Friday 19 January 2018

Karanta Kaji: Alamomin zazzabin cizon sauro (Malaria) da yadda za'a nisance shi

Tura Wannan Zuwa

Shimfida

Assalamu'alaikum jama'a barkan Ku da kasancewa da shafin Lafiyata a wannan lokaci

A yau ne wannan shafi mai albarka ya ke kawo muku rubutu akan cutar zazzabin cizon sauro,,wato a turance Malaria, alamomin ta da yadda za a kare kai daga kamuwa da wannan cuta.

To da farko dai kaman yadda kusan kowa yana jin ko ya taba jin an anbata sunan "Malaria" wato zazzabin cizon sauro. Wannan cuta na kashe dubban mutane a ko wacce shekara mussamman ma yankinmu na Africa wanda cutar tafi addaba. Haka ne ya sa wannan shafi ya daura damarar ilmintar da yan-uwa a takaice akan wannan cuta.

Mecece ita cutar ?

a takaice dai cutar zazzabin cizon sauro cuta ce da ke samuwa ta hanyar cizo da sauro ke yi wa dan-adam da ya ke dauka da wannan kwayar cuta ta malaria. Sauro ba a jikinsa cutar take ba, a'a sai ya ciji wani dan-adam dake dauke da wannan cuta a jikinsa kafinnan idan ya ciji wanda bai da kwayan cutan a jikin sa sai ya kamu. Dalili, ita wannan kwayan cuta ta malaria na zama cikin jini ne daga zaran sauron ya ciji mutum, kafin lokacin da za ta bayyyana alamominta a jikin dan-adam, shi ko sauro dama abincin sa jini ne.

Wannan yasa cutar zazzabin cizon sauro ke yaduwa cikin al'umma cikin karamin lokaci idan har ba a dauka matakan kariya daga wannan cutar ba, wanda anan gaba za muyi dan bayanin yan wasu hanyoyi na samun kariya ga cutar.

Illar cutar
cutar na da illa kwarai da gaske, wanda ta kan kai ga:

Hauka:
idan ba'a magance cutar da wuri ba har ta ci jikin mutum to takan taba kwa-kwalwa, daga nan sai ta juyar da kwakwalwar mutum har ya kai ga hauka ana cewa ai an masa sihiri ne, a'a ba wani sihiri malaria ce.

Mutuwa:
cutar na saurin kisa idan akai mata sakaci ba'a samu anyi maganinta da wuri ba. domin tai karfi za tai ga kona jini da halaka sassan jiki masu muhimmanci kamar su hanta da sauransu.

Yanayin yaduwar cutar

cutar na yaduwa ta hanyar cizo na sauro kaman yadda muka dan yi tayani a baya.

Ita cutar ba kowanne sauro ke yada ta ba. iya macen sauron ce ke yada wannan cutar. ta kan dauko cutar daga cikin jinin mutum mai dauke da kwayar cutar, sa'annan tana cizon wanda bai da cutar, to ta yaba masa.

wannan cuta ta zazzabin cizon sauro ta kan shiga cikin jini ne yayin da sauro mai dauke da wannan cuta ya ciji mutum, daga nan za ta tafi zuwa hanta ta zauna har zuwa lokacin da za tai karfi ta fara bayyana alamomin ta a jikin mutum, kuma alamomin ta basa bayyana daga lokacin da sauron yai cizo ya saka kwayar cutar har sai ta kai tsawon kwana (10 -15) goma zuwa shabiyar kafin su fara bayyana.

Alamomin cutar

Alamomin cutar sun hada da:
• zazzabi
• amai
• ciwon gabobi
• ciwon kai

a wassu lokuta idan ta fara kamari takan haifar da alamomi kamar haka:

• shashshekewa (Convulsion)
• jiki zai ta kar-karwa
• ido zai yi yalo
• mutum zai na ganin abubuwa wanda shi mai lafiyan ba zai gani ba (Hallucination).
• Jan dogon numfashi (Deep breathing)
• mutum zai kode (alamun babu jini a jikin mutum)

Wadannan sune wassu daga cikin alamomi na cutar, da anga wani daga cikin alamomin to ai maza-maza a garzaya asibiti mafi kusa.

Hanyoyin da za a bi don kare kai daga kamuwa da wannan cuta
Akwai hanyoyi da za a bI don kare kai daga wannan cuta ta zazzabin cizon sauro.

Hanyoyin sune kamar haka:

• Tsaftace muhalli
Sauro na zama a wuri ko muhallinin da ke da Kazanta, don haka ne yasa duk wurin da ke da ciyawa ko kwata wanda ba a gyarawa sauro zai ta sintiri a wajen ko muhallin.

Idan aka ce tsaftar muhalli ba ana nufin cikin gida ba kawai a'a har da ma bandaki,cikin gidan Kansa,daki da bayan gida.

idan akwai ciyawa a bayan gida a nome ta ko ai mata feshi. Idan kuma cikin gida ne mai ciyawa shima a gyara. Bandaki ma a rika wankeshi ana gyara shi. haka daki ma a rika tsaftace shi.

• Amfani da ragar sauro (Mosquitor net)
abu na biyu kuma mai muhimmanci wajen kare kai ga kamuwa da zazzabin cizon sauro shine amfani da raga ta maganin sauro (Mosquitor net).

Mosquitor net na dauke da sinadarin da ke
kashe sauro. Don hake ne nake shawartar wanda bashi da net da ya nemi net ya fara amfani da shi.

Tabbas idan aka dau wadannan matakai da muka zayyano to da yardar Allah an rabu da wannan cuta.

Rufewa

Daga karshe muna yi wa maziyarta shafinmu fatan alkaira,. Da fatan kuma zamu amfanu daga abinda muka karanta.

Bayan haka muna cewa maziyarta wannan shafi mai Albarka da su rika
Gayyato
abokanku da yan-uwa zuwa wannan shafi don suma su amfani tareda yin Share.

Shafin komai da ruwanka, Dadinkowa24 munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

Isar
da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradinmu

Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address
kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa
kamar haka dadinkowa24.blogspot.com

Ku hanzarta sanar da 'Yan Uwa da abokanan
Arziki sunan Website din Mu me Albarka, don
ganin sabbin posting din Mu sai ku duba cikin
website din akwai "Home" sai ku shiga,
mungode

Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin
Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa na
yau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin
bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya
Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin
Cikin Mu Always Visit==http://
dadinkowa24.blogspot.com

Ku Cigaba da Kasancewa da Shafin
Dadinkowa24 aduk inda kuke a fadin Duniya
farin cikin ku shine Farin cikin Mu

Babban Shafi a Yanar Gizo da
ke gabatar da
shirye-shiryensa a cikin harshen Hausa Zalla
cikin 24 Hours ba tareda kakkautawa ba

Burin shafin DADINKOWA24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje daya a ko ina suke

Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me
hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu
Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga
Suleman Abubakar saboda awajensa musami
Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani
ba, adinga yimana Uziri

ALLAH yabar Zumunci Amin

Source By ©Lafiyata

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user

0 comments: