Monday 8 January 2018

Mafi Yawancin Hausawa Munafukai Ne - Nafisa Abdullahi

Tura Wannan Zuwa Ga
Tauraruwar fina-finan Hausa, Nafisa Abdullahi ta saka wani hoton tauraruwar fina-finan Indiya, Deepika wanda hoton ya nuna tsiraicin deepikar, Nafisar dai ta saka wannan hotone dan ta taya tauraruwar fim din Indiyar murnar zagayowar ranar haihuwarta sannan kuma ta bayayyana cewa dama da gangan ta saka hoton dan ta san wasu zasu iya yin magana.


Hausawa, komai a yi musu sai sun tanka, domin wani yace mata tayi wannan abune a banza, kuma Nafisar ta mayar mishi da martanin cewa shi ma kuwa taga yana yiwa wasu jarumai da yakeso abubuwa a dandalinshi shi ma a banza.

Wani dake goyon bayan Nafisar akan wannan batu yace, "Hausawa akwai munafurci wallahi, idan bakwason irin wadannan abubuwa daga gurin masu nishadantarwa to kawai a daina nishadantar daku, domin ita harkar nishadantar da mutane abinda ta kunsa kenan".

Bayan da ya gama wannan batu nashi sai Nafisa ta rufamai baya da cewa" Rabu dasu.....Asalin munafukaima".


Source: Hausa Media

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user