Friday 9 February 2018

Karanta Kaji Dalili: Bazan Daina yin Film ba Har'abada-Rahama Sadau

Tura Wannan Zuwa

Fitacciyar jarumar fina finan
Hausa ta Kannywood, Rahama
Sadau, wadda aka dakatar daga
shiga harkar Fim, ta bayyana a
ranar Asabar cewar, ta fara
shiga matsaloli ne tun bayan da
ta fara yin shirin fim din ‘yan
kudancin Najeriya da aka fi sani
da Nollywood da kuma na
turawa wato Hollywood.

Rahama ta bayyana irin yadda
take shan bakar wahala daga
aftawan Kannywood, tace abu
ne marar dadi matuka idan
mutun yace zai tsallaka zuwa
shirin finafinai na kudanci ko na
turawa musamman yadda al’adu
da dabi’u suka sha bamban.

Ta bayyana cewar, kowadanne
masu shirya finfinai musamman
wadan da ake ganin sun saba da
dabi’unmu, suna da nasu
yanayin gudanarwar harkar fim
da ta sha bamban da ta
Kannywood.

Rahama Sadau ta yi kira ga ‘yan
uwanta masu harkar fim da
masu shirin shiga harkar da su
sanya damara wajen mai da
hankali akan abinda suka sanya
a gaba ba tare da wani tsoro ko
shakka ba.

“Ina mai baiwa jarumai shawara,
da su nutsu su mayar da hankali
sosai akan duk abinda suka
sanya a gaba, tare da yadda da
abinda suke yi, da kuma yadda
da zabin da suka yiwa kan, in
sun yi haka zasu ci nasara”
“Kasan me kake yi a harkar fim,
ka yi aiki tukuru dominsa, tare
da jajircewa da kuma tsayawa a
kai domin samun nasara da
kuma daukaka, in mutum ya
maida hankali sosai akan abinda
yakeyi to zai ci nasara”

Da aka tambayeta kan rawar da
ta taka akan wani sabon shiri
mai suna “Zero Hour” Wanda
aka kammala aikin daukar shirin
a birnin tarayya Abuja, Rahama
‘yar shekaru 24 tace ta fito a
shirin fim din a matsayin Zainab
ne.

“A cikin shirin na fito a matsayin
Zainab ne wadda take tsakanin
daukar fansar kawunta da aka
kashe da kuma batun abokin
samartakarta wanda shima yake
cikin rudani game da ita a cikin
shirin”

Da aka tambayeta kan batun
lambar yabo da ta samu daga
jaridar Leadership a matsayin
jaruma mafi barkwancita
shekara, tace ta cika da
mamakin jin cewar ita ce ta
lashe wannan lambar yabo.

Source by  ©Jaridar Daily Nigerian
Hausa

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user

0 comments: