Thursday 1 March 2018

Karanta Kaji: Wallahi Babu Yadda Mijina Baiyi ba Nadawo Harkar Film amma Naki Amincewa — Fati Ladan 'Yar Wasan Hausa

Tura Wannan Zuwa Ga
Hajiya FATI LADAN , shararriyar jarumar finafinan Hausa ce, wacce ta bar sana’ar a lokacin da ludayinta ya ke kan dawo, ta yi aure abinta.
Duk cewa ta na da dimbin masoya kuma a na tsaka da rubibin kallon finafinanta, hakan bai hana ta yin bankwana da shirin fim zuwa dakin mijinta ba, domin raya sunnar Ma’aiki.
Editan LEADERSHIP A Yau Lahadi,
NASIR S. GWANGWAZO, ya yi katarin tattaunawa da Fati Ladan a wata haduwa da ya yi da mijinta, Alhaji Yerima Shettima, wanda shi ne shugaban Kungiyar Hadaka ta Matasan Arewa (CNG), inda tsohuwar jarumar ta baje komai a faifai, domin rage radadin kishirwarta da masoyanta ke faman yi.
Ga yadda tattaunawar ta kasance:
Malama Fati Ladan tunda ki ka yi aure an daina jin duriyarki. Shin me ki ke ciki a halin yanzu?
To, da ma burin kowa, wato masoyanmu, iyaye da ’yan uwa shi ne idan a ka aurar da ’ya, su ji shiri. To, shi ya sa a ka ji ni shiru, kuma mu na fata a cigaba da jin shirun, saboda wani lokacin shirun alkhairi ne.
Wasu na kallon matan fim da cewa, ba su zaman aure.
Yadda mutane su ke ganin cewa, matan fim ba su zaman aure, ba gaskiya ba ne, saboda shi aure idan ka lura kamar rai da mutuwa ya ke.
Idan ka yi la’akari za ka ga cewa ai ba auren ’yan fim kadai ke mutuwa ba, amma saboda su ’yan fim an san su, shi ya sa a ke yi mu su kallon cewa bas a zaman aure. Amma auren da ke mutuwa ya fi na ’yan fim yawa. Shi aure da mutuwarsa duka a hannun Allah (SWT) ya ke.
Ke ya ki ka tsinci kanki a rayuwar aure yanzu?
Ni da na yi aure na tsinci rayuwar aure cikin farin ciki da annashuwa kamar yadda na ke fatan na samu, har ma in ce fiye da yadda na ke fatan samu, saboda burin kowacce ’ya mace shi ne ta samu mijin da ya ke son ta kuma ya son darajarta, ya ke kula da ita, ya ke darajanta ’yan uwanta da iyayenta. To, kuma na samu har fiye da yadda na ke tunani. Kuma yiwa ’yan uwana ’yan baya su samu farin ciki haka kamar yadda na samu a rayuwata.
Ya za ki iya kwatanta rayuwar aurenki ta farko da wannan?
(Dariya) Waccan rayuwar ai na yi ta ne kafin na shigo industiri… Na roki Allah Ya ba ni miji mai kula da ni, kuma na gaya ma ka na samu. Don haka ba zan hada shi da wancan auren ba, domin da na samu wannan rayuwar da na ke ciki a yanzu a baya, da ba zan fito daga can na fada wannan gidan ba. To, amma da ya ken a tsinci kaina a yanzu rayuwar wannan gidan ta fi ta wancan, shi ne na ke fatan na yanzun ya zama mijina na har abada. Mutuwa kadai za ta raba ni da shi.
Me ya sa ku ke daina yin sana’ar fim bayan kun yi aure, musamman ma ke da ya ke kin ji dadinta? Mijinki ne ya hana ki?
A’a, mijina ni bai hana ni ba, saboda lokacin da mu ka hadu da shi maganar da ya fara yi min ita ce, zan ci gaba da yin fim dina; ba zai hana ni ba, amma ni da kaina na ce ba na son na ci gaba da harkar fim, saboda ba na son abinda zai kawo min matsala a gidan aurena, saboda na san duk yadda ta yi dadi, idan har na hada rayuwar aurena da rayuwar fim, to dole ne zan tsinci kaina a cikin halin da ban yi zato ba, domin taura biyu bat a taunuwa a lokaci daya. Idan aure, aure; idan fim, fim.
Saboda haka na ce ma sa ban a bukatar na cigaba da rayuwar fim, don na sami kwanciyar hankali, shi ma kuma hankalinsa ya kwanta; na gujewa kananan maganganu ko jita-jita. Yau ko mu (’yan fim) ba mu fito ba mun ce mu na yin fim ba bayan mun yi aure, a gidan mijinmu ma a na bibiyarmu a na cewa wance ta yi kaza, wance ta yi kaza. To, ina ga kuma kin a fitowa kin a tafiya fim?
To, idan haka ne, meye bambancin sana’ar fim da sauran sana’o’i ga mace tunda za ki ga wasu matan su na cigaba da sana’arsu ko aikinsu bayan sun yi aure?
Ka san yadda a ke kallon fim a Arewacin nan namu, musamman a al’adarmu ta Hausa, an dauki fim kamar wani abu wanda ba sana’a ba. Amma masu yiwa fim irin wannan kallon ba su fahimce shi ba ne, saboda fim sana’a ce babba wacce za ka iya rike kanka ka rike wani ma. To, amma yadda yawanci iyayenmu da kakanninmu su ke kallon sana’ar fim da wata fuska biyu, shi ya sa ka ga mu ke kaucewa hada rayuwar fim da auren.
Mafi akasari yanzu da mutum zai bar matarsa ta cigaba da mutum, babu abinda za a fara cewa face ya zama mijin Hajiya ko ya zama mijin-ta-ce ko kuma ai yanzu matar ma ta fi karfinshi. Kaza kaza dai maganganu za su yi ta fitowa, wadanda yau da gobe duk rashin son jin tseguminsa watarana zai dauka. Ka ga daga nan an fara samun matsala cikin rayuwar aure kenan. Ni kuma abinda na kaucewa kenan.
Amma rayuwar aure da rayuwar fim ban ga bambancinsu ba, saboda shi aure za ka iya yin shi kuma idan har za ka iya tsare kanka, to za ka iya zuwa ka yi fim ka dawo gidan mijinka ba tare da ka samu matsala ba, idan har mijinka ya yarda da kai kuma ke ma kin tsare mutuncin kanki, tunda mata su na zuwa guraren aiki su yi mu’amula da mazajen da ba nasu ba, kuma su dawo gidajen mazajensu, amma kuma ba a yi mu su mummunan zato sai ’yar fim. Idan ’yar fim ta ce za ta yi aure tan a cigaba da sana’arta, za ka ga sunan da za a lakaba ma ta, ba za a lakaba wa wannan mata da ke aiki a ofis ba.
Saboda haka fuska biyu da a ka yi a ka bambanta mu da wadancan a ka kasa ganewa ne ya sa mu ke kaucewa cigaba da fim, mu ka gwammace idan mun yi aure sai mu kama wata sana’ar mu hakura da fim.
Yanzu ke wacce sana’a ki ke yi?
Ni yanzu Ina karatu. Kafin mu yi aure da mijina na koma makaranta, saboda yanzu bai wuce min saura shekara daya da ’yan watanni na kammala digirin da na ke yi a Political Science ba. Kuma Ina kiwon kaji, kifi da sauransu.
Shin yanzu ba ki begen masana’antar fim, ki rika ji a ranki kamar ki koma, saboda an ce sana’ar fim ta na da shiga rai?
Mu mata mu na da kayyadajjen lokaci a cikin wannan harka. Yau ko ba ka yi aure ba, don kar ka daina fim, to za fa a daina yi da ke, saboda idan ki na ji da kyau ne, wacce ta fi ki kyau za ta zo, kuma ki na ji ki na gani a saka ta a fim , ke ba a saka ki ba. Idan ki na ji da kuruciya ne, wacce ta fi ki kuruciya za ta zo, kuma a daina yi da ke a cigaba da saka ta. Ki na nan ma za ki ji an fara kiran kid a Anti. Daga Anti  za a fara kiran ki Mama. Daga Mama ki koma Kaka. Shikenan an ajiye ki. Saboda haka ban ji Ina begen industiri ba, saboda abinda zai sa ka yi begen indistiri shi ne ka samu mijin dab a zai kula da kai ba ko kuma ya ki tsare ma ka hakkokinka na aure ba.
To, ni gaskiya na samu mijin da ke kula da ni , ban rasa komai ba, kuma babu abinda na ke nema na rasa a gidan aurena. Don haka ba wani ‘missing’ da na yin a industiri, sai dai kawai na yi ‘missing’ din mutanen da mu ka zauna lafiya da su, kuma rike ni amana. Amma kuma duk da haka ai ba a rabu ba; a na tare, a na yin zumunci, a na gaisawa. To, ka ga babu abinda zan yi bege kenan a cikin harkar.
Kin ce ki na karanta fannin siyasa a jami’a kuma mijinki a Nijeriya ya na cikin fitattun matasan da su ke yin harkoki da siga ta siyasa. Shin ku na da wani buri ne na nan gaba ki zama ‘First Lady’ ne?
(Dariya) Eh to, ni dai wannan kwas ma da na ke yi, ‘in fact’ mijina shi ya zaba min. zabinsa ne y ace na yi Political Science, saboda ni na ce Ina so na yi ‘Business Admin’ (Kasuwanci), amma ya ce ya fi son na karanci siyasa.
To, ban san abinda ke a ransa ba tunda a farkon haduwarmu da shi Ina shirin shiga makaranta, sai ya ce na yi Political Science, sai na ce,to zan yi, amma zabinka ne, ba nawa ba. Har ma na ce, ‘ka na tunanin zan iya’, y ace, ‘za ki iya’. To, kuma cikin yardarm Allah da goyon baya da na ke samu a wurinshi har ga shi yanzu Ina 300 Lebel. To, shi kuma maganar First Lady ko wani abu ai kaddara ce daga Allah. Idan Allah Ya kaddara za ki zama First Lady, ko ba ki karanci Political Science ba, za ki yi. (Dariya)
To, ya maganar haihuwa tun bayan kun yi aure?
To, mu nan mu na ta fata. Ka san mai rai ba ya yanke kauna. Bayan shekaru hudu da aurenmu Allah Ya albarkace mu da haihuwar da namiji, to amma cikin hukuncin Allah Ya karbi KayanShi. To, amma mu na fata Ubangiji Allah ya ba mu rayayyu masu albarka.
Wane sako gare ki ga tarin masoyanki da ’yan baya masu sana’ar fim?
Sakona ga masoyana shi ne nag ode, Allah Ya saka mu su da alheri da soyayyar da su ka nuna min tun lokacin da na ke Kannywood da bayan na yi aure. Ina ji Ina karantawa, a na gaya min, kuma har gobe, idan na wuce, masoyana na nuna sha’awarsu da kuma kauna a gare ni. Ban taba jin wanda ya yi suka a kaina , idan Ina tafiya ba. To, nag ode; Allah Ya bar kauna. Su kuma ’yan uwana ’yan fim gabadaya Ina yi mu su fatan alkhairi. Allah Ya kara daukaka wannan sana’a, kuma duk sharrin da za a zo da shi, domin a gurgunta ta, Allah Ya kade shi.
Allah Ya kawo cigaba fiye da yadda a ke tunani, saboda harkar fim ta yi min komai, domin ita ce sanadiyya haduwata da maigidana. (Dariya)
To, wane sako za ki aike wa sabbinyan mata da ke shigowa sana’ar fim?
Sakona shi ne, ki sani idan kin shigo harkar fim da niyyar ki na so ki yi sana’a ne, to za ta karbe ki a matsayin za ki yi sana’a kuma za ki samu abinda ki ke so. Amma idan kin shigo da rawar kai ne, to shi ma ya na nan ya na jiran ki, saboda kafin ki shigo wasu sun yi sun tafi.
Yanzu na ga yara kanana sun yi yawa a cikin sana’ar. Don haka dole ne za a samu rawar kai ya yi yawa, to amma shawarar d azan ba su ita ce, kamun kai ya na daya da kyau gurin ’yan mace, saboda komai za ki yi ya na da iyaka; ke mace ce.
Namiji an ce duk abinda ya yi ado ne, amma ke ki na da iyakarki a rayuwa. Saboda haka su duba su rika sara su na duban bakin gatari.
Duk abinda za su yi su san cewa, Allah Ya na kallon su. Watarana aure za ki yi. Ba za ki so a zo neman aurenki a rika samun matsala ba.
TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user