Wednesday 3 January 2018

Karanta Kaji: 'Yan Gida Daya Duk Sun Mutu A Wani Hadarin Jirgin Sama

Tura Wannan Zuwa Ga

Wani jirgin sama me dauke da Amurkawa ya fado kuma ya kone inda yai sanadiyyar mutuwar gabaki daya wanda yake dauke dasu.

Jami'an kasar Costa Rica sunce suna binciken sanadin faduwar jirgin saman da ta wakana jiya Lahadi, a wani yanki mai duwatsu da bishiyoyi wanda ke yamma da birnin San Jose. Amurkawa su 10 dake cikin jirgin tare da matukansa su biyu sun mutu a wannan hatsari.

Jami'ai sunce jirgin, mallakar wani kamfanin safarar jiragen saman kasar mai suna Nature Air, ya kama da wuta a lokacin da ya fado. Babu wanda ya tsira da rai a cikin jirgin.

Wata dake zaune a bayangarin birnin New York, ta ce 5 daga cikin wadanda ke cikin jirgin 'Yan gida daya ne kuma hutu suka tafi.

Ta ce 'yan'uwan nata da suka hallaka a wannan hatsari sune Bruce da Irene Steinberg da 'yayan su maza uku Matthew, William da Zachary dukkansu mazauna garin Scarsdale.

'Yar'uwar ta Bruce, Tamara Steninberg Jacobson, tayi amfani da shafin facebook indata dora hotunan su ta kuma bayyana cewa suna cikin dimauta da jimami.

A lokacin da yake magana da manema labarai, Darektan kula da harkokin zirga zirgar jiragen saman farar hula na Costa Rica, Enio Cubillo, yace jirgin da akai shata na Nature Air ya tashi ne da tsakar rana jiya lahadi daga Punta Islita inda ya kama hanyar San Jose a lokacin da ya fado, ya kuma bayyana sunan matukin jirgin Juan Manuel Retana a matsayin kwararre, kuma suna ci gaba da binciken dalilin hadarin.

Shugaban kasar Costa Rica Luis Guillermo yace gwamnatin sa ta yi tsannanin nadama akan faruwar lamarin

Shafin komai da ruwanka, Dadinkowa24 munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

Isar
da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradinmu

Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address
kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa
kamar haka dadinkowa24.blogspot.com

Ku hanzarta sanar da 'Yan Uwa da abokanan
Arziki sunan Website din Mu me Albarka, don
ganin sabbin posting din Mu sai ku duba cikin
website din akwai "Home" sai ku shiga,
mungode

Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin
Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa na
yau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin
bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya
Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin
Cikin Mu Always Visit==http://
dadinkowa24.blogspot.com

Ku Cigaba da Kasancewa da Shafin
Dadinkowa24 aduk inda kuke a fadin Duniya
farin cikin ku shine Farin cikin Mu

Babban Shafi a Yanar Gizo da
ke gabatar da
shirye-shiryensa a cikin harshen Hausa Zalla
cikin 24 Hours ba tareda kakkautawa ba

Burin shafin DADINKOWA24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje daya a ko ina suke

Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me
hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu
Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga
Suleman Abubakar saboda awajensa musami
Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani
ba, adinga yimana Uziri

ALLAH yabar Zumunci Amin

Source By ©Voa Hausa

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user

0 comments: