Wednesday 28 February 2018

KARANTA KAJI: TSORON ALLAH YA HANA SHI YIWA 'YAR MALAMI FYADE AKARSHE KUMA YA AURETA.

Tura Wannan Zuwa Ga

Wani Matashi ne ya tare 'yar wani malami zai yi
mata fyade sai yaji tace ya
tsaya ta fada mashi wata magana da zata
amfaneshi tukuna.

Sai matashin ya tsaya domin Sauraronta

Sai yarinyar tace:

(1) Yanzu idan na tambayeka meye ribarka da
6ata mun rayuwata da kake
shirin yi alhali ni ban 6ata maka naka rayuwar ba,
Me zaka ce?

(2) Ko ka manta Allah zai saka mun ne?

(3) Shin ko ka manta cewa wata rana nima zan
zama uwar wani ne, toh ya
kake tunanin zai ji idan ya san kaine ka 6ata
rayuwar mahaifiyarshi?

(4) Shin baka tunanin zina bashi ce da sai an
biyata dole watarana?

(5) To idan mahaifiyarka ce zata biya maka
bashin zinan da kayi ya zaka ji?

Nifa a shekarun haihuwa ka girmeni ka fini
hankali amma abin mamaki ace har
ka bari ni 'yar qanwar qanwarka in rigaka tunanin
cewa zina sa6on Allah ce.

Zan so ace Allah Ya yafe maka wannan laifin
niyyar da kayi ba tare daka aikata
ba...

Sai matashin nan jikinsa duk yayi sanyi har ya
fashe da kuka ya duqa gwiwoyi
qasa yana mai neman gafarar yarinyar akan ta
yafe masa.

Ai kuwa sai ta yafe masa har tana rarrashinsa
akan ya bar kuka ta bashi
hankicif ya share hawayensa sannan yace mata
toh don Allah tayi masa
alfarma ta aureshi.

Sai yarinyar tace zata amince masa amma tare
da sharadin zai tuba da dukkan
mugayen halayensa, kuma tuba wadda ba zai
sake komawa laifinsa ba.

Sai matashin yayi mata Alkawari har ga Allah ya
tuba ya kimtsu saboda burin
kasancewa cikin salihan bayin Allah.

Sai kawai aka daura aurensu har ya zama
limamin unguwarsu...

Allah ka ganar da masu aikata irin wannan
halayyar kafin mutuwa ta cimma
masu. Allah ka shiryar dasu shiriya irin ta addinin
islama ka basu ikon tuba da
kauracewa aikin shedan.

Su kuma mata Allah ka basu irin wannan tunanin
da ikon yin nasiha aduk
lokacin da wani yake shirin keta mutuncin su.

Allah ya bamu ikon tsare farjin mu sai ga
matayen mu na sunnah.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku
Isar
da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradinmu

Ku hanzarta sanar da 'Yan Uwa da abokanan
Arziki sunan Website din Mu me Albarka, don
ganin sabbin posting din Mu sai ku duba cikin
website din akwai "Home" sai ku shiga,
mungode

Ku cigaba da Kasancewa da Website din Muryarhausa24.com don samun abubuwan more rayuwa na
yau da Kullum

An kirkiri Wannan Shafi domin
bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya
Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin
Cikin Mu Always Visit==http://www.muryarhausa24.com
Ku Cigaba da Kasancewa da Shafin
Muryarhausa24 aduk inda kuke a fadin Duniya
farin cikin ku shine Farin cikin Mu

Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me
hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu
Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga
Suleman Abubakar saboda awajensa musami
Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani
ba, adinga yimana Uziri

Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje daya a ko ina suke

KARIN BAYANI

Zaku iya aiko mana da labari,Nishadi,Fadakarwa,Hausa Novel,Ra'ayi,Labarin Soyayya, Sharhi ko nuna gamsuwar Ku akan yadda muke tafiyar da wannan shafi me Albarka aika sakon ka anan muryarhausa24@gmail.com mungode

Allah ka daukaka harshe Hausa dama Kasa baki
daya Amin Summa Amin.

Source by ©Hassan Goma

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user

0 comments: