Wednesday 3 January 2018

Karanta Kaji: Manyan batutuwan da suka faru a Nigeria a shekarar 2017

Tura Wannan Zuwa

A siyasance, Najeriya ta karya da batun rashin lafiyar shugaban kasar Muhammadu Buhari ne a watan Janairun 2017.

Shugaban bai samu cikakkiyar lafiyar zama a gida ba har ya gudanar da harkokin mulki yadda ya kamata sai a watan Agusta lokacin da ya koma gida daga birnin Landan inda ya yi jinyar sama da kwana 100, bayan da dama daga 'yan kasar sun cire rai.

Sai dai a lokacin da Buhari yake London, wata kungiya mai suna Resume or Resign sun yi ta gudanar da zanga-zanga inda suka yi kira ga Shugaban ya koma gida ko kuma ya sauka daga mulki, duk da yake kafin ya tafi jinya ya mika ragamar jagorancin kasar a hannun mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo.

Wani abu kuma da ya jawo ce-ce-ku-ce a lokacin shi ne sakon muryar da Shugaba Buhari ya aike wa 'yan Najeriyar a harshen Hausa domin taya su murnar bukukuwan karamar sallah.

Muryar shugaban dai ta janyo zazzafar muhawara.

Yayin da sakon ya bai wa wasu tabbacin cewa shugaban na raye sabanin masu ganin cewa ya mutu, wasu mutanen kuma sun ce muryar ta nuna shugaban na cikin yanayi irin na mutu kwakwai rai kwakwai, a inda wani sashe kuma ya tuhumi shugaban da bangaranci saboda amfani da harshen Hausa maimakon Turanci.

Kuma daga wannan jawabi ne kungiyoyin fararen hula suka zage da yin zanga-zanga tare da matsin lamba a gida da waje suna neman shugaban ya koma gida ya ci gaba da jagoranci ko kuma ya yi murabus.

Bayan dawowar shugaban ne a watan Agusta aka samu wata raha irin ta siyasa bayan da mai magana da yawunsa ya ce shugaban ba zai shiga ofis ba har sai an yi 'yan gyare-gyare sakamakon barnar da beraye suka yi a ofishinsa.

Ziyarar Shugaba Buhari zuwa kudu maso gabashin kasar wani yankin da ake kallon ba shi da tagomashin siyasa.

Sai dai wasu na ganin ziyarar ba ta samar da abun da aka je nema ba domin jam'iyyar APC mai mulki ba ta iya kai bantanta ba a zaben gwamnan jihar Anambra, daya daga cikin dalilan da suka sanya Shugaba Buhari kai ziyara yankin.

A ranar 7 ga watan Disamba ne kuma shugaban kasar ya ziyarci Kano, jihar da ya kira cibiyarsa ta siyasa, wacce kuma ta fi kada masa kuri'a a dukkan zabukan da ya fafata a cikinsu
Sai dai an bayyana ziyarar shugaban zuwa Kano da ba-kuka-ba-guda sakamakon daukar kusan shekaru uku a kan karaga ba tare da waiwayar Kanawan ba.

Kafin ziyarar Shugaba Buhari Kano, wani abu da ya dauki hankali a siyasa a watan Satumba, ministar harkokin mata Aisha Jummai Alhassan, ta fito fili ta ce ba za ta goyi bayan Shugaba Buhari a zaben 2019 ko da a ce ya ayyana aniyarsa ta sake tsayawa takara, tana mai cewa tsohon mataimakin shugaban kasar Atiku Abubakar za ta mara wa baya "saboda shi ne uban gidana a siyasa."

Batun dai ya jawo ce-ce-ku-ce a fagen siyasar kasar inda wasu magoya bayan Shugaba Buhari suka yi kira a sauke ta daga mukaminta yayin da magoya bayanta suka ce ta burge su da wannan kalami domin ta nuna cewa ba ta yaudara a siyasa.

A watan Disamba ne tsohon mataimakin shugaban kasar, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana ficewa daga jam'iyya mai mulki ta APC bisa zargin gazawa zuwa jam'iyyar adawa ta PDP. Amma mutanen da ake ganin za su bi shi kamar Aisha Jummai Alhassan da gwamnan jihar Adamawa, Umar Jibrilla Bindo sun ce za su ci gaba da zama a jam'iyyar ta APC.

Har wa yau, a watan Disamban ne jam'iyyar PDP mai adawa ta zabi sabon Shugaba, Uche Secondus a taronta na kasa da ta yi a Abuja.

An dai samu zarge-zargen tafka magudu a lokacin taron, al'amarin da ya sa masu fashin bakin siyasa ke ganin jam'iyyar ta PDP ba ta daddara ba.

Hakan ya sa wasu 'yan jam'iyyar sun balle inda suka bude abin da kika "sabuwar PDP".

Idan muka kalli zauren majalisun Najeriya kuwa a farko-farkon shekara, za a iya cewa an kai ruwa rana tsakanin majalisar dattawan kasar da bangaren zartarwa kan tabbatar da shugaban rikon kwarya na hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa kasa Ta'annati, Ibrahim Magu.

Majalisar dai ta ki amincewa da Ibrahim Magu bisa rahoton da suka ce hukumar tsaro ta farin kaya ce ta basu.

Sai dai bangaren zartarwa ya kekashe kasa har ma mataimakin shugaban kasar, Farfesa Yemi Osinbajo ya ce su ba za su cire shugaban riko na EFCC din ba.

Ana dai ganin wannan batu ne ya shafa wa Sanata Muhammad Ali Ndume kashin kajin da har ta kai majalisar ta dakatar da shi na tsawon watanni uku, kafin daga bisani ya koma aikinsa a watan Nuwamba.

Irin wannan rashin jituwa tsakanin majalisar dattawa da shugaban hukumar kwastam ta kasa, Hamid Ali kan shigowar shinkafa da kuma kin amincewar shugaban hukumar wajen sanya kayan sarki na hukumar da yake jagoranta, ita ma ta ja hankalin 'yan kasar.

Sanata Dino Melaye ne dai ya tayar da maganar a majalisar inda shi kuma Hameed Ali ya yi burus da maganar.

Tattalin arziki

Idan muka yi waiwaye ta fuskar tantalin arziki a kasar kuwa, za a iya cewa tsakiyar shekarar 2017 ta zo da dan dama-dama sabanin farkonta da kuma shekarar da ta gabace ta lokacin da kasar ta samu karayar tattalin arziki.

A watan Satumbar 2017 ne Hukumar Kididdiga ta kasar ta ce Najeriya ta fita daga matsalar tattalin arzikin sakamakon bunkasar da aka samu a fannin noma da man fetur da masana'antu da kuma kasuwanci.

A watan Nuwamban shekarar ne kuma shugaban Najeriyar, Muhammadu Buhari ya mika wa majalisar kasar kudirin kasafin kudin kasar na shekarar 2018 na tsabar kudi har naira biliyan 8,612 wanda ya fi kowanne girma a tarihin kasar.

Cin hanci

Manyan batutuwan da suka kankane batun yaki da rashawa da cin hanci a shekarar 2017 su ne kamun da hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arziki ta'annati ta yi na tsabar kudi fiye da dalar Amurka miliyan 43 a wani gida a birnin Legas da aka yi zargin mallakar tsohon shugaban hukumar tsaro ta kasar ne NIA wato Ayo Oke, al'amarin da ya janyo masa rasa aikinsa daga karshe.

A lokacin ne kuma aka kori tsohon sakataren gwamnatin tarayyar kasar, David Lawal Babachir kan zargin karkatar da wawure kudaden 'yan gudun hijra.

An dai kai ruwa rana kafin Shugaba Buhari ya zartar da korar shugabannin biyu da wani kwamitin da ya kafa domin binciken badakalar karkashin jagorancin mataimakinsa, Farfesa Yemi Osinbajo ya bayar da shawara.

Wannan dai ya janyo suka daga kungiyoyi masu rajin yaki da rashawa da cin hanci.

A farkon watan Nuwamba ne kuma wata jaridar kasar Jamus ta saki wasu takardun tonan silili da ake yi wa lakabi da Paradisepapers da ke fallasa yadda shugabannin Najeriya suka rika ketare biyan haraji.

Daga cikin 'yan Najeriyar da jaridar ta ambata akwai shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki da shugaban babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele da dai sauransu.
Kun san wanda ya mallaki kuɗin da EFCC ta gano a Lagos?

Tsaro

Idan muka koma bangaren tsaro, za a iya cewa Najeriya ta ga tasku duk da cewa abun da dama-dama idan aka yi la'akari da shekarun baya lokacin da hare-haren kungiyar Boko Haram suka yi kamari.

A watan farko na shekarar 2017 ne sojojin saman kasar suka yi irin abin nan da Bahaushe ke cewa garin neman gira an rasa ido, wato sojojin na sama sun kashe mutum kimanin 70 a kauyen Rann na jihar Borno kudu maso arewacin Najeriya a watan Janairu bisa abin da suka kira kuskure a kokarinsu na yaki da kungiyar Boko Haram.

A watan Janairun ne kuma hare-haren Boko Haram suka sake yawaita har ma ta kai ga a watan Yuli aka yi garkuwa da wasu ma'aikatan aikin hakar man fetur a jihar Borno guda uku wadanda har kawo yanzu suna hannu.

Har dai karshen watan Nuwamban 2017 an yi ta samun karuwar hare-haren Boko Haram a jihohin Borno da na Adamawa duk da cewa an hana ta fallasa zuwa sauran sassan kasar.

Sai dai kuma a shekarar ta 2017 ba a samu yawaitar hare-haren masu tayar kayar baya na tsagerun Naija Delta ba, abin da ake ganin ya taimaka wajen farfadowar tattalin arzikin kasar sakamakon samun kudaden shiga da a baya suka samu tawaya saboda fasa bututan man fetur da 'yan kungiyar suka rika yi.

Kungiyar masu fafutukar kafa kasar Biafra, wato IPOB karkashin jagorancin Nnamdi Kanu ta shiga kundin tarihin kasar na shekara 2017, al'amarin da ya harzuka wasu kungiyoyin arewacin kasar suka bai wa 'yan kabilar Igbo mazauna yankin zuwa 1 ga watan Oktoba da su san inda dare ya yi musu.

Kungiyar IPOB ta so tsayar da al'amuran yankin kudu maso gabashin kasar, a inda har ta yi barazanar hana gudanar da zaben gwamna a jihar Anambra.

Sannan kuma rahotanni a kafafen sada zumunta suka yi ta yawo cewa 'yan kungiyar na kai wa 'yan arewacin kasar mazauna kudu maso gabashi hare-hare.

Haka dai ta ci ba ta ci ba aka yi ta fama har lokacin da sojojin kasar suka far wa kauyen su Nnamdi Kanu kuma tun lokacin ba a kara jin duriyarsa ba.

Za a iya cewa ba a taba samun wata shekara da rikicin makiyaya da manoma ya rincabe ba kamar 2017, har ta kai ga kungiyar makiyaya sun yi barazanar kai gwamnatin jihar Taraba kotun hukunta manyan laifuka ta Duniya wato ICC, al'amarin da gwamnatin ta ce shi laifi ai tudu ne.
Jihohin da aka fi samun irin wannan rikici dai su ne Benue da Taraba da Kaduna.

Wani rikici mai kama da wannan shi ne wanda ya faru tsakanin Fulani da Bachama a Numan na jihar Adamawa, abin da ya yi sanadiyyar mutuwar mata da kananan yara da dama.

Hare-hare kan garuruwa da ake zargin masu satar shanu ke kai wa ya kazanta a 2017 domin a watan Nuwamba ne masu satar shanun suka bai wa al'ummar wasu garuruwa a jihohin Zamfara da Sokoto kwanaki da ko dai su ba su kudade ko kuma su bar garin.
Har wa yau, garkuwa domin neman kudin fansa ta tazzara a 2017 a kusan dukkanin fadin Najeriya.

Yankin da ya fi kaurin suna a shekarar shi ne titin Abuja zuwa Kaduna da kuma Kaduna zuwa Birnin Gwari.

Al'amarin ya kai ga rundunar 'yan sanda jibge jami'anta fiye dari biyar a hanyoyin.

Jami'an tsaron dai sun yi nasarar cafke wani da ake zargin ya shahara wajen yin garkuwa da mutane domin neman kudin fansa a Legas mai suna Evans.

Mabiya mazhabar Shi'a karkashin Islamic Movement of Nigeria sun yi zanga-zanga ta fi sau shurin masaki a 2017 suna masu neman a saki jagoransu, Sheihk Ibrahim El-Zakzaky wanda gwamnatin kasar ke rike da shi tun 2015.

Kuma a ranar 12 ga watan Disambar nan ne mabiya Shi'ar suka yi tarukan juyayin kame shugaban nasu shekaru biyu ba tare da hukunci ba.

A watannin Nuwamba da Disamba ne Maryam Sanda, matar da ake zargi da kisan mijinta saboda samun wasikar wayar hannu ta wata mace daban a wayar mijin nata, ta gurfana gaban kuliya manta sabo har karo uku a Abuja.

Har wa yau, irin wannan al'amari ya faru a jihar Zamfara inda aka zargi wata macen daban da aikata irin wannan aiki sai dai kuma ita nata mijin bai mutu ba.

Lafiya

A fannin lafiya kuwa, wani sabon nau'in cutar sankarau ne da ya fara daga jihar Zamfara da ke arewacin kasar ya kuma ya yadu zuwa jihohi 15, ya yi sanadiyyar mutuwar daruruwan mutane.

A shekarar ne kuma wani zazzabi mai tsanani da aka yi wa lakabi da suna 'merger' a arewacin kasar wanda kuma jama'a suka yi amannar cewa annoba ce, ya yi sanadiyyar mutuwar mutanen da dama.

Ilimi

Masana harkar ilimi a Najeriya da kungiyar kwadago dai ba za su taba mantawa da shekarar 2017 dangane da jarrabawar da gwamnatin jihar Kaduna ta yi wa Malaman makarantar firamare, inda fiye da dubu 21 suka fadi jarrabawar 'yan aji hudun firamare da aka ba su.
Kuma sakamakon hakan gwamnatin jihar ta ce za ta maye gurbin Malaman da wasu sabbi.

Wasanni

A harkar kwallon kafa, za a iya cewa shekarar ta 2017 ta zo wa Najeriya da hannun dama domin a shekarar ne ta samu cancantar shiga a dama da ita a gasar wasan kwallon kafa ta duniya da za a yi a Rasha a shekara mai kamawa.

Kwallo daya tilon da Alex Iwobi ya zura wa Zambia ce ta sa kasar ta zamo ta farko a nahiyar Afirka wajen samun gurbi a gasar kwallon duniyar.

Sai dai kuma za a iya cewa murna ta so ta koma ciki lokacin da hukumar kwallon kafar duniya ta ci tarar Najeriya kan sakacin kasar na barin Shehu Abdullahi ya buga wasan da Najeriya ta ci Algeria 1-0 duk da cewa tana sane da bai kamata ya yi wasan ba saboda yana da dauke da katin gargadi guda biyu.

Fifa ta kuma damka wa Algeriya nasarar da aka samu a wasan abin da ke nuni cewa an datse wa Najeriyar maki uku.

Kusan dai za a iya cewa wadannan batutuwan ba tare da ragin daka ba, su ne dai suka kankane kafafen sada zumunta.

Yayin da kuma wasu batutuwan sun faru sannan sun mutu a shekarar ta 2017, wasu kuwa za a iya cewa za su dora a shekara mai kamawa.

Ana kuma hasashen batutuwan siyasa za su fi kankane shekarar ta 2018 bisa la'akari da yadda tuni aka buga gangar siyasa kuma ta fara zaki.

Shafin komai da ruwanka, Dadinkowa24 munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

Isar
da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradinmu

Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address
kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa
kamar haka dadinkowa24.blogspot.com

Ku hanzarta sanar da 'Yan Uwa da abokanan
Arziki sunan Website din Mu me Albarka, don
ganin sabbin posting din Mu sai ku duba cikin
website din akwai "Home" sai ku shiga,
mungode

Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin
Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa na
yau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin
bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya
Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin
Cikin Mu Always Visit==http://
dadinkowa24.blogspot.com

Ku Cigaba da Kasancewa da Shafin
Dadinkowa24 aduk inda kuke a fadin Duniya
farin cikin ku shine Farin cikin Mu

Babban Shafi a Yanar Gizo da
ke gabatar da
shirye-shiryensa a cikin harshen Hausa Zalla
cikin 24 Hours ba tareda kakkautawa ba

Burin shafin DADINKOWA24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje daya a ko ina suke

Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me
hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu
Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga
Suleman Abubakar saboda awajensa musami
Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani
ba, adinga yimana Uziri

ALLAH yabar Zumunci Amin

Source By ©Bbc Hausa

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user

0 comments: