Monday 26 February 2018

Karanta Yanzu Kaji: Babban Dalilin dayasa nace Inason yin Aure Yanzu-Hannatu Bashir 'Yar Film

Tura Wannan Zuwa
Hannatu Bashir tana daya daga cikin fitattun jarumai mata a masana’antar finafinai ta Kannywood.
Wadda a yanzu ake damawa da ita. Ta yi finafinai masu yawan gaske duk da cewar ba wasu shekaru masu yawa ta yi ba a cikin masana’antar, kai har ma finafinai ta shirya nata na kanta.
Hirar ta da wakilin BBC Hannatu tana mai cewa "Ko wace mace tana son ta ganta a gidanta kuma tana kula da iyalen ta. Idan ina da mijin yanzu idan nayi aure, ka gan zan fita da safe zuwa wajen aiki wa zai kula dashi? Idan kuma na fara tara yaya wa zai kula mun dasu?. Ka gan ya zama dole in hakura da daya. Kuma harkar fim dinmu ba a iya kano kadai muke yi muna iya zuwa wasu garuruwa muyi.
Ina da miji zai barni in tafi wani gari inje inyi kwana biyar zuwa goma wajen daukar fim? kaga abu ne mai kamar wuya. "Ni daia zaman aure ya fiye mun kudin da zan samu kuma ya fiye mun komai da komai ma". Hannatu wanda ta kwashi sama da shekara bakwai a dandalin nishadantarwa tayi karin haske game da zargin da ake yawan yi ma yan fim na cewa su yan iska ne.
Domin jin sirrin rayuwar matashiyar jarumar waikilin mu ya yi hira da ita don haka sai ku biyo mu ku ji yadda hirar ta kasance.
Da farko za mu so ki gabatar da kan ki ga masu karatun mu
To assalamu alaikum, kamar yadda aka sani sunana Hannatu Bashir wadda aka fi sani da Hanan kuma tarihin. An haife ni a garin Kano a unguwar Tukuntawa a shekarar 1992. Na fara girma sai muka tashi daga nan muka koma Unguwar Sharada a nan na yi karatuna na firamare da sakandire zuwa yanzu dai bayan na gama sakandire ina ci gaba da karatu a halin yanzu.
To ya ya aka yi kika samu kanki a harkar fim?
Ni dai tun ina karama na ke kallon finafinan Hausa kuma hakan ya yi tasiri a zuciyata sosai kuma na ga akwai fadakarwa sosai don haka ni ma sai na yi burin na zama daya daga cikin masu fadakarwa sosai, don haka ni ma sai na yi burion na zama daya daga cikin masu fadakarwar.
Wace shekarar da kika fara fitowa fim?
Zan iya cewa, na shigo harkar ne a karshen 2011, kuma a lokacin da yake na san Darakta Hassan Giggs sai na fara yi masa magana, amma dai ba ta hannunsa na shiga ba, na shigo ne ta hanun Umar Jalo. Shi ne ya fara saka ni a fim. Wani fim mai suna Kotun Ibro. Shi ne fim dina na farko.
Yanzu daga fim din da kika yi na farko zuwa wannan lokacin, kin yi finafinai za su kai nawa?
To, gaskiya na yi finafinai da yawa, wadanda ba zan iya cewa ga yawansu ba. Sai dai na dan kimanta na ce za su kai 40 zuwa 50 da wani abu.
Ko zaki fadawa karatu kadan ne daga cikinsu?
Wadanda zan iya fada su ne kamar Kotun Ibro, Rai Dangin Goro, Hindu, Wani Hani Ga Allah, Gaskiya Ta Fi kwabo, da dai sauransu.
A cikinsu, wanne fim ne ya fito da ke har duniya ta san ki?
Tun farkon finafinaina zan iya cewa duk sun fito da ni, saboda ba fim ba ne da na yi sin daya ko biyu ba, don ka ga fim dina na farko Kotun Ibro, ni na ja fim. Sai na yi makahon Tunani. Shi ma na yi sin wajen sha biyar a ciki, Kaskon Wuta ma ina da sina-sinai da dama. Kuma daga nan sai muka ci gaba da yin finafinai, amma dai fim din da na san an fi gane fuska ta sosai shi ne Gaskiya Ta fi Kwabo.
Idan na fahimce ki tun da kika fara fim kin fara ne da matsayin jaruma ko?
Haka ne, ni da matsayin jaruma na fara yin fim. Kuma a yanzu a cikin finafinan da na yi wadanda ni ce na ja fim din su ne suka fi yawa a kan wadanda ba ni na ja ba.
Wannan yanayi naki ko kuma a ce sa’ar da kike da ita ba kasafai ake samun jarumai da suke shigowa da sa’a kamar taki ba.
Ko mene ne sirrinki?
To wannan dai sai dai na ce daga Allah. Don duk yadda Allah ya tsara abu to da haka zai zo wa mutum don haka ni sirrina abu ne daga Allah.
Ganin cewar a yanzu kina cikin matan da za a lissafa su a cikin harkar fim.
ko ya ya za ki iya kwatanta yadda harkar fim take a yanzu?
To, rayuwar harkar fim ga ta nan a yadda take, kowa yana yin abubuwansa na ci gaba. Kuma ka san a kowacce sana’a mutum ba ya rasa samun kalubale na rayuwa.
Amma ni dai a kaina ba zan iya cewa ga kalubalen da na samu a harkar fim ba.
Ko za ki iya tuna irin nasarorin da kika samu a cikin harkar fim?
Nasarori na same su da dama, domin kuwa lokacin da na fara yin fim ina gida za a kira ni, amma yanzu na kai matsayin da za a kai mini labari na duba idan ya yi min zan fito a fim din, sai mu yi ciniki da mutum na fada masa yadda zai biya ni. To ina ganin wannan ma kawai nasara ce.
Wani lokacin jarumai mata suna hadawa da shirya finafinai nasu na kansu ko ke ma kin fara shirya naki na kanki?
Eh, ni ma ina shirya fim dina. Ka ga na shirya fim din “Mero” kuma na yi “Kukan Kurciya. Duk da yake shi ba nawa ba ne, kuma a yanzu ma akwai wadanda nake shirin yi a nan gaba.
Harkar fim takan ba da damar jarumi ya yi yawo gurare da dama a duniya.
ko ke ma kin samu damar yin tafiye-tafiye kamar yadda ‘yan fim suke yi?
Gaskiya ina yin tafiye-tafiye da dama duk da yake mafi yawa ba fim ne yake kai ni ba, amma dai ta dalilin fim na smau damar yin tafiye-tafiyen da nake yi.
Akwai wani shiri na talabijin da kike yi a yanzu mai suna Mata Adon Gari.
ko mene ne hikimar yin wannans shiri?
Shirin Mata Adon gari ya kunshi abubuwa da dama, amma dai shiri ne na mata kawai wanda yake fadakar da mata a game da yanayin rayuwarsu ta cikin gida tsakaninsu da yara da maigida, da yadda za su gyara jikinsu da irin kwalliyar da za su yi, yadda za su zauna da yara da kuma kula da maigida. Wannan ya sa a cikin shirin muke gayyato mata da dama domin su ba da tasu gudunmuwar. To irin abubuwan da shirin ya kunsa kenan. Duk da dai cewar a yanzu ne muka fara, muna fatan wannan shirin ya samu karbuwa a wjaen mata wadanda domin su ake yin shirin.
Shirin naki ne ko wata kungiya ce tadauki nauyi?
Shi dai wannan shirin an yi shi ne domin a nuna shi a manyan gidajen Talabijin na duniya. Kuma idan da hali ma a shigar da shi kasuwa.
Wanne irin buri kike da shi a rayuwarki ta gaba?
Burina shi ne na yi nasara a duk abin da na sa a gaba. Kuma ina burin na samu miji nagari wanda zan aura, domin ita rayuwar ‘ya mace duk inda ta kai to aure shi ne babban rufin asiri gareta.
Mene ne sakon ki na karshe?
Sakona na karshe shi ne, ina fatan yadda na shiga harkar fim lafiya Allah ya fitar da ni lafiya.
Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku
Isar
da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradinmu
Ku hanzarta sanar da 'Yan Uwa da abokanan
Arziki sunan Website din Mu me Albarka, don
ganin sabbin posting din Mu sai ku duba cikin
website din akwai "Home" sai ku shiga,
mungode
Ku cigaba da Kasancewa da Website din Muryarhausa24.com don samun abubuwan more rayuwa na
yau da Kullum
An kirkiri Wannan Shafi domin
bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya
Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin
Cikin Mu Always Visit==http://www.muryarhausa24.com
Ku Cigaba da Kasancewa da Shafin
Muryarhausa24 aduk inda kuke a fadin Duniya
farin cikin ku shine Farin cikin Mu
Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me
hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu
Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga
Suleman Abubakar saboda awajensa musami
Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani
ba, adinga yimana Uziri
Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje daya a ko ina suke
KARIN BAYANI
Zaku iya aiko mana da labari,Nishadi,Fadakarwa,Hausa Novel,Ra'ayi,Labarin Soyayya, Sharhi ko nuna gamsuwar Ku akan yadda muke tafiyar da wannan shafi me Albarka aika sakon ka anan muryarhausa24@gmail.com mungode
Allah ka daukaka harshe Hausa dama Kasa baki
daya Amin Summa Amin.
Source by ©Hausa Leadership
TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user