Friday 2 February 2018

KARANTA KAJI: A DUNIYA BANI DA WANI BURIN DAYA WUCE NAYI SUNA KAMAR MAHAIFINA-Ahmad Ali Nuhu

Tura Wannan Zuwa

Shafin Mujallar Mu ta buga labari kamar haka:

A hankali,a hankali Ahmad Ali Nuhu ‘Da na biyu na fitaccen jarumi Ali Nuhu yanata zama fitaccen jarumi a jarumai yara ‘Kanana babu kamar sa,a industiri.

Dama hausawa sunce kyawun ‘Da ya gaji mahaifinsa,to Ahmad yana kan hanyar cin wannan gadon.

Ga kadan daga jin ta bakin wannan yaro Ahmad Ali Nuhu:-

*Ka Fadawa Masu Karatu Sunanka*
Sunana Ahmad Ali Nuhu

*A Wace Shekara Aka Fara Sanya Ka A Fim?*

To,gaskiya tun ina karami fim din da aka sanya ni sunansa “CARBIN KWAI”shine fim dina na farko dana fara yi.

*Zaka Kai Shekara Nawa Yanxu Da Yin Fim Din?*
E,to zai kai akalla shekara biyar zuwa shida

*Shekarunka Nawa Yanxu?*

An Haife ni a shekarar 2004 kaga kenan a yanxu inada shekara goma sha biyu (14yrs) a duniya.

*Zaka Iya Rawa A Fim Kuwa?*
Eh, mi zai hana idan haka ta kama zanyi sosae har na burge masoyana

* Mi Kake So Ka Zama Idan Ka Girma?*
Ina son Nazama Injiniya.

Kafar yada labarai ta Hausa.naija ita ma ta buga nata labarin kamar haka:

Ahmad Ali Nuhu din da ya fara fitowa a talabijin tun yana dan shekara biyar a duniya
Dan fitaccen jarumin nan na wasannin fina-finan Hausa a masana'antar fim watau Ali Nuhu mai suna Ahmad ya bayyana cewa yana da burin duniya ta san shi fiye da mahaifin sa a harkar.

Ahmad Ali Nuhu din dai ya bayyana hakan ne a cikin wata fira da yayi da wata mujallar fim a watannin baya inda ya ce yana da burin ya fi mahaifin nasa suna da kuma daukaka a harkar ta shirya fina-finan Hausa.

NAIJ.com ta samu cewa Ahmad Ali Nuhu din da ya fara fitowa a talabijin tun yana dan shekara biyar a duniya ya bayyana haka zalika ya bayyana cewa yana iya taka duk rawar da aka saka shi yayi a cikin fim yanzu haka dai-dai gwargwado.

Daga karshe kuma yaron jarumin ya yi wa masoyan sa da ma dukkan masu sha'awar fina-finan Hausa fatan alheri da kuma godiya tare kuma da rokon su rika basu shawara a duk inda suka ga ba dai-dai ba.

Shafin komai da ruwanka, Dadinkowa24 munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

Isar
da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradinmu

Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address
kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa
kamar haka dadinkowa24.blogspot.com

Ku hanzarta sanar da 'Yan Uwa da abokanan
Arziki sunan Website din Mu me Albarka, don
ganin sabbin posting din Mu sai ku duba cikin
website din akwai "Home" sai ku shiga,
mungode

Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin
Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa na
yau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin
bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya
Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin
Cikin Mu Always Visit==http://
dadinkowa24.blogspot.com

Ku Cigaba da Kasancewa da Shafin
Dadinkowa24 aduk inda kuke a fadin Duniya
farin cikin ku shine Farin cikin Mu

Babban Shafi a Yanar Gizo da
ke gabatar da
shirye-shiryensa a cikin harshen Hausa Zalla
cikin 24 Hours ba tareda kakkautawa ba

Burin shafin DADINKOWA24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje daya a ko ina suke

Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me
hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu
Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga
Suleman Abubakar saboda awajensa musami
Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani
ba, adinga yimana Uziri

ALLAH yabar Zumunci Amin

Source By ©Mujallar Mu and  Naij.com

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user

0 comments: