Wednesday 7 February 2018

Kalli Yadda Za'a Shirya Bikin 'Yar mai Kudin Africa Aliko Dan Gote

Tura Wannan Zuwa Ga

Hamshakin Dan kasuwa, Aliko Dangote, zai aurar da 'yar sa, Fatima, a watan Maris ga Jamil, dan tsohon shugaban hukumar 'yan sanda, MD Abubakar.

- Ana saka ran mutumin da yafi kowa kudi duniya, Bill Gates, zai halarci daurin auren

- Kamar yadda sanarwa ta gabata, za'a daura auren ne a katafaren Otal din Eko dake garin Legas, a watan Maris, 2018

Wani gagarumin aure na nan tafe a watan Maris na shekarar nan, 2018, a garin Legas, a katafaren Otal, Eko Suite and Towers. Aure tsakanin Fatima dangote da Jamil abubakar.

Auren Fatima, diyar Aliko dangote, mafi kudi a nahiyar Afrika, da Jamil dan tsohon shugaban hukumar 'yan sanda ta kasa, MD abubakar, zai tattara masu hannu da shuni da kuma masu fada aji a daga ko ina a fadin Duniya.

Kamar Yadda rahotanni suka nuna, shugabanin kasashe biyar zasu halarta, har da hamsahakin maidukiya da babu kamarsa a duniya, wato Bill Gate.

An dade ana kishin-kishin din aure tsakanin Fatima da masoyinta Jamil, yanzu ta tabbata zasu saka lalle a cikin shekarar nan.

Rahotannin da jaridar naija.com ta samu basu ambaci ranar da za'a daura auren yaran manyan ba.

Kazalika, ya zuwa yanzu, babu jadawalin yadda shagulgulan bikin zasu kasance ba.

Source by ©Hausaloaded

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user

0 comments: