Wednesday 28 February 2018

KARANTA KAJI: Wata Kirista kenan datafara Ginin Masallaci a Secondary tareda Burin Musilinta Amma Ta Mutu

Tura Wannan Zuwa

Jiya wani bawan Allah yake bani wani labari
wanda yayi matukar girgizani ainun.
Ya bani
labarin kamar haka: Wata baiwar Allah ce da aka
turo ta jihar Kano domin yin NYSC ko hidimar
kasa.

Ita wannan baiwar Allah ba Musulma bace,
kuma an tura ta babbar makarantar Sakandiren
Gwamnati dake garin Kumbotso wato GSS
Kumbotso.

Ita wannan kwafa ko mai hidimar kasa, ta lura
duk lokacin Sallah idan yayi, dalibai kan yi Sallah
ne a karkashin bishiya ko su samu wani wajen su
rabe su yi Sallah. Ganin hakan ko da yaushe,
yasa ta nemi hukumar Makarantar ta bata dama
domin ta gina masallaci a makarantar, aka bata
dama, wannan baiwar Allah ta siyo kayan aiki
yashi da bulo da siminti sannan tasa a nemo
ma’aikata da zasu dinga yin ginin tana biyansu.

Abin mamakin wannan Baiwar Allah gaba daya
ginin da take yi babu wani wanda ya tayata ko
ya sanya kudinsa a ciki, ita ce kullum take kula
da aikin ginin Masallacin, Lokacin da take gina
masallacin ta nemi da a samu wani ya aureta
domin ya musuluntar da ita, tana yawan nanata
batun a aureta a Musuluntar da ita, amma babu
wanda ya kula wannan batu nata.

Kwatsam wannan baiwar Allah bayan da ta koma
garinsu domin yin hutu, ta kamu da rashin lafiya,
kuma cikin kankanin lokaci Allah ya yi mata
rasuwa. Wannan shi ne labarin da aka bani kan
wannan baiwar Allah mai yin hidimar kasa wadda
take aikin gina wannan Masallaci.
Wayewar garin yau, nace ni kuwa sai naje naga
wannan masallaci da makarantar.

Nayi sa’a na
samu ginin wannan Masallaci yana nan yadda
wannan baiwar Allah ta barshi, sannan na kuma
zanta da Shugaban makarantar (Principal) Zakari
Kofar Mata, ya tabbatar min da cewar labarin da
aka bani dangane da wannan baiwar Allah na
gina wannan masallaci haka yake. Ya zagaya da
ni cikin ginin masallacin na ganewa idona.

Hakikanin gaskiya na jima ban ji abinda ya
girgizani kamar wannan ba. Ace a garin Musulmi
inda Musulmi ne ke yin Sallah, amma wannan
baiwar Allah ta dauki wannan gabarar aiki, ba
tare da jiran wani ko wasu ba domin sanya nasu
kudin a ciki ba. Bugu da kari matar nan ta nemi a
aureta a Musuluntar da ita, amma aka rasa
wanda zai iya amsa mata wannan bukata.

Gashi
Allah ya karbi ranta, tana fatan ta zama
Musulma. Yanzu sabida Allah mutanan da suke
wannan makaranta ba zasu tuhumci kansu kan
hakkin wannan baiwar Allah na kin Musuluntar da
ita ba? Hasbunallahu Wani’imal Wakeel!

Babu wanda zai iya shiga tsakanin Allah da
bawansa, Allah yana ganinmu kuma yana duba
izuwa zukatanmu, watakila wannan baiwar Allah
kafin rasuwarta tayi Imani, Allah shi ne masanin
gaibu da abinda ke fake a garemu. Amma saura
kadan nayi mata adduar Allah ya kai mata ladan
aikinta, amma tunda imaninta bai bayyana a
garemu ba zamu kame baki, Allah shi ne yasan
abinda ya dace da ita. Ba shakka wannan
al’amari ya girgizani.

Abin mamaki wannan al’amari ya faru ‘yan
watanni da suka wuce, amma Masallacin yana
nan yadda wannan baiwar Allah ta fara ginin, da
mutanan wajen, da masu Sallah a wajen, babu
wanda yake da tunin cigaba da wannana aikin
alheri. Na zagaya ginin na kuma ga yadda
wannan baiwar Allah tayi kokari matuka wajen
samarda wannan masallaci.
Wannan ya sake sauyamin tunani gaskiya. Da
yawan aikin alkhairi ba sai kana da tarin dukiya
ba, dan abinda kake da shi zaka iya taimakawa
komai kankantarsa domin ciyar da addinin Allah
gaba. Wannan kuma kalubale ne garemu baki
daya, mu zama jakadu nagari ga Musulunci a duk
inda muke, lallai Malamai sun gaya mana ba’a
sanya wajen baiwa mutum Kalmar shahada.

Wanda duk yake fatan cigaba da ginin wannan
masallaci yana iya zuwa ya karasa. Masallacin
na nan a makarantar Sakandiren Gwamnati dake
garin Kumbotso (GSS Kumbotso) dake daura da
Al-Mukab City dake da mashiga daga Titin zuwa
Zariya kusa da kwanar dawaki.

Allah ka bamu iko
da zuciyar taimakon addininka.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku
Isar
da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradinmu

Ku hanzarta sanar da 'Yan Uwa da abokanan
Arziki sunan Website din Mu me Albarka, don
ganin sabbin posting din Mu sai ku duba cikin
website din akwai "Home" sai ku shiga,
mungode

Ku cigaba da Kasancewa da Website din Muryarhausa24.com don samun abubuwan more rayuwa na
yau da Kullum

An kirkiri Wannan Shafi domin
bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya
Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin
Cikin Mu Always Visit==http://www.muryarhausa24.com
Ku Cigaba da Kasancewa da Shafin
Muryarhausa24 aduk inda kuke a fadin Duniya
farin cikin ku shine Farin cikin Mu

Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me
hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu
Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga
Suleman Abubakar saboda awajensa musami
Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani
ba, adinga yimana Uziri

Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje daya a ko ina suke

KARIN BAYANI

Zaku iya aiko mana da labari,Nishadi,Fadakarwa,Hausa Novel,Ra'ayi,Labarin Soyayya, Sharhi ko nuna gamsuwar Ku akan yadda muke tafiyar da wannan shafi me Albarka aika sakon ka anan muryarhausa24@gmail.com mungode

Allah ka daukaka harshe Hausa dama Kasa baki
daya Amin Summa Amin.

Source by  ©Yasir Ramadan Gwale

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user

0 comments: