Wednesday 3 January 2018

Karanta Kaji Wannan: Jawabin Shugaba Buhari Na Sabuwar Shekara A Takaice

Tura Wannan Zuwa

Ina matukar bakin ciki kan yadda wasu tsirarun mutane suka hana al'ummar kasar nan samun walwala na bukukuwan Kirismeti da sabuwar shekara ta hanyar haddasa karancin fetur da gangan wanda hakan ya hana wasu samun yin tafiya zuwa garuruwansu saboda Tsadar kudin mota, don haka na yi alwashin hukunta wadannan tsirarun mutanen

> " Abu na biyu, Ina son sanar da ku irin matakan da gwamnati ke dauka kan inganta harkokin ci gaban kasa saboda muna shirin fadada ayyukan hanyoyin mota da na jiragen kasa da kuma harkar wutar lantarki.

A game da harkar jiragen kasa, mun sanyawa kanmu wa'adi wanda tuni aikin gina hanyar jirgin kasa na Legas zuwa Kano ya rigaya ya yi nisa. " Muna sa ran kafin karshen shekarar 2019, aikin titin jirgin kasa sai kai garin Ibadan daga Legas

> " A game da ayyukan hanyoyi kuwa, an karfafa hukumar kula da hanyoyi ta kasa( FERMA), wadda aka dorawa nauyin yin gyara dukkanin hanyoyin da suka lalace a cikin makonni 12. Za a yi amfani da kudaden da aka samu ta hanyar tsarin, SUKUKU na Naira Bilyan 100 wajen aikin hanyoyi 25 da ke fadin kasar nan kamar haka:

a. Hanyar Oyo – Ogbomosho,
b. Hanyar Ofusu – Ore – Ajebandele – Shagamu,
c. Yenagoa Road Junction – Kolo Otuoke – Bayelsa Palm,
d. Enugu – Port Harcourt Dual Carriage Way,
e. Onitsha – Enugu Expressway,
f. Kaduna Eastern Bypass,
g. HanyarKano – Maiduguri
h. Hanyar Abuja – Lokoja – Benin
i. Hanyar Suleja – Minna

> " A game da harkar wutar lantarki kuwa, gwamnati ta bayar da Tallafin Naira bilya 701 ga kamfanonin da ke samar da hasken wutar lantarki don inganta ayyukansu. An kuma samu nasarar kammala ayyukan gyaran wasu tashoshin wutar lantarki wanda ya hada da na Afam, Katsina sai na Zungeru wanda aka kusa kammalawa. Sauran su ne, tashar Gurara, Kashimbala da na Mambila"

> " Game da tattalin arziki kuwa, za mu ci gaba da aiwatar da wasu tsare tsare na ganin an zaburar da tattalin arzikin kasa. A shekaru biyu da suka wuce, na nemi mutane su koma Gona kuma hakan ya fara tasiri saboda a cikin wannan shekara za mu dakatar da shigo da shinkafa gaba daya"

> " Ina sauraren muhawara da ake yi game da canjawa Nijeriya fasali sai dai abin sanin kawai shi ne, babu wani tsarin gwamnati da ba shi da ta sa matsala. Kasance kuma kakar siyasa za ta fara a cikin wannan, Ina kuma kira ga 'yan siyasa su guji amfani da kabilanci da addini wajen raba kan al'umma.

Shafin komai da ruwanka, Dadinkowa24 munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

Isar
da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradinmu

Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address
kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa
kamar haka dadinkowa24.blogspot.com

Ku hanzarta sanar da 'Yan Uwa da abokanan
Arziki sunan Website din Mu me Albarka, don
ganin sabbin posting din Mu sai ku duba cikin
website din akwai "Home" sai ku shiga,
mungode

Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin
Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa na
yau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin
bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya
Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin
Cikin Mu Always Visit==http://
dadinkowa24.blogspot.com

Ku Cigaba da Kasancewa da Shafin
Dadinkowa24 aduk inda kuke a fadin Duniya
farin cikin ku shine Farin cikin Mu

Babban Shafi a Yanar Gizo da
ke gabatar da
shirye-shiryensa a cikin harshen Hausa Zalla
cikin 24 Hours ba tareda kakkautawa ba

Burin shafin DADINKOWA24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje daya a ko ina suke

Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me
hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu
Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga
Suleman Abubakar saboda awajensa musami
Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani
ba, adinga yimana Uziri

ALLAH yabar Zumunci Amin

Source by ©Hausazone

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user

0 comments: