Thursday 11 January 2018

WATA SABUWA TOFA: ANYI KIRA GA KUNGIYOYI MASU ZAMAN KANSU DAKE KARE HAKKIN BIL’ADAMA DASU TURSASAWA GWAMNATIN NAJERIYA TA SAKI EL’ZAKZAKY

Tura Wannan Zuwa Ga

Rahoton Auwal M Kura

Rubutawar Abdulmumini Giwa

An yi kira ga kungiyoyin masu zaman kansu, masu rajin kare hakkin bil adama da kuma gwamnatocin kasashe da su tursasawa gwanatin Najeriya da ta gaggauta sakin Sheikh Ibraheem Zakzaky domin ya samu daman kula da lafiyarsa.

Shugaban Resource Forum ne na kasa Farfesa Abdullahi Danladi yayi wannan kira a wani taron manema labarai na musamman da aka gudanar a garin Kaduna a ranan laraba.

Ya bayyanawa manema labaran cewa labarin tsanantan yanayin jikin Sheikh Zakzaky ya bayyana ne bayan wani ziyara da na kusa da shi suka kai masa, inda suka bayyana cewa muryarsa ta yi kasa, jikinsa yayi rauni sosai kuma sashen jikinsa na dama baya aiki yadda ya kamata.

Malamin ya kasance a wannan yanayi tun kwanaki bakwai da suka gabata daga ranan da aka yi wannan taron.

Ya kuma kara da cewa dama Shehin Malamin na fama da hawan jini kusan yanzu shekaru goma kenan inda hana masa daman ganin kwararrun likitocin da zasu kula da lafiyarsa da gwamnatin Muhammadu Buhari tayi ya munana lamarin.

Farfesan ya bayyana cewa a lokacin mummunan harin da sojoji Najeriya suka kaiwa Sheihin Malamin a gidansa da ke Zaria a watan 12 na shekara 2015, sun zazzage harsasun bindigoginsu a jikin dattijon da dan shekaru 67 yanzu wanda har ya sa ya rasa idonsa na hagu ya kuma samu rauni a idon dama.

Wani likitan ido na gwamnati da ya duba shi ya bayyana cewa idon nasa na dama na bukatan kula daga kwararru kuma babu asibitin da zai iya yin wannan aiki a kasannan.

Ya kara da cewa hatta likitan da na kusa da Malam suka shirya ya duba jikin nasa, hukuman tsaron na DSS dake tsare da shi sun hana likitan ya gan shi.

Yanayin jikin Malam dai ya tsananta sosai ta yadda a zaune ma yake zama yana sallah kuma gwamnati ta hana a kula da lafiyansa kuma ta ki kula da lafiyan malamin duk da cewa Malam ne ke ciyar da kansa, yake biyan kudin wutansa da sayan mai da ake sanya wa janareta da duk sauran bukatunsa duk da cewa su ke tsare da shi.

Malamin Jami’an ya kara da cewa mai dakin Shehin Malamin, Malama Zeenatu Ibrahim ma na dauke da harsasu da sojoji suka harbeta a lokacin harin da suka kai musu a jikinta. Amma duk da ciwon da take fama da shi sun ki bata daman ta samu kula daga likita domin a cire mata su.

Da ga karshe dai ya bayyana cewa almajiran ShehK Zakzaky sun dauki matakai na hankali wurin ganin cewa an saki jagoransu inda suka shigar da kara kotu kuma kotu ta ba da umarnin a sake shi amma gwamnatin Buhari ta yi burus da wannan umarni.

Ya kara da cewa kuma almajiran suna gudanar da zanga-zangan lumana domin kira ga a saki jagoransu amma gwamnatin sai ta turo yan sanda su bisu da harbi da kisa inda ko a ranar lahadi da ya gabata sun kashe mutum biyu a garin Kaduna kuma suka kama sama da mutane dari a Babban Birnin Tarayya Abuja.

Yace wadannan duka sun saba wa sashe na 35 na dokokin Najeriya da suke kari hakkokin bil adama da kuma sashe 6 na yarjejeniyar kare hakkokin bi adama na Afirka. `

Shafin komai da ruwanka, Dadinkowa24 munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

Isar
da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradinmu

Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address
kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa
kamar haka dadinkowa24.blogspot.com

Ku hanzarta sanar da 'Yan Uwa da abokanan
Arziki sunan Website din Mu me Albarka, don
ganin sabbin posting din Mu sai ku duba cikin
website din akwai "Home" sai ku shiga,
mungode

Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin
Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa na
yau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin
bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya
Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin
Cikin Mu Always Visit==http://
dadinkowa24.blogspot.com

Ku Cigaba da Kasancewa da Shafin
Dadinkowa24 aduk inda kuke a fadin Duniya
farin cikin ku shine Farin cikin Mu

Babban Shafi a Yanar Gizo da
ke gabatar da
shirye-shiryensa a cikin harshen Hausa Zalla
cikin 24 Hours ba tareda kakkautawa ba

Burin shafin DADINKOWA24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje daya a ko ina suke

Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me
hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu
Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga
Suleman Abubakar saboda awajensa musami
Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani
ba, adinga yimana Uziri

ALLAH yabar Zumunci Amin

Source By ©Mujallarmu

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user

0 comments: