Monday 8 January 2018

Hotuna Da Cikakken Tarihin Rahama Sadau: Abubuwan Da Yakamata Kusani Dangane Da Rayuwar Jaruma Rahama Sadau

Tura Wannan Zuwa Ga
Rahama Sadau wata fitacciyar Jaruma ce a kasar Najeriya wadda tayi fice wajen fannin wasan kwaikwayo na masana’antar Kannywood.


An haifi rahama Sadau a ranar 7 ga watan Disamba na shekara ta alif dari tara da casa’in da uku (7 December 1993) a unguwar Sarki dake cikin garin

Kasancewa Jaruma Jaruma Rahama Sadau wacce take rike da kambu na karatun Kasuwanci daga Foliteknic ta Kaduna ta samu shiga masana’antar Kannywood a shekarar 2013.

Rahama Sadau ta kasance daya tilo wajen tafka mahawara a cikin yaren Hausa, Turanci da Indiyanci baki daya. Jaruma Rahama Sadau ta samu fice bayan fitowar ta a wani shiri mai suna “Gani Ga Wane” tare da Jarumi Ali Nuhu.


Lambar Yabo da ta Girma

Jaruma Sadau ta samu lambonin girma da yabo daban daban a kasar Najeriya dama kasashen ketare da dama wanda ya hada da Jaruma ta musamman a shekara ta 2014 da kuma 2015 wadda ta samu daga City People Entertainment Awards.

Bugu da kari ta samu award din African Film Awards a shekara ta 2015 wanda African Voice ta hada.


Aikin Gidauniyar Rahama Sadau mai suna Ray of Hope a turance tayi fice wajen shiga shirye shirye na masu ciwon daji mai suna Cancer da turanci wanda Medicaid sukan shirya a lokaci lokaci. Sannan a wani lokaci a baya ta samu ziyartar gidan ‘yan gudun hijira dake garin Wasa a babban birnin Abuja a Najeriya.


Kora Daga Masana’anta

Duk da dai cewar Jaruma Rahama Sadau ta samu fice a ita masana’antar ta Kannywood, sai dai kuma a ranar 2 ga watan Oktoba na wannan shekata ta dubu biyu da sha shida (2 October 2016) kungiyar MOPPAN ta samu dakatar da Jarumar kasancewar samunta da laifin rungumar wani mawaqi a wani faifan bidiyo mai suna ClassiQ wanda ya fito daga yankin Jos na jihar Filato a Najeriya.

Ita dai wannan dakatarwa bata samu cirewa ba har a yanzu inda wadansu kan kalle ta a matsayin kora gaba daya daga cikin masana’antar.

Kungiyar MOPPAN tayi tsokaci da cewar rungumar da Jarumar tayi ya saba tarbiya da tsari irin na duk wani mai yin shirin fim na Hausa. Sai dai korar Jaruma Rahama Sadau bai hana fina finai masu hoton ta fita ba duk da cewar masu wallafa shirin na fina finan basu ci gaba da sakata ba a cikin shirin sabbin fina finai. Hakan kuwa tana faruwa ne sakamakon cewar akwai fina finai da dama wadanda Jaruma Sadau take cikin su da basu samu fita ba a kasuwannin fina finai a lokacin da akayi kata ita waccan kora.


Da dama kan kalli korar Rahama Sadau a matsayin kalubale ga wadansu ‘ya’yan kungiyar. Sai dai a nata bangaren a wata hira da tayi da Hafsat Abubakar ta shaida cewar babu wanda ya taba sanar mata cewar an kore ta daga masana’antar shirya fina finai na Hausa. Sadau ta kara da cewa ita ce a kankin kanta ta daina shiga shirye shiryen a duk tsawon wadannan lokutan.

A ranar 8 ga watan Oktoba na dubu biyu da sha shida (8 October 2016) Jaruma Sadau ta samu fitowa a wani shirin fim a harshen turanci mai suna Sons of the Caliphate wanda tashar EbonyLife TV kan nuna.


Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku
Isar
da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu

Domin samun Labarai,Nishadi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya

Source: MURYAR AREWA
TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user