Wednesday 3 January 2018

Siyasar Nigeria: Nad'a Matattu A Gwamnatin Tarayya Abun Kunya Ne Ga Buhari –Jam’iyyar APDA

Tura Wannan Zuwa

Wata jam’iyyar siyasa a Nijeriya (APDA) ta jefa wa shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari tambaya kan cewar ta yaya aka yi har ya yi sake wajen nada matattu domin su jagoranci wasu hukumomin gwamnatin tarayya, inda jam’iyyar ta ce kurakurai suna dankare a cikin nadin mukaman siyasar na Buhari.

Jam’iyyar ta ce kuskuren da aka samu wajen nadi mukaman abun kunye ne ga kasar Nijeriya da kuma nuna nakasu ga dukkanin jama’an da suka ga sanawar jerin jadawalin sunayen shuwagabanin da za su jagoranci hukumomi da ma’aikatun gwamnatin tarayyar.

Jam’iyyar sun dai ta bayyana cewar mutane tara ne aka samu sun rigaya sun mutu a cikin jerin sunayen da Buharin ya fitar da su shugabanci sashin hukumomin da kuma wasu ma’aikatu da sashi-sashi na gwamnatin tarayya.

Jam’iyyar ta APDA ta yi wadanan jawaban ne a cikin wata sanarwar manema labaru wacce suka raba ta a jiya Lahadi wacce babban sakataren watsa labaru na jam’iyyar Tosin Adeyanju ya sanya wa hanu, ya kuma baiwa shugaban Nijeriya Buhari shawarar gami da yin kiresa da ya bayar da umurni wa wadanda abun ya shafa domin su dawo da martabar tsarin fidda jadawalin domin kaurace wa aikata abun kunya a idon duniya da kuma abun kunya a cikin kasa.

Ya ce, sun zura ido su ga jerin sunayen da Buharin zai fitar domin suna tsammanin za a fito da hazikai, jajirtattu kuma mutane masu nagarta daga cikin Nijeriya wadanda za su yi aiki tukuro domin ciyar da Nijeriya gaba ba wai fiddo da matattu ba.

Sun kuma bukaci Buharin da ya daina bayar da dama wajen jawo wa Nijeriya abun kunya da takaici a idon duniya, ya kuma hori gwamnatin tarayya take nutsuwa sosai wajen tafiyar da aiyukansu.

A ranar juma’ar nan ne dai shugaban Nijeriyan ya amince da nade-naden mukaman shuwagabanin da za su jagoranci sashi-sashi na wasu hukumomin da ma’aikatun gwamnatin tarayya, inda a cikin sunayen ka samu matattu a cikin jadawalin.

Wannan yanayi mai ban mamaki da ta’ajibi, shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari, ya nada wasu matattu a matsayin jagorori da mambobi na wasu hukumomin gwamnatin tarayyar kasar, to amma a wata majiya ta shaida ma na cewa, hakan ya faru ne sakamakon dadewa da sunayen su ka yi a ajiye ba tare da ya sanya mu su hannu ba, sakamakon jinya ya yi fama da ita a wajejen karshen shekarun baya.

Wannan kuskuren dai na ci gaba da jawo cecekuce a fadin Nijeriya, inda kuma gwamnatin ta bukaci ministoci su bayar wa sabbin nada-naden izinin fara aiki nan take, jadawalin dai ya fito ne daga babban sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha a ranar juma’ar.

Shafin komai da ruwanka, Dadinkowa24 munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

Isar
da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradinmu

Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address
kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa
kamar haka dadinkowa24.blogspot.com

Ku hanzarta sanar da 'Yan Uwa da abokanan
Arziki sunan Website din Mu me Albarka, don
ganin sabbin posting din Mu sai ku duba cikin
website din akwai "Home" sai ku shiga,
mungode

Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin
Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa na
yau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin
bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya
Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin
Cikin Mu Always Visit==http://
dadinkowa24.blogspot.com

Ku Cigaba da Kasancewa da Shafin
Dadinkowa24 aduk inda kuke a fadin Duniya
farin cikin ku shine Farin cikin Mu

Babban Shafi a Yanar Gizo da
ke gabatar da
shirye-shiryensa a cikin harshen Hausa Zalla
cikin 24 Hours ba tareda kakkautawa ba

Burin shafin DADINKOWA24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje daya a ko ina suke

Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me
hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu
Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga
Suleman Abubakar saboda awajensa musami
Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani
ba, adinga yimana Uziri

ALLAH yabar Zumunci Amin

Source By ©Hausa Leadership

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user

0 comments: