Saturday 10 February 2018

Kalli Abubuwan da baku sane ba game da Mutuwar Dan Jarida Mahmoon Baba-Ahmed

Tura Wannan Zuwa Ga

An fi saninsa a duniyar jarida a matsayin
zaqaqurin d'an rahoto, musamman a zamanin
siyasar jamhuriya ta biyu.

Sunansa ya yi sharafi
sosai a rahoton rikicin Mai-tatsine na Kano
wanda Gidan Rediyon Tarayya Kaduna (FRCN) ya
riqa yad'awa a farkon shekarun tamaninoni.

Bai yi zaman lumana da gwamnan Kano na
lokacin ba, Alhaji Abubakar Rimi.

Saboda galibin
rahotanninsa suka ne ga 'bangaren tsantsi na
jam'iyyar PRP. Hakan ya kusantar da shi ga Sabo
Bakin Zuwo. 'Yan 'bangaren ta'bo sun rungume
shi ainun, musamman bayan sun kafa gwamnati
a shekarar 1983.

A duniyar Adabi, marigayin ya rubuta waqoqi
masu yawa da labarai cikin waqoqi. Kazalika ya
fassara litattafan Williams Shakespare irin su
Julius Cesar, Macbeth da Romeo and Juliet.

Babban abin mamaki game da wannan fassara ta
marigayin shi ne yadda ya yi ta cikin ainihin
zubinta na baitocin waqe da sahihin harshe mai
dad'in ji.

Daga baya ya kafa kamfanin Garkuwa
Publications Limited wanda ya riqa wallafa
jaridar SAWABA wacce ta yi wasu shekaru ana
bugawa.

A shekarar 2004, na kasance muqaddashin edita
na wannan jarida. Daga baya bayan jaridar ta
tsaya, sai Sam Nda Isaiah, mawallafin jaridar
LEADERSHIP ya fara wallafa jaridar Hausa mai
suna LEADERSHIP HAUSA, ya kuma tuntu'bi
marigayi da ya yi masa edita.

Marigayin ya ce
a'a, amma zai yi masa aikin tuntu'ba
(consultancy) kuma zai ba shi matashin da zai
masa aikin na edita. A ranar farko ta zuwa Abuja
aikin wannan tuntu'ba, ni ne marigayi ya d'auka
don taya shi.

A iya zaman da na yi da marigayi a wad'ancan
shekaru, na same shi gawurtaccen d'an jaridar
da yake matuqar son aikinsa kuma yake
muhimmantar da harshen Hausa. A wurinsa na
koyi abubuwa da dama da suka shafi rubutun
jarida na Hausa a aikace, kama daga rubuta
ra'ayin jarida (editorial), maqala (article), da
rahoto (news report). Kazalika na koyi yadda ake
hira (interview) da manyan qasa. Marigayi ya
koya min yadda ake jefa wa manya tambayar
qurulla ba tare da shakka ba.

Ban da harshen da zan iya siffanta hikimarsa a
rubutun Hausa a wannan lokaci da idanuwana ke
zubar hawayen rashin wannan MAIGIDA nawa,
illa iyaka kawai in ce mai son gane haka ya duba
litattafansa da maqalunsa a jaridar AMINIYA da
shafinsa na Facebook, lallai tabbas za a gane
harshen Hausa ya yi babban rashi da rasuwar
Mahmoon Baba-Ahmed.

Allah ya nauwara makwancinsa!

Shafin komai da ruwanka, Dadinkowa24 munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

Isar
da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradinmu

Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address
kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa
kamar haka dadinkowa24.blogspot.com

Ku hanzarta sanar da 'Yan Uwa da abokanan
Arziki sunan Website din Mu me Albarka, don
ganin sabbin posting din Mu sai ku duba cikin
website din akwai "Home" sai ku shiga,
mungode

Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin
Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa na
yau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin
bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya
Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin
Cikin Mu Always Visit==http://
dadinkowa24.blogspot.com

Ku Cigaba da Kasancewa da Shafin
Dadinkowa24 aduk inda kuke a fadin Duniya
farin cikin ku shine Farin cikin Mu

Babban Shafi a Yanar Gizo da
ke gabatar da
shirye-shiryensa a cikin harshen Hausa Zalla
cikin 24 Hours ba tareda kakkautawa ba

Burin shafin DADINKOWA24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje daya a ko ina suke

Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me
hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu
Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga
Suleman Abubakar saboda awajensa musami
Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani
ba, adinga yimana Uziri

ALLAH yabar Zumunci Amin

Source By ©Muhammad Bin Ibrahim

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user

0 comments: