Tuesday 9 January 2018

Karanta Wannan Yanzu: KADA AYI WASA DA HANKALINKA, DAGA KARSHE AMAIDAKAI JAHILI!!!-Muhammadu Buhari

Tura Wannan Zuwa Ga

Lokacin dana fito na Zabi GENERAL
MUHAMMADU BUHARI, wallahi banyi zaton zan
samu kudi ba ko kadan, kuma banyi zaton yunwa
ko rashin kudi zai magance mini su ba.

Na zabe shine bisa hujjar neman Allah ya tsayar
da zubar
da Jinin bayinsa da akeyi a Arewa maso
Gabashin Nigeria da kuma ragowar Garuruwan
mu na Arewa da sauran wurare a Nigeria.

Har ga Allah na Zabe shine domin naga an tsaida
satar kudin Al'umma ana kashe Makarantun
Gwamnati don kawai raya shafaffu da mai da
kuma bunqasa Makaratun
'Kasashen waje da kudaden Nigeria.

Wallahi ko yanzun nan Buhari ya sake tsayawa
takara to shi zan Zaba! kuma ina da Amsar
dazan bawa Allah gobe 'kiyamah na dalilin yin
hakan.

Na tuna sanda za kaga Sojojin mu suna gudu a
daji kuma 'yan ta'addan Boko Haram suna binsu
suna kamo su.

Na tuna sanda Mutane suke fitowa daga
Garuruwansu, suna gudu suna barin gari basu
dauki Kayan Abinciba, basa tunanin Kudinsu da
suka bari a Gidajensu basa ma tunanin fita da
iyalansu.

Na tuna sanda a Maiduguri da Yobe da wasu
Bangarorin garuruwan Adamawa baka isama ka
fito Sallah ko kuyi taro ba.

Amma cikin ikon Allah yau hatta "yan gudun
Hijira a matsuguninsu suna iya yin zanga zanga
batare da tsoron sanya musu Bomb ko 'yan Boko
Haram zasu kai musu
mummunan hari kosu yanka su ba,
A yau masu gudun Hijirah a Bauchi da Kano da
Kaduna da ragowar
wurare sun koma gidajensu a Maiduguri da Yobe
da wasu garuwan Adamawa.

Wannan kawai ya isa kullum na tuna na kara
yiwa Allah
godiya wani lokacin ma na fadi qasa nayi
Sujjadar godiya ga Allah.

Tabbas ina da 'kwarin gwiwar kamar yanda wan
nan yazamo Tarihi a yau gobe ma maganar
Yunwa da rashin kudi a hannun Jama'a zai zamo
tarihi shima.

Allah ya fada mana a Qur'an akan Yahudawa
yace damu:
" ﻟﺌﻦ ﺷﻜﺮﺗﻢ ﻷﺯﻳﺪﻧﻜﻢ ﻭﻟﺌﻦ ﻛﻔﺮﺗﻢ ﺇﻥ ﻋﺬﺍﺑﻲ ﻟﺸﺪﻳﺪ ".

"Wallahi idan har kukayi godiya[bisa ni'imar da
nayi muku],
wallahi [inji Allah] zan 'kara muku[ wata ni'imar],
(amma
kuma) Wallahi in kuka butulcewa [ni'imar tawa]
lallai Azaba
ta akwai ra'da'di a cikinta"

Allah kada kasa mu zama masu butulci ga
ni'imar da kayi
mana akan harkar tsaro da dakushe Cin hanci da
rashawa.

Ya Allah karka kamamu da maganganun Wawaye
a cikinmu kamar yanda muke rokon ka Allah bisa
godiyar mu da
Ni'imar ka,ka kawo mana Karshen wahalhalun
tattalin Arzikin da muke fama dashi

BUHARIYYA!!
BUHARIYYA!!

Menene hukuncin masu fadin wannan kalmar?

Shin kunyi imani cewa Buhari ne mai
azurtawa ?

Shin Buhari ne mai talautawa? ko ciyarwa da
tufatarwa?

shin baku jin kunyar ALLAH kuna zagin dan
uwanku musulmi shugaban ku ?

Shin Baku yarda
Allah ne ke azurta bayin sa bane?

Shi ke bada
abinci, shi ke rufa asirin bayin sa ba wani mutum
ba?

Shin ko kunsan gidan fiyayyen halitta manzon
Allah Baban Alkasim Annabi Muhammadu(S.A.W
.) an taba yin kwanaki ba'a hura wuta an dora
tukunnya a gidan ba, babu abinda sukeci sai
dabino da ruwa???

shin kun tabayin sati 3 ba'a hura wuta a gidan
kuba?
kwana 3 fa?

Shin ko bakwa karanta AlQUR'ANI ne?

ALLAH MADAUKAKIN SARKI YACE
ﻭﻟﻨﺒﻠﻮﻧﻜﻢ ﺑﺸﻲﺀ ﻣﻦ ﺍﻟﺨﻮﻑ ﻭﺍﻟﺠﻮﻉ ﻭﻧﻘﺺ ﻣﻦ ﺍﻷﻣﻮﻝ
ﻭﺍﻷﻧﻔﺲ ﻭﺍﻟﺜﻤﺮﺕ ............. ﺍﻟﺒﻘﺮﺓ 155

MA'ANA: KUMA LALLAINE ZAMU JARABA KU DA
WANI ABU DAGA TSORO DA YUNWA DA NAKASA
DAGA DUKIYA DA KAYUWANKA DA "YA"YAN
ITACE KUMA KAYI BUSHARA GA MASU
HAKURI.

hmmmmm ALQUR'ANI kenan baya tsufa komai
dadewar zamani.

MASU HAKURI SUNE :WADANNAN DA IDAN
MASIFA TA SAME SU SUKE CEWA LALLAI NE
DAGA ALLAH MUKE LALLE NE MU GARESHI
ZAMU KOMA

shin bazaku rinka tunani akan wannan ayarba?

duk wanda yake cewa BUHARIYYA ya manta
da wannan ayar idan ka tuna kuma kai/ki maza
ka/ki yi istigifari

ALLAH kasa muna daga cikin masu HAKURI
wadanda idan masifa ta same su suke tunawa
da ALLAH suce
ﺇﻧﺎﻟﻠﻪ ﻭﺇﻧﺎ ﺇﻟﻴﻪ ﺭﺟﻌﻮﻥ

Shafin komai da ruwanka, Dadinkowa24 munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

Isar
da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradinmu

Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address
kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa
kamar haka dadinkowa24.blogspot.com

Ku hanzarta sanar da 'Yan Uwa da abokanan
Arziki sunan Website din Mu me Albarka, don
ganin sabbin posting din Mu sai ku duba cikin
website din akwai "Home" sai ku shiga,
mungode

Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin
Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa na
yau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin
bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya
Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin
Cikin Mu Always Visit==http://
dadinkowa24.blogspot.com

Ku Cigaba da Kasancewa da Shafin
Dadinkowa24 aduk inda kuke a fadin Duniya
farin cikin ku shine Farin cikin Mu

Babban Shafi a Yanar Gizo da
ke gabatar da
shirye-shiryensa a cikin harshen Hausa Zalla
cikin 24 Hours ba tareda kakkautawa ba

Burin shafin DADINKOWA24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje daya a ko ina suke

Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me
hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu
Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga
Suleman Abubakar saboda awajensa musami
Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani
ba, adinga yimana Uziri

ALLAH yabar Zumunci Amin

Source By ©M. Kabiru Muhammad

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user

0 comments: