Friday 19 January 2018

KARANTA WANNAN QISSA KUJI MAKIRCIN SHAIDAN

Tura Wannan Zuwa Ga
Wani mutumi ne yatashi tunda wuri yashirya tsaf!
Ya canza tufafi yayi alwala domin zuwa
masallaci yayi sallar asuba.
Yana kan hanyarsa tazuwa masallaci, kwatsam!


Sai ya fadi, tufafinsa suka lalace.
Sai yatashi ya kakka6e jikinsa ya koma gida ya
canza kaya, ya sake alwala, ya kuma nufi hanyar
masallaci.

Yana isowa inda yafadi dazu sai yasake faduwa!!
Tufafinsa suka sake lalacewa ya kakka6e ya
koma gida ya canza wasu tufafin, yasake alwala,
ya kuma kama hanya zuwa masallaci.
Koda ya iso inda ya fadi harsau 2 dinnan kawai
sai yaga wani mutum rike da fitila, dasuka gaisa
sai mutumin yace dashi:

"Dazu naga kafadi har sau 2, akan hakane nazo
domin in haska maka".

Suka kama hanyar masallaci su 2, sai da suka
isa, sai wanda yafadi dazu yashiga masallaci,
yakuma kira wanda yake haska
masa yashigo suyi sallah tare; amma yaqi
yashigo,
Yayi~yayi yashigo masallaci amma yaqi !!!
Daga qarshe sai mutumin yace masa:
"Da farko dai ni shedan ne.

(sai mutumin yaji tsoro dajin wannan magana).
Yaci gaba da cewa:

A lokacin daka fito zaka masallaci nine na kayar
dakai akaro na farko.

Sanadiyar faduwar dakayi baka damuba kakoma
kashirya kasake dawowa.

Sai Allah ya gafarta maka zunubanka gaba daya!
Akaro nabiyu nasake kayar dakai.

kakuma yin hakuri kasake dawowa baka yanke
shawarar yin zamanka a gidaba.

Sai Allah kuma ya gafartawa iyalanka
zunubansu!!

Shiyasa naji tsoron idan nasake kayar daka Allah
zai gafartawa mutanen kauyenku zunubansu gaba daya.

Shiyasa nayi musu hassada da bakin ciki, domin
kada agafarta masu nafito da fitila har
na tabbata ka isa masallaci lafiya batare daka
fadiba, balantana
agafartamasu, ni kuma ina baqin ciki naji
UBANGIJI yayiwa bawansa gafara)"..
Tofa kunji irin Qiyayyar da Shaytan yakeyi mana.

Yaa Allah kasamu a cikin masu Rinjaye akansa.

Source By ©Tafarkin Tsira
TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user