Saturday 10 February 2018

‘Yan Najeriya fiye da Miliyan 144 su ka mallaki wayar salula – NCC

Tura Wannan Zuwa
Hukumar Sadarwa ta Kasa, NCC, ta bayyana cewa akalla akwai mutane miliyan 144, 631,678 masu amfani da wayar salula.

Wannan adadi kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai ya ruwaito, na nufin yawan layukan wayoyin hannun da ake amfani da su a Najeriya sun wuce milyan 144 kenan.

Kafin adadin ya kai haka a cikin watan Disamba, a cikin watan Nuwamba adadin ya na miliyan 141,900.405 ne, wato an samu karin mili yan 2,731,273 kenan.

Source by ©Premium Times Hausa
TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user