan kasar ne fa muka samu wani babban
alkali, makare da kudaden kasashen waje a
gidansa, na miliyoyin kudi, da fasfo na
musamman har kala hudu.

Irin wadannan
mutanen fa sune suke daure mutane shekaru 20
sabida sunci hanci ko sun karbi rashawa, amma
sai gashi mai dokar barci ya bige da gyangyadi.”
Inji Buhari.

Haka kuma, Shugaba Buhari ya tunawa mutane
cewar,daga shekarar 1999 har zuwa 2014
Najeriya na fitar da gangar danyan mai Miliyan
biyu da digo daya (2.1m) a kusan farashin da bai
gaza dalar amurka 100 ba, yace wadannan
makudan kudade duk sunyi batan dabo a
karkashin mulkin PDP.

“Abin takaici, lokacin da muka karbi mulki
farashin gangar danyan mai ya karye, inda ake
sayar da kowace ganga akan dalar amurka 28,
sai daga bisani ne ta daga zuwa 37 har ta kai
40.

A dan haka naje Babban bankin kasa CBN
domin a lokacin kowa yasan nawa ne Najeriya
take samu daga danyan man da take
kasuwancinsa, na tambayi nawa muke da shi a
ajiye, aka shaida min cewar, babu komai, sai ma
ciko da ya biyo gyartai.”

“Ban iya gamsuwa da bayanin ba, sabida ina
tunanin kamar ba gaskiya bane.

Aka ce min wai
anyi amfani da kudaden wajen shigo da mai da
kayan abinci, bayan kuma nasan a yankunan
kudu maso yamma, da maso gabas da maso
kudu, da kuma Arewa maso yamma da maso
gabas da Arewa ta tsakiya duk muna iya samar
da abincin da zamu ci, nace ba zai yuwu ba mu
dinga siyan abincin kasar waje, wannan rayuwar
karya ce.”

“A lokacin da muka bincika yadda ake shigo da
tattacen mai, abin takaici, mun samu kazamar
cuwa cuwa tsakanin masu shigo da man da kuma
masu kasuwancinsa a gida Najeriya tare kuma da
hadin bakin babban bankin kasa CBN.

Sam ko a
jikinsu basu damu da halin da ‘yan Najeriya zasu
fada ba ta sanadiyar ci da guminsu da suke yi.”

Tare da irin wannan mugun alkaba’in da aka yi a
Najeriya karkashin Gwamnatin PDP ta tsawon
shekaru 16, wai suna shirye shiryen dawowa kan
karagar mulki, ni kam ina cike da mamaki a
gaskiya. Inji shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Haka kuma, yayi godiya ga al’ummar jihar Kano
akan irin goyon baya da suke bashi, da kuma
karrama shi da aka yi a yayin wannan ziyara da
ya kawo, naga har da kananan yara sun fito
sosai kawai dan su yi ido biyu da ni gaskiya ban
yi tsammanin haka ba, “Na gode kwarai da gaske
mutanen Kano” Inji Shugaba Buhari.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user

0 comments: